8

68 8 0
                                    

Bayan wasu kwanaki da zuwan Baba gidan Nura wanda kuma bai sake zuwa ba Ummi ta tara yaran nata a dakin ta tayi musu nasiha me ratsa jiki. Ta nuna musu cewa duk abinda bawa ya shuka zai girba walau alheri ko sharri sannan Baba mahaifinsu ne, haka Allah ya ƙaddara saboda haka dole ne su mutunta shi su girmamashi kuma suyi masa biyayya idan har hakan bai saɓawa addini ba. Bazata taɓa yarda su koma gidansa ba amma kuma idan ya nemi kusanci dasu dole ne ta bari saboda yanada hakki a kansu.
"Idan kuna ganin cewa ya zubar da girmansa akan irin abubuwan da yayi mini a kan idonku wannan tsakanina da shine da kuma mahaliccin mu, yanda kuke da hakki akansa shima yana da hakki a kanku saboda haka ku daina bari zuciya tana diɓanku musamman kai Nura. Kaine babba amma kaine kafi kowa riqo. Bana son daƴa daga cikinku ya kasance cikin fushin Ubangiji a dalilin Abdullahi. Dan Allah a kula a kiyaye. Idan kun ji bacin rai ya taso muku kuyi ta istighfari da a'uziyyah in shaa Allahu zakuji zuciyarku tayi sanyi. Idan kuka lazimci karatun Alqur'ani kaf duniya babu abinda zai dami zuciyarku indai kuna yawan ambaton Allah. Hatta salatin annabi yana yaye damuwa to akan me zaku tada hankulan ku bayan Allah ya kawo mana sauki ta hanya mafi sauki kuma ga samun lada?"
Duk jikinsu yayi sanyi sai suka fara bata hakuri akan abinda ya faru tare da yi mata alƙawarin cewa in shaa Allahu irin hakan bazai sake faruwa ba. Albarka ta saka musu tausayinsu yana daɗa kamata. Lallai da ana nunawa mutum abinda zai sameshi a rayuwa to da tabbas ta hakura da aure kwata kwata domin auren Abdullahi bai ƙare ta da komai ba sai ɓacin rai da ciwon zuciya. A kullum da dana sanin aurensa take kwana take tashi sai dai bawa baya wuce kaddararsa kuma ko ba komai Allah ya bata nagartattun yara masu jin ƙai da kaunar ta kuma masu yi mata biyayyah saboda haka bazata butulce ba dole ta kasance me yawaita godiya wa Allah daya yi mata wannan ni'imar.
"Za'a yi post utme next week Fiddausi. Ki zama cikin shiri" Nura ya faɗa bayan sunyi sallama da Ummi sun fito yana son fita zuwa wurin Musadik. Baki ta tunzuro gaba tana haɗa rai.
"Haba Boss dan Allah me nayi maka ne wai? Ni fa wallahi na gaji da boko. Tunda dai zan karanta na rubuta da Hausa da turanci kuma daidai gwargwado na iya turancin me ake buƙata kuma? Very soon ma zan dawo da sana'ar yin lalle kaga ai shikenan ko?" Ta fada hankalinta kwance duk da dai tana tsoron abinda zai je ya dawo. Baya dukansu amma kuma baya musu da sauki idan ransa ya ɓaci.
"Wallahi tallahi kinji na rantse ko? Sai kinyi karatu ko zaki mutu Fiddausi. Mu zuba ni dake a gidan nan" tsaki yaja ya fice daga gidan ransa na suya. Wai har shi zai faɗi magana Fiddausi tace bazata yi ba idan ba hauka irin nata ba suna da gatan da ya wuce karatun ne. Lallai kuwa zasu sa kafar wando ɗaya da ita kuma ko me zai faru sai dai ya faru amma sai tayi karatu.
"Ai wallahi a level one zanyi daƙikancin da sai anyi withdrawing dina a course din. Bokon nan dai ba hanyar shiga aljannah bace" ta fada tana kunkuni. Ko kallon inda take Faridah batayi ba saboda tasan haukanta take yi. Ita yanzu damuwarta bata wuce na ƙin barinta sauraron samari da boss din yayi ba kuma tana shekarar karshe a jami'a batasan meye nufin sa akan hakan ba. Haka dai ta cigaba da faɗan maganganu da yadda zata yi ko yaki ko yaso ya hakura ya bar ta.
"Kin cika min kunne Fiddausi. Ki bari boss din ya dawo sai kiyi masa rashin kunyar taki da kika koya kwana biyu. Banda abunki ko wuta Yaya Nura yace ki shiga a zatona shiga zakiyi tunda duk faɗi tashin da yake yi da rashin hutu akan mu ne. Idan ta shine me yake nema yanzu? Daidai gwargwado Allah ya rufa masa asiri."
"Nifa ba haka nake nufi ba kar ki fassara ni. A duniya bayan Ummi banda kamar Yaya Nura kuma nasan bazan taɓa biyansa akan sadaukarwarsa a gare mu ba. Karatun ne kawai na tsana kuma bana tunanin akwai abinda zai sa na so shi "
"Ai shikenan, tunda ke baza'a faɗa miki magana ki ji ba"  tashi tayi ta bar mata falon saboda ta tabbata idan ta cigaba da zama zata iya mata shegen duka don takaici. Ita gwara ita gata zai mata daya tursasata yin karatun ita kuwa fa? Aure fa yake son hanata kuma bata ma san dalilinsa nayin hakan ba. Ita dai ta fara gajiya da ƙosawa kuma tana daf da kai ƙarar sa wurin Ummi ko wan Baba.
Ranar post utme da sassafe ya tasa ƙeyar Fiddausi yace ko ta shirya ko bata shirya ba sai taje. Haka ta tafi fuska a murtuƙe babu annuri. Ko credentials dinta bata dauka ba sai Faridah ce ta biyo ta dashi mota. A hanya Nura ya sauke makaman yaƙinsa don yaga alama Fiddausi ba zata ji faɗa ba. Nasiha yayi mata da nusar da ita amfanin ilimi.
"Ko Kanada kudi fa sai da ilimi ake ganin girman ka. Kuma idan bakiyi karatu ba me zakiyi? Bazan hanaki sana'a ba. Duk abinda kike son yi indai bai saɓawa Shari'a ba a shirye nake dana baki ko nawa ne ki fara. Kawai dai ina son ko ta wanne ɓangare ku wuce wulakanci, bana son wani yayi muku kallon kaskanci ko rashin isa. Dan Allah ki fahimce ni" jikinta yayi sanyi sosai dan bata taɓa tsammanin zai lallaɓata ba sai taji ya sagar mata da gwuiwa.
"Dan Allah yaya kayi hakuri. In Shaa Allahu zanyi kokari. Ni wallahi karatu wahala yake bani kuma ina jin labarin cewa karatun jami'a yanada wahala. Sannan bana fahimtar abubuwa da sauri shi yasa kawai naga da ka ringa asarar kudin ka ina samun carry over ko na kasa gama karatun gwanda kawai banyi ba "
"Haba autan Ummi. Ban sanki da ragwanta ba. Babu abinda yafi karfin ɗan Adam indai yasaka a ransa cewa zai iya to sai kiga Allah ya dafa masa. Ko baki zama gwana ba zaki zama a cikin ɗaliban da suke wucewa ta bayan katanga. Ballantana ma ina da yaƙinin indai kika saka kanki kuma kikayi tarayya da masu kwazo da son karatu zaki zama gwana kema " tunda ya samu tayi laushi sai ya cigaba da karfafa mata gwuiwa kafin su isa sai da taji ba first class ba ko sama da haka ne zata iya fita dashi.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now