13

50 9 4
                                    

Babansu Nura tun ranar da suka yi masa korar kare ya koma gida bai sake jin ɗadin duniyar ba.  Gabaɗaya ya rasa me yake masa daɗi. Tunani ya dinga yi akan me ya kaishi rabuwa da matarsa da ya'yansa akan abun duniya. Wai ina ma hankalinsa ya tafi ne a lokacin sannan kuma bai sake waiwayarsu ba na tsawon lokaci. Idan ya kori Na'ilah me su Nura suka yi masa da zai kore su a inda basuda kamarsa? Ya shiga mawuyacin hali har ya fara ciwo amma tsabar rashin sanin girma da mutuncin miji amarya bata ma san yanayi ba. Dama suna cikin gidan ma sai yayi sati biyu sai sakata a ido ba tunda dama komai masu aiki ke masa. Matsalar ta dashi kuɗi ne idan na hannunta sunyi ƙasa tazo a ƙara mata. Duk rashin hankalin da zata zo masa dashi baya tsawatar mata kuma ya rasa menene dalilin hakan. Yaransa ma babu wata shaƙuwa a tsakaninsu. Ya tuna lokacin da suke rayuwa a nutse cike da farin ciki da ƙaunar juna shida yaransa da Na'ilah. Yafi tunanin ɓarakar da ta auku tsakanin sa da Nura domin sun kasance kamar abokan juna. Yasan bai isa ya tunkari wansa da zancen ba tunda yasha yin tattaki zuwa gidansa yana nusar dashi illar abinda ya aikata amma sai yayi masa rashin kunya da korar kare.  Duniya tayi masa zafi ya rasa tudun dafawa kuma bashi da abokin shawara ko rarrashi.

_______
Sai da akayi sati uku ba'a san inda Suhaila take ba. Neman duniyar nan Abba da Umma sunyi amma babu ita babu labarinta. Ashe zuwa tayi wajen Bashir ta bashi labarin duk abinda yake faruwa ta nemi ya ɓoyeta har zuwa lokacin da Abba zai saduda ya bari su cika burinsu na auren juna. Sai a sannan yasan cewa ya tafka babban kuskure kuma ya sake tabbatar da cewa lallai ba da Suhaila yake chatting ba domin yarinyar da yake chatting da ita tanada nutsuwa da sanin ya kamata. Kuka ne kawai bai ba don takaici. Yasan cewa Allah ne ya kamashi kuma yake hukunta shi akan ta'asar da ya aikata wa yaran mutane harda wa'yanda basu ji ba basu gani ba. Gidan da abokinsa ya siya na shakatawa ya kaita kuma yake zuwa wurinta kullum da abinci da dukkan abubuwan da take buƙata. Abba yayi ta neman layinta har Allah yasa ya shiga a satin da zata dawo. Bai jira jin abinda zata ce ba kawai yace ta dawo zai ɗaura mata aure da Bashir ɗin ya kashe wayarsa. Sunyi shawara da Umaimah da ƴan uwansa maza kuma duk shawara ɗaya suka bashi akan ya aurar da ita ga muradin ranta ya bita da addu'a tunda rashin yin hakan kamar ƙara tunzurata ne akan ta cigaba da lalacewa. Ba haka yaso ba kuma zuciyarsa tana masa ƙuna amma babu yadda ya iya. Cuta dai Habi ta cuce shi kuma shima ya cuci kansa da ya tashi aure bai auri macen arziƙi ba duk da cewa bai san haka halayen ta suke ba sai bayan shekaru da aurensu. Da Suhaila ta dawo tun tana ɗari ɗari har ta saki jikinta ganin babu wanda yace da ita ci kanki akan guduwar da tayi sai ma shirye shiryen da ta ga Umman tana ta yi. Tana son yi mata magana da faɗa mata irin tsarinta akan abubuwan da za'a siya mata duk da ma Bashir ɗin ya faɗa mata gidanta an riga da an saka duk wani abun buƙata ba sai an wahala ba amma dai tana son idan ta juya a gidanta ko wacce kusurwa taga wani abu daya kasance mallakinta da iyayenta suka siya mata amma bataga fuska ba tunda dama ita ba gwanar gaisuwa bace saboda haka babu abinda yake haɗasu.

