10

79 6 3
                                    

Bayan sati biyu da rubuta jarabawa result da admission suka fito. Amma ba public administration aka bata ba international relations ta samu. Murna a wajen Sabirah ba'a magana kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha. Ita dai burinta da fatan ta ta shiga jami'a ta samu ilimi ko ta yaya ne bawai tanada zabin course bane domin public administration ɗin ma kawai ta saka shi a Jamb ne. Tunda Khairiyyah ta santa bata taɓa ganinta cikin farin ciki da annashuwa irin haka ba.
"Eh lallai Sabs kina son bautar yahudu. Irin wannan murna haka?"
"Bazaki gane bane. Ina matukar son yin karatu kuma nasan shine gata na a rayuwa" ta faɗa da madaukakin murmushi akan fuskarta.
"Haka ne kuma. Allah dai ya sa mu fara a sa'a mugama a sa'a. Allah yasa damu da al'ummar musulmi zamu amfana da ilimin "
"Amin Khairee. In Shaa Allah su Inna zasu yi alfahari damu. Bazamu basu kunya ba "
"Wai ke yaushe zaki fara ce mata Ammah ne ? Ni ban ma san wa ya ƙaƙaba mata Inna ba. Kina ganin babata yar gaye kina wani ce mata Inna" ta haɗe rai kamar gaske. Dariya Sabirah tayi tace Allah ya shiryeta. Da Baffa ya dawo da daddare bayan sun gama cin abinci ya tayasu murnar samun admission kuma yace su dage da karatu su tsare mutuncinsu dana gidan da suka fito, banda ƙawayen banza da kula maza barkatai indai ba akan harkar karatu bane sannan kuma su dage da addu'a domin shi karatun jami'a yana da kalubale masu yawa. Ammah ma tayi musu nasiha kuma tace ita bazata saka musu ido ba duk da cewa a makarantar take aiki, ta yarda dasu da irin tarbiyyar da aka yi musu kuma su sani cewa Allah yana kallon su idan suka sa tsoronsa a ransu babu wanda zai ce musu suyi daidai ko suyi akasin haka tunda sun san cewa Allah yana kallon su ko sun boye musu ba zasu boye wa Allah ba. Godiya suka yi musu da alkawarin cewa in shaa Allah ba zasu basu kunya ba kuma za suyi taka tsantsan. Hira akayi sosai cike da nishadi ga shirye shiryen bikin Yaya Muhammad anata yi domin saura kaɗan a gama haɗa lefen da an kai kuma za'a saka rana wanda bazai wuce wata biyu ba. Baffa sai tsiya yake wa Ammah wai ta tsufa har ta kusa fara tara jikoki tace dadin abun ma shi ya tsufar da ita. Anan taji cewa Mubarak ya kusa dawowa daman project ne yasaka ya daɗe bai leƙosu ba. Quantity survey yake a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.
"Sai ku shirya zan bawa Ammahnku kuɗi kuje kasuwa kuyi siyayyah" Baffa yace lokacin da yake ƙokarin tashi ya wuce ɗaki.
"In Shaa Allah. Mun gode Baffa Allah ya saka da alheri ya ƙara buɗi" suka faɗa a tare. Murmushi kawai yayi yace musu sai da asuba ya wuce dakinsa. Yana jin dadin zaman da Sabirah take yi a gidan duk da har yanzu bata wani sake yadda ya kamata ba amma yana jin daɗin yadda take mu'amala da Khairiyyah kuma take rage mata rawan kai da karaɗi. Gashi har tuwon alkama takeyi masa da girke girken gargajiya. Ko da bata sake ba dai yasan bata cikin ƙunci da damuwa kuma babu me hantararta wanda shine fatansu.
Kafin sati ya zagayo sun je kasuwar kuma sun siyo duk abinda ya dace, suturu ne da takalma da hardcover note books masu kyau sai yadin hijabi da niƙab da Sabirah ta siyo ita kuwa oganniyar mayafai ta siyo da kayan kyale kyale ita bata yarda ba gayu zatayi da shigar alfarma ta kece raini. Sai faɗawa Sabirah take yanda take son idan aka fara semester har a gama bazata maimaita kaya ba.
