22

55 7 0
                                    

Ɓata rai sosai Yaya Muhammad yayi lokacin da Ammah ta kirashi ɗakinta take yi masa bayanin abinda ya wakana tsakaninta da Maman Bilkisu da yayarta. Haƙuri suka bata sosai kuma sunyi mata alƙawarin cewa Bilkisu tayi karatun ta nutsu kuma idan Allah ya yarda wani abu mara daɗi makamancin abinda ya faru bazai sake giftawa a tsakaninsu ba.

"Da alama ta horu kuma tayi hankali. Dan Allah kayi haƙuri. Bana so a fara maka ƙirgen aure a ƙananun shekarunka. Nasan bata kyautaba kuma nafi kowa jin ciwon abinda ta aikata maka amma rayuwar aure daman kusan gabaɗayanta haƙuri ne saboda haka ina mai roƙon alfarmarka da ka manta da komai ka maida ita ku fara gina rayuwarku akan turban mutunta juna da koyarwar addini"

"To Ammah naji in shaa Allah karshen wata zanje na mayar da ita amma Ammah da zaki taimaka ki aura min Sabirah" Dam!!! gaban Ammah ya faɗi. Me ke shirin faruwa ne a gidan nata? Duk abubuwan dake faruwa duk da cewa dai baya gidan baida masaniya akan ɗan uwansa yana son Sabiran ne ko kuma dai son zuciya yake son nunawa?

"Me kuma ya haɗa ka da ƙara aure? Mace ɗaya ma ta gagare ka ballantana ka haɗa biyu? Kuma waya faɗa maka Sabirah bata da wanda zai aureta da har kake cewa a aura maka ita?"

"Kawai dai Ammah na yaba da nutsuwa da tarbiyyarta ne kuma ina da yaƙinin cewa bazata wulaƙanta ni ba bawai don ina sonta ba " ɓoyayyiyar ajiyar zuciya Ammah ta saki.

"To ai kuwa kada ka kuskura ka fara sonta. Na roƙeka da Allah kuma mu rufe zancen nan anan ba sai kowa yaji ba. Allah yayi maka albarka ya baku zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba. Sai ka jajirce ka tsaya sosai a gidanka sannan ka dage da addu'a. Dukkan wani kyautatawa da hakkinta kayi kokarin saukewa kaji?" Gyada mata kai yayi yayi mata sai da safe ya wuce ɗakinsa na gidansu. Shifa yanzu da za'a bi ra'ayinsa to kawai sawwaƙe wa Bilkisu zai yi domin ta fita fit a ransa. Tun ranar da akayi musu Shari'a ko muryarta bai sake marmarin ji ba balle kuma yayi tunanin sake zama inuwa ɗaya da ita a matsayin matarsa. Addu'a yake kullum akan Allah ya tabbatar masa da alheri. Yadda Sabirah take kula da lamuransa da kuma yi masa biyayyah ne ya ƙawata masa ita a matsayin mata. Bai tsaya dogon tunani akan zancen da Ammah tayi masa ba ya cigaba da sabgogin gabansa.

Ammah kuwa kwana tayi tana tunani da addu'ar Allah ya daina ƙawatawa Muhammad Sabirah a matsayin mata domin kuwa tasan za'a yi ɗan ƙaramin yaƙi idan Mubarak yaji labari. Duk da cewa tanada tabbacin cewa bai furta wa Sabirah yana sonta ba amma alamu sun nuna kuma yadda ita ma Sabiran take rawar jiki akan lamuran Mubarak ɗin dole son shi take sai dai ita batada masaniya akan hakan a wajenta kawai shaƙuwa ce da haɗuwar jini.

Su Sabirah sun fara exams saboda haka suka ajiye komai a gefe suka fuskanci abinda ke gabansu. Hajiya Khairiyyah anji uwar bari sai dagewa ake ana kashe kai da karatu kuma tana da yaƙinin cewa in shaa Allah bazata bawa su Ammah kunya ba. Mubarak kullum sai ya kira Sabirah video call idan ta dawo daga exams don hatta time table ɗinta yana dashi ta tura masa. Yana ta bata labarin wani babban mutum daya haɗu dashi me kirki wanda yake koya masa aiki kuma yake jansa a jiki kamar ɗan cikinsa. Sosai yake jin daɗin Lagos.

Tun ranar da Nura ya sameta a school ta sake shashantar da zancen sa duk da cewa sunyi shawara da Hafsah da Khairiyyah sai ta sha'afa bata tura masa da message ɗin nuna amincewarta ba shi kuwa bawan Allah yana can yana jiran tsammani. Zuciyarsa har wani zafi zafi take masa idan ya tuna hoton kan wallpaper ɗin Sabirah. Ya rasa yadda zai ɓullomata gashi babu abokin shawara domin har yanzu haushin Musaddik yakeji shi kuma ya tattara shi ya watsar. Yana cikin gidan zai zo har falo suyi hira da Faridah ya kama gabansa ba tare da ya neme shi ba. Shima Musaddik ɗin haushin Nura yake ji saboda bai taɓa zaton shi ma bai yarda dashi ba. A tunanin sa Nura zaifi kowa murna akan alaƙarsa da Faridah tunda yafi kowa sanin halinsa. Jira yake ya takaleshi ya amayar masa da cikinsa don sai ya gaggasa masa maganganu masu ɗaci.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now