28

59 6 0
                                    

Fatimah tana business sosai a Lagos don babu abinda bata siyarwa indai ana so musamman atamfofi da laces domin babbar dealer ce. Abdallah ma kuma Allah yayi masa arziƙi tunda a babbar ma'aikata yake aiki kuma yana noma da aikin kwangila. Kamfani ne dashi sukutum a Kano ya ɗaura yaran ƴan uwa akan lura da ayyukan da suke samu. Bugu da ƙari kuma basu da ɗawainiyar yara tunda Allah bai basu ba kuma dangin su na da rufin asiri da wadatar zuciyar da babu wanda ya dogara dasu sai abinda sukayi niyya suka bayar domin zumunci shiyasa suka kasance masu tarin arziƙi kuma babban abun burgewar shine ta hanyar halal suke nema basu saɓawa umurnin Ubangiji ba.

Suna bada tallafi sosai a gidajen marayu na Lagos da Kano kuma gwargwadon iko suna taimakawa mabuƙata saboda samun lada a wurin Allah. Har masallatai da rijiya sun gina domin yiwa kansu tanadin samun lada har bayan mutuwarsu saboda sun sadaƙar da cewa basu da magaji a duniya ko ɗan da zai musu addu'a bayan sun mutu.  Wannan shine dalilin da yasa babu wani tunani ko tashin hankalin tsadar kuɗin jirgi sukayi booking washegari da sassafe suka kama hanyar airport domin jirgin farko suka kama saboda suna son isa da wuri. Sha ɗaya a Kano tayi musu kuma kafin isowarsu Oga Abdallah ya riga da ya tanadar musu da mota da driver saboda haka daga airport hanyar Gombe suka kama ba tare da sun yada zango a ko ina ba. Gudu sosai drivern yake shararawa amma Fatimah gani take kamar baza'a isa ba. Allah Allah takeyi tayi tozali da sanyin idaniyarta kuma tana fatan ƴar tata zata so ta ta ƙaunaceta kamar yadda take matuƙar kaunarta sama da kowa da komai a duniya. Fatanta Allah yasa tayi rayuwa mai kyau kuma bata fuskantar tsangwama saboda yanayin halittar su. Hotunanta da tasa Mubarak ya tura mata tun a daren jiya take ta bi tana kallo kuma tana fatan ta samu hotunan ta na yarinta domin taga yadda ta taso tun tana ƙaramarta.

Sai da suka kusa isowa Dukku Mubarak ya nemi izininsu akan ya sanar da Baffa suna hanya saboda a tanadar musu da abinci saboda yanada tabbacin cewa yana gida tunda weekend ne.

"Ba sai ka takura su ba. Ai zamu nemi hotel mu sauka idan mun ɗauko Khadijan" Fatima ta faɗa.

Kallon anya kanki ɗaya Oga Abdallah yayi mata kafin yace "Haba Fatimah? Mutanen nan fa idan ba don Allah ya ƙaddara zamu san da zaman Khadijah a duniya ba da sune gatanta kuma danginta. Saboda haka dan Allah ki bi komai a sannu kuma ki zauna a gidan idan yaso ni da nake namiji na nemi masauki amma bai kamata daga zuwa a fara nuna musu iko akanta ba. Calm down please "

"Afwan. Kasan hankalina gabaɗaya baya jikina" murmushi ya sakar mata ya kamo hannunta ya saka a cikin nashi tunda suna zaune a baya tare shi kuma Mubarak da driver suna gaba. Yasan yadda matar tasa take matuƙar son yara da sakalta su. Duk ya'yan ƴan uwa ita ce favorite aunt dinsu ballantana kuma ƴar da ta haifa ta fidda ran haɗuwa da ita dole sai anyi mata uzuri. Shi kansa ƙarfin hali kawai yake yi amma ya zaƙu sosai yayi tozali da ɗiyarsa, gudan jininsa.

Da mubarak ya kira Ammah ya sanar da ita cewa sun kusa ƙarasowa gari kuma yana tare da baƙi mutum uku sannan ta kira Yaya Muhammad yazo gidan kafin su ƙaraso abun ya matukar bata mamaki amma tasan lafiya daga yanayin muryarsa. Kuma daman ya saba dawowa gida ba notis lokacin da yake makaranta. Sabirah ta kira ta sanar da ita zuwan mutuminta. Nan da nan cikin murna da annashuwa suka fara aikin tarbar baƙin. Dayake tazarcen shinkafa da miya da salad sukayi sai kawai suka ce bari su nemi wani abun suyi domin ya ƙayatar da abincin tunda akwai baƙi. Peppered chicken sukayi da coconut drink sai ceaser salad.

"Kiyi musu Chinese buns ɗin nan mana, naga baya ɗaukan lokaci" Khairiyyah tace.

"Sai dai gobe tunda nasan kwana zasu yi. Ya kamata ace sun ƙaraso ma yanzu indai ba a hankali suke tafiya ba" Khairiyyah bata kai ga bata amsa ba sai ga Sallamar Yaya Mubarak. Runtumawa sukayi a guje sukayi falo domin tarbarsa sai dai ganin mutanen da sukayi a tsaye da kuma salati da salallamin da Ammah keyi Baffa ma fuskarsa tayi kamar wanda yaga fatalwa yasaka su yin turus.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now