"Kinsan fa yadda ake ƙarya a jami'a to bazan bari a raina ni ba nima dole na ringa shiga ta alfarma shi yasa ma na roƙi Yaya Mubarak da Muhammad wasu kudade akwai yayar ƙawata da take siyar da zafafan abayas na gwanjo su zanje na siyo kala kala na ɓadda kama ayi tunanin na Dubai ne ko Oman ko Turkey" kallonta kawai Sabirah take tana mamakin hali irin nata, duk kokarin da iyayenta ke yi akanta bata gani, ita bataga dalilin da zai sa tayi kokarin kai kanta inda Allah bai kaita ba kawai saboda  ta burge mutane. Kuma kayan da ba wanda ya saka kudi ya siya maka akan wanne dalilin zaka takurawa kanka wai bazaka maimaita ba don gudun raini. Ta tabbata wannan ba tarbiyyar Ammah da Baffa bane sai dai idan ita ta ɗaura wa kanta ko tana bin ruɗin kawayen banza. Kamar zata yi mata shiru sai kuma taga rashin dacewar hakan tunda ko babu komai ƴar uwarta ce kuma a gidansu take zaune sannan tana kaunar ta tsakani da Allah saboda haka bazata iya bari ta ɗaukarwa kanta wahala ba.
"Kinga Khairee ita fa rayuwar nan sauƙi gare ta sai dai idan kaine zaka daura wa kanka wahala. Kada ki biyewa abinda mutane zasu fada ko irin kallon da zasu miki, shi ɗan Adam ba'a taɓa iya masa, duk kokarin ki wani sai yaga gazawarki kuma ni banga abun burgewa ba don ka ɗinka sutura ka saka ta sau ɗaya ta tashi aiki ba. Karki manta da cewa wani ko kala ɗaya me daraja baida ita, wani ɗaya yake sakawa a kullu yaumin sai dai ya wanke ya sake maidawa. Allah ya mana ni'imomi dayawa kuma idan bamu gode masa ba bai kamata mu butulce masa ba. Khairiyyah kinada suturar da ko a mafarki ban taɓa tunanin samu ba amma kike kokarin haɗawa da gwanjo dan kawai ki burge wasu? Bawai ina nufin gwanjo ba kaya bane ko kuma bai kamata ki saka su ba amma na tabbata iyayenki bazasu ji daɗi ba idan suka ji labari"
Jikin Khairiyyah duk yayi sanyi duk da dai bawai ta gamsu bane. "Shikenan zan kamanta. Nagode Sabs"
"Bakomai nima na gode"  haka suka cigaba da shirye shiryen su cikin natsuwa har aka fara registration. Gabaɗaya sun manta da zancen Fiddausi dan tun da suka karɓi lambar juna babu wadda ta nemi ƴar uwarta. Fiddausi kuwa tana sane dasu jira take su kirata don kada su raina ta tunda an bata amsa. Batasan cewa daga Sabiran har khairiyyah babu wanda ya sake tada zancen. Ranar da zasu fara registration Ammah tace su karɓo confirmation letter dinsu su sameta a office. Ai kuwa Khairiyya tanata murna wai daɗin sanin wani kenan domin tana jin labarin irin baƙar wahalar da ake sha wajen registration. Suna karɓowa kuwa suka wuce office dinta. Bata nan sai da suka jira ta dawo sannan ta haɗasu da wani tace ya taimaka musu su yi komai da komai a ranar. Ai kuwa babu ɓata lokaci suka yi duk abinda ake buƙata hatta ID card sun bada passport dinsu ance za'a neme su idan ya zama ready. Admission number ma da komai sun karba harda account din school an musu creating. Godiya sosai sukayi wa mutumin dan ana tafka rana ga uban layi me tsayi su kuwa suna zuwa sai dai su shige. Allah ya isa da tsinuwa kuwa sun shata yafi cikin kwando. Sabirah nikab din data saka ya takura mata tunda bata saba ba amma hakan yafi mata sauki akan kallon da take da tabbacin za'a bita dashi duk inda ta ratsa.
