40

69 7 4
                                    


Bayan sati biyu da haɗuwar Nura da Khadijah ne Amatu ta gaji da jiran da take mata akan ko zata buɗe mata cikinta ta faɗa mata abinda ke damunta saboda duk wanda ya santa ya san cewa ta ƙara yin sanyi, ta daina walwala kuma tana saurin fushi ga yawan lulawa duniyar tunani ayita mata magana bata ma san me ake cewa ba.

"Parrof me wai me ke faruwa ne ? Me yake damunki? A tunanina munyi shaƙuwar da zamu share wa juna hawaye kuma mu kasance tare duk wuya duk daɗi. Tunda na dawo bayan nayi ciwo na lura da cewa akwai abinda yake damunki a zuciya kuma ina ta jira ko zaki faɗamin amma kinyi shiru kin bar damuwa na neman affecting karatunki bayan dukkan mu muna sa ran zaki gama a matsayin wanda tafi kowa hazaƙa a set din mu. What's wrong?( Meke faruwa)"

"Hmm ban ma san me zance miki ba parrof me. Takamaimai bazan ce miki ga yadda nake ji ba. I just know that I'm sad and heartbroken ( nasan dai kawai ina cikin damuwa kuma an karya min zuciya"

"Subhanallahi. Kada kice min Abinda nake tunani ne ya faru don na lura tun kafin mu tafi hutu bakwa waya?" Amatu ta tambaya cikin tashin hankali.

Gyada mata kai Khadijah tayi tana kokarin riƙe hawayen dake kokarin silalo mata akan fuska. Rungumeta Amatu tayi tana dukan bayanta a hankali.

"Let it all out ( ki fitar da komai) nasan zaki samu salama idan kinyi kuka. Ina tare dake kinji" haka ta riƙe ta sai da tayi mai isarta sannan ta faɗa mata abinda ke faruwa tsakaninta da Nura.

"Tabbas na yarda da hasashenki tunda a gaskiya kowa yasan cewa Nura yana miki so irin na haƙiƙa. It's so obvious (a bayyane yake) amma gaskiya mamansu ta shiga hakkinku kuma bata kyauta muku ba. Kunyi bala'in dacewa da juna amma kamar yadda na sanki da yarda da ƙaddara da kuma hakuri da yadda rayuwa tazo miki to dan Allah kiyi hakuri, ki cire komai a ranki kamar ba'a yi ba mu cigaba da addu'a. Ki sani cewa Allah yana jarabtar bayinsa don yana son su samu kusanci dashi. Wannan wata dama ce a gareki da zaki ƙara ƙaimi wajen ibadah sai Allah ya wanke miki zuciyarki daga damuwa. Kinga karatun mu yazo gangara ko a da can da baki da gata baki bari damuwa ta hanaki sukuni ba saboda haka yanzu ina son wannan jarumar ƙawar tawa dana sani tayi abinda ta iya, ta maida komai ba komai ba mu fuskanci gaba saboda baya ta riga da ta wuce ɓata lokaci ne tunani a kanta"

Sun dade sosai Amatu tana faɗa mata kalaman da suka kwantar mata da hankali kuma suka ƙara mata ƙaimi wajen ganin tayi duk abinda zata yi domin yakice tunanin Nura da duk wani namiji da zai shigo rayuwarta tunda yanzu ta gane cewa kalubalenta ba wai wani yazo yace yana sonta bane sai dai yardar ahalinsa ce mai wuya.

"Naji dukkan shawarwarinki parrof me kuma in shaa Allah zanyi amfani dasu. Nagode kwarai da kulawa Allah ya saka miki da alheri ya bar mu tare har aljanna"

"Amin. Ki tambayi Ammah dan Allah idan zata bari kizo gidanmu mu kwana. Muyi kallo, na wanke miki wannan kan naki da bakya ƙaunar gyara shi sannan ki koya min sabbin recipes ɗin nan da kika ce kin koya wajen Ammi" Amatu ta fada tana mata murmushi.

"Anya kuwa zata yarda? Tunda nazo banda gidan addah Khadijah bamu taɓa kwana wani wuri ba shima saboda bikin yaya Muhammad ne amma bari na kirata sai ki tambayeta"

Tana kiran Ammah sai tace mata Amatu tana son yin magana da ita sai tace ai tana makaranta ma su zo su same ta a office. Sun tarar da ita tana marking wasu takardu suka samu wuri suka zauna. Sai da ta ɗan dauki lokaci kafin ta ɗago kai tace.

"Ina jinku, fatan dai ba wani abu ne ya faru ba ko wata matsala da karatunku Amatu?"

"A'a Ammah daman dan Allah neman alfarma nakeyi akan ki bawa Khadijah izinin kwana a gidan mu. Ina son gyara mata kanta ne kuma kinga wannan semester din kusan kullum yini muke a makaranta"

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now