6

55 9 0
                                    

ƳAR BAƘA
Written by Aishatu Humaira Bello
Humylash @wattpad. 

BABI NA SHIDA (6)

Washegari da safe Abban nasu ya dawo kuma yace ta zauna cikin shiri gobe zasu wuce Gomben da asuba. Motar farko yake son su shiga domin yana kaita zai juyo dan bazai kwana a gidan suruki ba. Izinin Umman ta nema ta wuce gidan su Hafsah don sun gama planning din tsarabar da zata kai wa su Innar daga cikin ribar data samu. Yajin da yayar Hafsan ke siyarwa da spices ta siyawa Inna, sai tea mix na Baffan su Khairiyyah, mutuniyar tata kuwa alawar madara da gullisuwa da Hafsan keyi ta siya mata dayawa. Har hango yadda zata yi tsalle ta ɗane ta take yi don khairiyyah ba'a barta a baya ba wajen barkwanci. Manyan yaran Innar maza Muhammad da Mubarak ta siya musu body spray na maza. Sukayi packaging komai gwanin ban sha'awa sai zumudi Hafsah keyi kamar ita zata tafi don ita bata ci Jamb ba so take yi ta samu ko FCE ne ko Polytechnic ta fara kafin ta sake yin Jamb din.
" Tashin hankali na ɗaya da kikace da asuba zaku wuce don har nayi niyyar aje miki komai a wajena sai goben na shigo na kawo miki"
"Me yasa? Ai dama nazo mu karasa shirin ne na nunawa Umma"
"Amma kuwa lallai baki da hankali ko nace bakida wayo. Kema kinsan ko zata bari ki kai musu sai ta tsige ki tas kar waccar roommate din take me kwailalliyar fuska taji labari. Dan tana iya cinye kayan khairiyyah a daren kafin gobe"
"Ikon Allah! To ya kike so ayi?"
"Malama idan zaki waye ki bude ido ki waye. Ban ce kiyi wa Umma rashin kunya ba amma dai gaskiya ki daina bari ana kwarar ki dayawa. Abun da za'ayi shine muje na rakaki tunda Abba yana gida ki nuna mata a gabansa sai ki mika masa kice ya saka miki a kayan sa ke babu wuri a jakarki. Nasan zai gane wayon da kika yi ya karba. Duk iskancinta ai bata isa ta shiga dakin sa ba ko?" Hafsah ta dage tana bayani kamar wata yar jagora.
"Ai shikenan. Yadda kikace din haka za'ayi kawas. Gaskiya zanyi missing ɗinki sosai idan na samu admission na koma chan"
"Kibari kawai ai ko tunanin hakan bana son yi amma wallahi har kasan zuciyata ina miki addu'a da fatan ki samu din. Kuma dan Allah ki cire tsoro da wani noqe noqen da kike yi a cikin mutane. Ke mutum ce kamar kowa kuma Allah ya san hikimar sa da yayi ki a baƙa. Idan ban taɓa faɗa miki ba to yau zan faɗa kiji. Kinada matukar kyau Sabirah, kaf yaran gidanku babu me kyanki kuma da zaki ringa kallon kanki a madubi zaki gane hakan. Ki sani cewa bawa baya wuce kaddararsa kuma Allah baya zalunci, baya wulakanta bawansa sai idan shi ya wulakanta kansa. Ina son kada ki bari kowa ya hantareki ko ya wulakanta ki a Gombe. Kema mutum ce kamar kowa. Dan Allah kada ki bari maganganun da su Umma da Suhaila suke faɗa a kanki suyi tasiri. Yanzu ne zaki shiga duniya ki fara sabuwar rayuwa ki hadu da mutane kala daban daban daga mabanbanta wurare da al'adu. Saboda haka sai kin jajirce." Haka Hafsah ta cigaba da bata shawarwari da karfafa mata gwuiwa kafin suka tattara komai suka nufi gidansu.
"Abba Barka da yamma an wuni lafiya?" Hafsah ta tsugunna ta gaishe da Abban bayan sun gaisa da Umma.
"Lafiya kalau Hafsatun Sabirah, ya baban naku fatan kowa lafiya?"
"Lafiya kalau Alhamdulillahi. Bai dawo ba tukunna yana wajen aiki."
"To Allah yayi jagora yayi muku albarka " suka amsa da amin Hafsah nata zungurin Sabirah akan ta aiwatar da plan din su. Suna zaune a wajen har Umman ta kosa da shirun nasu, su basu magantu ba kuma basu tashi sun shige dakin su Sabiran ba.
"Umma, Abba, daman tsaraba ce na hadawa su Innar Gombe shine nace gashi ku gani ko sunyi" da ta gaji da mintsinin da Hafsah ke mata ta faɗa a dan tsorace. Tana addu'a da fatan kar ayi tsiyar da aka saba. Wuff umma ta janyo gift bag din tana buɗe kayan daya bayan daya tana tabe baki.
"Yanzu ke Sabirah a ina kika samo kudin da kika narka wajen siyan wa'yannan kaya masu tsada haka?" Umma ta tambaya cike da al'ajabi. Idan tace bata morar sana'ar Sabiran tayi karya domin kuwa ko bata tambaye ta ba tana daukan wani abu ta bata sannan ta daina tambayar kudin omon wanke wanke da wanke banɗaki haka ma sabulun wankin da take mata duk daga aljihunta take siya. Sannan kullum tana da awarar Naira dari ko sama da haka idan tayi baki kuma ta basu kyauta.
"Banda abunki Habi, yarinyar dake sana'a kike tambaya inda ta samo kuɗi? Irin wannan ai sai dai ki tambayi Suhaila. Kuma wa'yannan kayan ba masu tsadar da za'a ce ina ta samo kudin siyarsu bane"
"Ai dole kace haka tunda sam baka kaunar laifin yarinyar nan. Idan banda neman suna daga zuwa jarabawa shine zata haɗa uban kaya haka da sunan tsaraba? Ko matan aure ma yanzu ai ba kowa ke tsaraba idan zaiyi tafiya ba sai ita ƴar iya" ta cigaba da fada tana jujjuya body spray din tana son tasan kudinsu.
"Kaya sunyi Sabirah kuma nasan zasuji dadi. Allah yayi miki albarka ya ƙara budi. Tashi ki tafi kinji" Abban ya fada yana mamakin rashin hankali irin na matarsa. A gaban kawar ƴarki ma sai kin nuna bakya son ta bakya kaunar ta? Kullum addu'ar shiriya yake mata saboda yasan akwae ranar dana sani da kuma lokacin da Sabiran zata kangare ta daina yi mata biyayyah duk da cewa baya fatan zuwan wannan rana.
Ganin ta fara hada kan kayan tana kokarin tashi su wuce dakinsu ne yasa Hafsah yin caraf tace wa Abban ai kayan bazasu shiga cikin jakar Sabirah ba sai dai ya haɗa a kayansa. Nan da nan ya gane hikimar yin hakan domin da har zaice ai shi ba kaya zai dauka ba tunda a ranar zai juyo. Ya karba kuwa ya shiga dakin da kansa ya boye don yanda yaga matar tasa ta sakawa body sprays din ido yasan tana iya dauke su tayi neman suna dasu ko ta bawa Suhaila duk da cewa na maza ne.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now