A cikin masu tsine musu kuwa harda Fiddausi don dama a ƙufule take dasu gashi Faridah tace bazata rakata ba lokacin da tasha wahalar ta ai ba tare suka je ba kuma Nura yana ajiye ta ya wuce kamar wanda ake bi. Ya so tambayar ta labarin su Sabirah amma ya waske don yasan sai ta yayata shi a gidansu kuma shi har tsoron haɗuwa yake da yarinyar don ta dagula masa lissafi tana kai kawo cikin ruhi da zuciyar sa shi yasa yana ajiye ta ya bar makarantar. Tasha baƙar wahala kafin ta samu ta kammala komai kuma dan wulakanci Nura yace ta shiga Napep aiki yayi masa yawa bazai iya zuwa daukan ta ba. A fusace ta shiga gidansu tana mita. Ko kallonta Faridah batayi ba don ta lura wani tashen rashin kunya take ji tunda aka tilasta mata yin karatu. Ummi ce ma ta saurareta kuma tayi mata faɗa akan yawan korafi tunda ba ita kadai ce ta bi layin ba kowa ma haka ya wahala kafin ya gama registration din.
"Tab wallahi banda wa'yannan marasa mutuncin. Muna tsaye suka zo suka wuce da wani ko su min kara mu wuce tare"
"Kin musu magana ne suka share ki ko kuma dai faɗan rashin gaskiyar taki da kika saba zakiyi?" Ummi ta tambaye ta.
"Haba Ummi, ko nema na fa basuyi ba. Ya kamata ai da admission ya fito su kirani su ji ko na samu sannan da za'a fara registration ma su kira su ce nazo muyi tare tunda ni duk kawayena na secondary ba anan zasu yi karatu ba" ta cuna baki muryarta kaman zata yi kuka.
"Da basu kiraki ba ke kiransu kikayi? Ko kin kirasu basu ɗaga ba kuma basu kiraki daga baya ba? Ni bana son faɗan rashin gaskiya"
"Amma ai tunda ita tafara karɓan lamba ta ita ya kamata ta fara kira bani ba"
"Sai kiyi ai yar wahala. Watakila ma sun manta dake kina nan har gaba kike dasu a iska saboda kwata kwata bakida hankali " Faridah ta faɗa tana jan tsaki da takaicin ƙarfin hali da rashin aikin yi irin na kanwar tata. Ta dauki mutanen da basu ma san tana yi ba tasaka su a zuciya.
"Ummi kin ganta ko? Ni ban san me akayi mata ba kwana biyu sai hucewa take a kaina"
"Bana son shashanci Fiddausi. Faridah ba sama take dake ba ? Kuma shikenan ke ba'a isa ace kinyi ba daidai ba ko a faɗa miki gaskiya sai kice ana adawa dake?" Ummi ta tsawatar mata tace taje tayi sallar la'asar ta fito ta shiga kitchen da dafa abincin dare.
"Yanzu fisabilillahi yau din ma baza'a ɗaga min kafa ba? Nayi tunanin ma adda Faridah tayi ai"
"Sai yanzu na zama Adda wato, ba adda ba ko takobi ne malama ki fito kiyi aikin ki dan ma kin samu nayi miki sauran girki ne kaɗai yake jiranki?" Turo baki tayi ta tura dankwalinta zuwa gaban goshi tana shiga daƙin ta murza key a zuciyarta kuwa ta ƙudurta cewa tana sallah lafiyar gado zata bi ta huta. Idan sun gaji da jira sa shiga su dafa dan ita ko yunwar ma ta daina ji tsabar ɓacin ran data ƙaƙabawa kanta.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now