Sosai take jin daɗin karatun ga kuma sana'ar da take yi. Tana kiran Umma duk juma'ar sati kuma indai ta kirata sai ta yaɓa mata magana amma bata cika damuwa sosai kamar da ba saboda bata da lokacin yin tunanin abubuwan da basa tafiya daidai a rayuwarta saboda akwai abubuwa masu yawa daya kamata ta godewa Allah akan su. Gashi da taimakon Adda Khadijah sun fara samun kostomomi masu odar snacks na biki ko suna to ko daya yaushe idan basa makaranta suna gida suna sana'ar su hankali kwance cikin aminci da yardar juna domin yanzu Khairiyyah ta canza ta koma yadda take a da.Sabirah tuni ta manta da wanzuwar wani Nura a faɗin duniya sai dai shi a ɓangaren shi ba haka bane. Ya shiga damuwa sosai kuma ya rasa wanda zai tunkara ya faɗa masa abinda ke faruwa dashi. Har cikin ransa yana son sanin yarinyar domin ya taimaka mata. Gashi abubuwa sun sake kacamewa sunyi masa yawa saboda shi ke kula da dukiyarsu da kuma tashi baki ɗaya ga kuma asibiti wanda ba don yasan cewa basu da yawa wa'yanda suka karanci wannan fannin ba daya haƙura da aikin kawai. Faridah kuwa ashe da Musaddik take soyayya. Lokacin da Nura ya sani ƙaramin hauka ya kusa yi kuma yasha mamaki domin bai taɓa hasaso faruwar hakan ba amma sai dai kash! Kaddara ta riga fata domin Musaddik yace babu gudu ba ja da baya indai Ummi ta amince ta saka albarka a shirye yake da yaje neman aurenta wurin wan Baba kuma bazai damu ba idan har hakan zai kawo tangarɗa a alaƙarsu. Ƙiri ƙiri Faridah ma ta nuna masa sai dai yayi hakuri amma ita ta samu wanda take so yake sonta kuma take da yaƙinin bazai wulaƙanta ta ba saboda haka yayi hakuri ya saka musu albarka kuma Ummi ma ta bi bayanta. Babu yadda ya iya haka ya gama fushinsa babu wanda ya nuna yasan yana yi gashi bashida wani aboki face Musaddik ɗin dan har Ummi ma wani sha masa ƙamshi ta dinga yi. Ya kira layin Sabirah, ya je gidansu lokuta mabanbanta sai dai wayarta bata shiga alamar tayi blocking dinsa, idan yaje gidan kuma sai ya rasa kwarin gwuiwar shiga ko yin sallama da ita tunda maigidan da kansa ya kira ya dakatar dashi daga zuwa gidan nasa. Sai dai yana yawan hango ta daga nesa idan ya kai ƙannensa makaranta kuma kamar yadda ta faɗa alamu sun nuna cewa tana jin daɗin rayuwa kuma abubuwa da yawa sun canza ba kamar lokacin da ya fara tozali da ita ba. Lokacin da da yana da iko da ya koma ya hana faruwarsa domin kuwa ta jirkita masa duniyarsa.
Semester ta ɗau zafi domin har an kafa musu time table saboda haka gaba ɗaya a rikice suke suna ta karatu ba kama hannun yaro domin suna so suyi maintaining grade ɗinsu ita da Amatullahi. Sunje gidansu ita da Khairiyyah kuma ta sake tabbatar da cewa rashin uba ko uwa ko wani jigo na rayuwa ba shi ke hana bawa yin rayuwarsa cikin farin ciki da annashuwa ba domin idan ba ka san da cewa su Amatu marayu bane bazaka taɓa kawo hakan ba idan kaga yanayin rayuwarsu. Tabbas sunyi sa'ar jajirtacciyar mace a matsayin uwa kuma jagora. Rasa inda za'a saka su akayi a gidan dan kowa yana ɗokin ganin Beauty abokiyar Amatu. Sun sake sosai ansha hira da raha. Da suka tashi tafiya humra da turaren wuta masu daɗin ƙamshi da sanyaya zuciya wanda mamansu Amatu ke siyarwa ta basu kuma ta aika da saƙon gaisuwarta ga Ammah.
"Parrof me [(part of me) ɓangarena]" Amatu ta kira Sabirah da sabon sunan da suka ƙaƙabawa junansu tana taɓa ta domin ta ɗago kanta.
"Wancan kamar wannan Dr Nuran. Kamar kuma wurinki zaizo" Dam!! Ƙirjin Sabirah ya buga amma ta waske ta cigaba da abinda take yi kamar Amatu ba da ita take magana ba.
"Kinsan ban cika son ana raina min hankali ba. Malama da ke nake"
"Dan Allah parrof me ki rabu dani. Karatu nake kuma ni ban sanshi ba"
"Kaji min ƴar rainin wayo. Saurayin naki ne baki sani ba?" Ba shiri Sabirah ta ɗago kanta tana zare ido.
"Yaushe na taɓa faɗa miki cewa shi saurayina ne? Me yasa ke da Khairiyyah baku da wani burin daya wuce ku haɗani alaƙa da wanda banda alaƙa dashi kuma bana fatan hakan ya faru?""Relax, cool down madam. Wasa nake amma naga har kin ɗau zafi kina kokarin kare kanki. Ko dai ko dai?" Ta ɗaga mata gira. Tsaki tayi tana jin haushin Nura da ya sake yi mata kutse a cikin rayuwa ko maye albarka abu an kusa shekara amma yaƙi haƙura ya barta ta sarara. Tana ta zancen zuci kuma duk mita take akan Nura har ya iso da sallamarsa. Amatu ce ta amsa masa a fili amma ita oganniyar a zuciya ta amsa.
YOU ARE READING
ƳAR BAƘA
General FictionSabirah baƙa ce. Irin baƙin nan mai maiƙo, ga muryarta mai kauri da amsa kuwwa. Tana fuskantar tsangwama da izaya kala kala a wajen mahaifiyarta da ƴan uwanta da babu wata ƙauna da shaƙuwa a tsaƙaninsu. Shin zata iya haƙuri da ƙulubalen rayuwa ko ku...