26

53 6 0
                                    

Wani mummunan mafarki Umma tayi daya gigitata ta tashi a firgice tana ihu ba salati ba. Gabaɗaya ahalin gidan sai da suka farka aka nufi ɗakinta domin ganin abinda yake faruwa.

"Habi meye haka? Ki dinga kiran sunan Allah idan abu mara kyau ko mai kyau ya sameki mana ba ihu ba kamar wata ƙaramar yarinya"

"Abba zasu kamani, sun ma kamani sun ɗaure. Dan girman Allah mu bar garin nan, idan da hali ma ko Nijar ne mu koma kaji" Umma ta faɗa a firgice tana rawar ɗari. Takaici ne ya turnuƙe Abba, ya lura da cewa sam bata cikin nutsuwarta a ƴan kwanakin kuma yayi tambayar duniya tace ita babu abinda ke damunta. Motsi kaɗan ko maganar Sabirah sai ta zabura ta fara zare idanu kamar wadda tayiwa sarki ƙarya.

"Kin dai sawa ranki wani abu ne kawai. Kuma kin taɓa ganin inda mafarki ya zamanto gaskiya? Wa kika cuta da har zai ɗaure ki? Kuma kawai saboda kinyi mafarki ni kuma na zama soloɓiyo sai mu kwashe kayan mu mubar gari? Zancen ki yayi kama dana masu hankali?"

"Idan abu ya samu bawa taimakon Allah yake nema da kariyarsa. Kina tunanin koma me ke bibiyarki zaki iya kare kanki ne ko wani bil adama zai iya kare ki? Ki yawaita yin azhkar da karatun Alqur'ani in shaa Allah zaki daina firgita. Wataƙila ma ko addu'ar bacci bakiyi ba kika kwanta" Abba ya faɗa da sigar lallashi. Suhaila daman ta ƙosa da tsayuwar sai rafka hamma take. Allah Allah take ace su koma dakinsu domin tun ranar da Abba ya mareta ta ɗan rusuna ta daina rashin kunya a gidan. Kamar Abba ya shiga ranta ya juya yace su koma ɗaki shi zai zauna da Umman tasu har ta samu ta koma bacci.

Kusan kwanan zaune sukayi Umma na abubuwa kamar me taɓin aljanu. Har ya fara tunanin idan gari ya waye zai nemo malami ayi mata ruƙiyyah. Sai sambatu take tana cewa kada ya gujeta idan sun zo kamata. Kada ya manta shi mijinta ne bai kamata ya gujeta ba duk wuya duk tsanani.

"Anya Habi baki aikata wani mummunan abu ba yanzu yazo yana damunki? Haƙƙin wa kika ɗauka da ya fara bibiyarki kina kokarin rasa hankalin ki?"

Kalaman Abba sun sa ta ɗan dawo hayyacinta sai kuma ta sake diriricewa "Ni ban ɗauki hakkin kowaba. Idan ma na ɗauka zaka fi kowa sani"

"Ta ina zan sani ni da ba mazauni ba? Lokacin da zaki aikata son zuciyarki ai bazaki so na sani ba tunda bakyason gaskiya ko gyara"

"Yanzu dai saboda Allah, ina cikin wannan tashin hankalin me ya kawo wannan zancen?"

"Haka ma zakice? To Allah ya baki lafiya Habi. An kusa kiran assalatu, bari nayi alwala na taso yara mu wuce masallaci. Allah ya baki lafiya kuma tunda ke kwata kwata a rayuwa ba za'a miki gyara ki ɗauka ba to ni kuma bazan iya aikin gadi ba. Daga yau idan kin farka da ihu da kururuwarki ki nemi wani ya zauna dake amma bani ba. Kai! Kima daina yimin ihu a gida" ya sa kai ya fice ya bar Umma da bugun zuciyarta ya ƙaru jin furucinsa na ƙarshe. Ita ma zata so ta daina mafarkan da take yi amma kullum abu ƙara gaba yake yi kuma kullum abubuwan da take gani na tashin hankali yafi na baya. Haka ta wuni sukuku kamar mara lafiya sallolin farillan ma a gaggauce take yin su balle tayi tunanin amfani da shawarar Abba. A halin da take ciki kamata yayi ace Suhaila ta taimaka mata da ayyukan gidan ko da bata yi gabaɗaya ba amma bata fito daga dakinsu ba ma sai azahar tana hammar yunwa sai dai Umman ko ci kanki bata ce mata ba. Daman da safe Abba ya bawa Imam kuɗi ya siyo musu kunu da ƙosai sannan suka ci kowa ya wuce inda zashi. Abbas da yake SS 3 sun fara zana jarabawar fita sai Imam daya shiga aji daya a sakindire shi kuma Abba ya wuce kasuwa. Wannan dalilin ne yasa Umma bata da niyyar girki duk da cewa ita ma yunwa na sakaɗar cikin ta. Da Imam ya dawo da rana babu abinci bai damu ba kuma bai yi wa Umma korafi ba. Wanke kayansa yayi Sannan yayi shirin makaranta hankali kwance.

"Kai Imam bazaka ci abinci bane?" Umma ta tambaya ganin yana ƙoƙarin fita daga gidan batare da yayi mata zancen abinci ba.

"To Umma kin dafa ne da zanci? Kamar nasani na roƙi Abba ya bani kuɗin abinci saboda na tabbata yau kam kin samu hutu ba yi zakiyi ba" Ya kwaɓa mata magana hankali kwance yayi wucewarsa. Suhaila dake zaune a bakin ƙofa tana jinsu.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now