29

49 6 1
                                    


A ranar talata ranar da Habi tayi wa laƙabi da baƙar rana, ranar da bata taɓa tunani ko hasaso zuwanta ba.  Tun cikin dare take zufa duk da cewa sanyi ake gashi gabanta sai faɗuwa yake ta rasa dalili. Tana son faɗawa Abba halin da take ciki tana tsoron ya yaɓa mata magana kamar yadda ya saba. Bashi ba, ita kanta ta gaji da yanayin da take ciki kuma tana neman sassauci. 

Tayi mamakin ganin har rana ta take Abba bai fita kasuwa ba kuma bai ce da ita komai ba.

"Abba yau bakaza fita bane?" Ta tambaya bayan ta kife kwanon da ta wanke na ƙarshe a kwando. Hatta hannunta rawa yake. A tsorace take sosai gabanta sai dukan tara tara yake.

"Eh ko akwai abunda na tsare miki ne?" Abba ya bata amsa a zafafe. Shi kansa ya rasa dalilin da yasa yake matuƙar jin haushinta a ƴan kwanakin. Abubuwan da take yi a da yake ɗauke kai su yake fusata sosai akansu yanzu. Ya tsani ya budi ido ya ganta a gidan wani irin ɗaci ke taso masa tun daga ƙasan zuciyarsa.

"Allah ya baka haƙuri. Na lura a hasale kake da kowa da komai a gidan nan. Idan aure kake son ƙarawa ai sai kayi bayani ba ka zauna kana muzurai ba. Kuma babu wadda ta isa ta aure min miji ta zauna lafiya"

"Kinfi kowa sanin cewa idan inada niyyar ƙara aure baki isa ki hanani ba duk masifa da bala'inki. Kawai dai nagaji da zaman haƙurin da nake yi dake ne ina tunanin mafita "   Gabanta ne ya faɗi sai da ta saka hannu ta dafe kirjinta.

"Haba Abba. Yanzu tsofai tsofai dakai sai ka aikata saki bazakaji kunya ba?" Ta tambaya muryarta na rawa. Wannan wane irin masifa da bala'i ne ya tunkarota. A tunanin ta tunda da daina yawo ya haƙura ashe lamɓo yayi.

"Idan Allah ya haɗaka da mace mai bala'in taurin kai wadda ba'a isa a faɗa mata taji ba kuma bata san ƙuru ba ai dole mutum ya aikata saki ko shi ya fi kowa shekaru a duniya. Ki fita a idona Habi. Ki kama kanki dani fa. Tam!" Yayi kwafa yana girgiza ƙafa.


Tun daren jiya da Baffa ya kirashi ya sanar dashi cewa suna nan zuwa gabaɗayansu akan wata muhimmiyar magana jikinsa yayi sanyi kuma yana da tabbacin wata tsiyar Umma ta aikata ko Suhaila. Kamar zai wuce kasuwa ya dawo idan sun iso kuma ya fasa. Yaso ya sanar da ita zuwansu sai dai yasan bata jituwa da duk wani mai ƙaunar Sabirah ko nuna kulawa a gareta shiyasa ya wakilta matar wansu da yin girkin.  Ace ƴar uwarsa da iyalanta zasu zo gidansa amma bashi da mutuncin da zai saka Habi tayi musu girkin arziki saboda kwata kwata kullum girkinta ƙara komawa jagwal yake yi. Daga ta cika gishiri, sai tayi shi garas garas ko kuma ta bari ya ƙone tana can tana tunani da zabure zaburen banza da wofi kuma bata san tayi salati ko addu'a ba.

"Nidai kayi hakuri mu gurgura a haka har Allah ya karɓi ranmu. Ka tausaya wa kananan yaran dake gaba na."

"Ke ai naga tausayinsu kike ji ko kuma kina kula dasu yadda ya dace duk wata uwar arziki tayi wa yaranta. Abbas yafi sati baya kwana a gidan nan amma na tabbata baki lura ba idan ma kin sani to baki damu ba saboda tsabar son kanki da rashin sanin ya kamata" shiru tayi don tasan batada gaskiya kuma kiris yake jira ya bata red card tayi gidansu.

Suna zaune a wannan yanayin Suhaila ta da ƙara muni ta kwanjame ga tulelen ciki a gaba haihuwa yau ko gobe ta fito tana yamutsa fuska.

"Wai hayaniyar me kuke yi ne Umma? Duk kin katse min bacci wallahi"  baki Abba ya saki yana kallonta yana jinjina tsaurin ido irin na Suhaila. Sam bata tauna magana kafin ta furta ta. Iyayenta take wa magana kamar wasu ƙannenta ko yaran cikinta. Bai ce mata uffan ba saboda a yadda yake jin kansa yana iya yi mata shegen duka saboda haka taci albarkacin cikin dake jikinta. Umma kuwa abinda ke damunta yafi ƙarfin ta tsaya ɓata lokacinta akan Suhaila. Duk yarinyar ta sire mata kuma da tana da yadda zata yi ko inda zata kaita ba tare da asirinsu ya tonu a idon duniya ba da tuni ta tattarata ta kaita wani gidan ko ta samu salama.  Zama Suhaila tayi a bakin kofar daƙin tana kallon iyayennata kuma a ranta tana mamakin dalilin da ya hana Abban nasu fita.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now