Abba ya kira Bashir yace ya turo magabatansa. Amma abinda duk basuyi zato bane ya faru domin suna neman auren aka basu kuma Abba ya nemi alfarmar a ɗaura a wurin a cewarsa jinkirin bashi da wani amfani. Dayake duk dattawa ne sai suka amince aka wuce masallacin anguwar ana idar da sallar la'asar aka ɗaura auren Bashir da Suhaila bisa sadaki Naira dubu ɗari. Ko Umma bata san haka Abba ya tsara abun ba saboda haka ranta yayi matuƙar ɓaci. Sai banbami take akan an aurar mata da yarinya sai kace bazawara. Abba yace ai bata da maraba da bazawarar kuma ta shirya ta tattarawa Suhailan abinda ya sawwaka wanda yayi mata daidai karfinsa ta bar masa gida. Taje chan ta karata Allah ya sanya alheri. Babu wanda ya sanar da Sabirah abunda yake faruwa dayake ba kowa ya sani ba hatta Hafsah bataji labari ba ballantana ta shafa mata.

_______
Semester sai gudu takeyi don har sun fara gwajin aji kuma Alhamdulillah duk tambayar da aka musu tasan amsar ta kuma tana da yaƙinin cewa zata ci da yardar Allah. Amatullahi ƙawar da tayi duk da har yanzu bata taɓa ganin fuskarta ba yarinya ce mai mutunci da kamala kuma ita ma bata da yawan surutu gata da son karatu. Tare suke fita daga aji idan lokacin sallah yayi suje suyi alwala suyi sallah kuma ko a wasa bata taɓa yiwa Sabirah korafin yadda take juya mata baya ba idan zata wanke fuska. Tasan cewa ko ma menene tana da dalilinta na ɓoye fuskarta kuma ko ba dade ko ba jima watarana zata gani idan Allah ya yarda. Sosai take jin daɗin mu'amala da ita saboda son karatun ta. sannan duk inda ɗaya ya kakare suna zama suyi wa juna bayani sosai har sai ka fahimta. Basa hulɗar da ta wuce sallama da sauran matan ajin haka ma maza. Khairiyyah kuwa ana can ana ta zuba wanka da gayu. Babu abinda ya dame ta da wani takura kai wajen yin karatu gashi ta sake haɗuwa da wasu ƴan karyan a ajinsu. Kullum Sabirah tana mata nasiha da kokarin nusar da ita akan illar abinda takeyi. Dariya kawai take mata tace bazata gane bane saboda ita bata shiga mutane. Bata san me duniya take ciki bane shiyasa take ganin kamar abunda take ba daidai bane.
Amatu ta saka Sabirah dole ta buɗe Whatsapp saboda ana yawan basu assignment, kuma a group class rep dinsu yake posting. Bayan haka ta sakata a groups masu yawa duk na karatun addini ne sai wani na koyon girke girken zamani kuma tana gwada wa Idan taga akwai kayan haɗi a gida tunda ba'a yi mata shamaki da ko ina ba. Mayen mutumi sunan da ta sakawa Nura kuwa duk sati sai yazo siyan awara kuma baya tanadi kafin yazo sai dai ya aiko yaro kuma tun ranar bata sake fita ba sai dai Khairiyyah ko Baba Zuwaira su kai masa. Bai taɓa tambayar su ita ba dukda cewa yana son ganinta sai dai bazai taɓa sarewa ba don hatta Ummi ma yana kai mata tsarabar awarar kuma tana jin daɗinta sosai. Faridah ma sauƙi ya samu shi yasa ko bai yi niyyar zuwa ba sai sun kirashi sun tuna masa akan ya taho musu da awara.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now