31

58 7 0
                                    

Kwanan su Ammah biyu a Kano suka koma Gombe. Su Khairiyyah da Sabirah da Mubarak sai da sukayi sati ana zaga dangi sannan suka wuce Lagos inda anan zasu ƙarasa hutun su kafin su koma makaranta.

A washegarin ranar da suka zo Kano Sabirah ta kira Nura tayi masa bayanin abinda ke faruwa. Murna yayi sosai kamar zai zuba ruwa a ƙasa yasha don daɗi. Yace mata congratulations yafi sau goma yana wangale baki. Tsabar samun wuri harda video call sukayi. Hafsah ma har gidan Mama tazo taya aminiyarta farin ciki kuma Ammi tayi mata tarba kamar ta ƴar sarki saboda taji labarin ta. Daɗi kamar ya kashesu ita da Khairiyyah sai rawar kai da karaɗi suke yi.

"Allah kenan. Dama shi ba azzalumin bawansa bane ki ga dai yadda ya canza miki rayuwa ta hanyar da baki taɓa zato ba " Hafsah ta faɗa tana ƙarewa ɗakin da suke kallo.

"Ki bari kawai. Yadda kika san nice haka nake ji mata daɗi sai dai ƴar ƙauyen ƙawar taki har yanzu bata sake ba sai wani nuƙu nuƙu take kuma baki ga yadda mutanen nan ke sonta ba kamar su maida ta cikinsu" Khairiyyah ta sa baki tana makawa Sabirah take zaune tana jinsu harara.

"Zata sake ne Khairiyyah, abunne yazo mata a bazata shiyasa. Amma dolenta ta sake. Kiga fa yadda Amminta ke nan nan da ita kamar wata ƙwai. Motsi kaɗan me kike so me ke damunki. Daga zuwa na ta shigo ɗakin nan duba ta yafi sau biyar"

"Ai baki ga komai ba. Ranar ma abinci ta bata a baki in faɗamiki. Ina kallon su suna bani sha'awa ita Madam din kunya ta dinga ji. Ina ma nice Ammah zatayi feeding ɗina"

Tsaki Sabirah taja kafin tace "wai ku bakwa kunyar gulmar mutum a gabansa? Ina zaune kuna zancena kamar bana wurin hakan daidai ne?"

"Shine daidai mana. Da muyi a bayan idonki kuma mu samu zunubi ai gwara kina zaunen. Kuma wannan ai faɗan gaskiya ne ba ƙarya ba" Hafsah ta bata amsa.

"Ai daman ba'a cin ku musu ko yaya ne sai kun ƙure mutum. Sai kuyi ta fama ai tunda bakwa gajiya da maida zance"

"Ga earpiece nan ki toshe kunnuwanki idan bakya son jin hirar tamu" Khairiyyah ta faɗa tana miƙa mata earpiece ɗin dake jikin wayarta.Haka suka wuni suna raha har yamma tayi Ammi ta haɗa su da ɗan ƙanwar Abbu Sa'ad daya zo ganin Sabirah saboda baya gari lokacin da suka zo sai ranar ya dawo akan ya kai su shopping ya maida Hafsah gida. Khairiyyah ke ta surutu ita kaɗai a motar saboda Hafsah ta hau Whatsapp tana chatting da saurayinta sai dai tace ehh ko a'a Sabirah kuwa karatun wani Novel take hankalinta sam baya kansu.

"Are you a parrot? ( Ke aku ce) tun da kika shigo motar nan kike surutu ba coma ba full stop kamar wadda zata yi ciwon baki idan tayi shiru " Sa'ad ya faɗa bayan ya ɗan juyo da kansa baya. Haushi ne da kunya suka turnuƙe Khairiyyah kuma a take ta saka shi a blacklist ɗinta. Kuma tayi alkawarin ko tari bazata sake yi ba indai yana guri kuma har su koma bazata sake bari su haɗu ba.

Har sukayi shopping suka kai Hafsah gidan bayan sun tsaya sun gaida Abba Khairiyyah sai cika take tana batsewa kuma yana lura da ita.

"Yaya Sa'ad kaga ka ɓatawa ƴar uwata rai ku? Ina ruwanka da surutun ta tunda dai ba da kai take ba?" Sabirah tayi masa magana a hanyar su ta komawa gida. Ta riga da ta saba dashi ta waya tun kafin yazo shiyasa bataji kunyar yi masa magana ba bugu da ƙari kuma tasan da Khairiyyah ce ita da tuni ta shigar mata faɗan ko da kuwa ita ce bata da gaskiya.

"Yanzu Khadijah daga faɗan gaskiya sai cibi ya zama ƙari" Ya tambaya yana murmushin ƙeta.

"Ƙari ya zama ƙababa kuma ba"Khairiyyah ta bashi amsa a hasale. Ji take kamar ta shaƙe masa wuya.

"Allah ya baki haƙuri. Ya huci ran gimbiya. Idan kina so ma sai na kaiki gidan Radio kiyita zuba son ranki"

Baki ta cuno gaba tana gunaguni Sabirah kuwa ta kwashe da dariya a ranta tana cewa yau Khairiyyah ta gamu da daidai da ita.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now