27

57 5 2
                                    


Tun Sabirah na kaucewa kiran Nura har ta bada kai bori ya hau kuma tunda ya fahimci cewa ta bawa karatunta muhimmanci sosai sai yake ɗaga mata ƙafa baya takura mata sai lokacin da ta samu sararin yin waya sannan yake kiranta. Shaƙuwar da sukayi a baya wasa ne akan wadda sukayi yanzu domin har waya take bawa Khairiyyah da Amatu su gaisa sannan sunyi conference call da Hafsah ƙawar da batada kamarta a faɗin duniya. Tun sunayi mata tsiya akan soyayyah take da Nura tana nuna rashin jin daɗin hakan har ta haƙura ta daina sababi akan cewa ita ba soyayya suke yi ba. Ta dai tabbatar musu da cewa ko da yana sonta to bai kai ga furta mata ba.

Suna waya yake bata labarin tafiyar Faridah Korea siyayyar kayan ɗaki. Kamar zatayi nauyin baki sai ta fasa tace.

"Allah Sarki, Allah ya kai su lafiya ya dawo dasu lafiya. Dan Allah idan babu damuwa ina da saƙo"

"Amin ranki ya dade. Menene saƙon naki? Zan faɗa mata kuma zan tabbatar da cewa bata dawo ƙasar nan ba sai da saƙonki in shaa Allah"

"Fin ƙarfi zaka yi mata kenan? Ni dai ka lallaɓata ta siyo min. Daman naji ance kayan gyaran jikinsu suna da kyau. Zan tura mata kuɗi sai ta ɗan samo min na shafawa baƙar fuskata ko zata yi fasali"

Ɓata rai yayi kamar tana gabanshi yace "kefa matsalata dake kin iya cin fuska. Zan faɗa mata in shaa Allah. Zancen kuɗi kuma ki riƙe abunki idan ta siyo sai a haɗa lissafi"

"A'a bazan yarda da wayon nan ba. Haka kace min wai kunyi zancen kuɗin Form da registration na koyon ɗinki da Baffa ashe kaine ka biya. Dan Allah ka daina min hidima. Ka ga ni banda alaƙa dakai kuma Kanada yan uwa da mahaifiya da kake kula dasu. Bai kamata ace ka ɗaurawa kanka nauyina ba kuma dai ina sana'a ina samun na kashewa sannan ga Baffa da Ammah na tabbata duk abinda na tambayesu zasu bani indai suna da hali "

"Allahu Akbar Sheikha Sabeeeraah. Idan kin gama fatawar taki sai ki sanar dani. Ni dai da baki na bance zan biya ba cewa nayi idan ta dawo za'a yi lissafi. Yanzu dai ki shiga yanar gizo ki duba kalar kayan nasu da kike so ki turo min da sunan sai na faɗa mata saboda kada taje tayi miki shirme"

"Bana so na fasa" ta faɗa a ɗan shagwabe.

"Kanki ake ji Malama. Ina jiranki. Sai anjima zamuyi magana. Ki kular min da kanki" ya sakar mata dariyar mugunta ya kashe wayarsa.

Haushi ne ya turnuke sabirah tana jin haushin tambayarsa da tayi tunda ko ma menene ya faru ita taja wa kanta. Khairiyyah ta faɗawa ta tayata shige shige harda su Pinterest sai da suka samo abinda suke so sannan ta tura masa sunan kamfanin da kayan da take so. Gwalo ya turo mata a matsayin reply ai kuwa ya ƙara bata haushi tace sai tayi maganinsa zai san ita yayi wa gwalo.

Sai da su Faridah sukayi wata ɗaya a Korea sannan suka dawo kuma kaf ahalin gidan Baffa babu wanda ba'a kawo wa tsaraba ta bajinta ba. Saƙon Sabirah kuwa Korean skin care products ne kamar wadda zata buɗe shago haka aka jibgo mata su. Hatta Amatu da Hafsah sai da suka samu rabonsu. Baffa da kansa ya kira Nura yayi masa faɗa akan abinda yayi sai cewa Baffa yayi ai shi a ƴan uwa ya ɗauki su Sabirah, Baffa da Ammah kuma a matsayin iyaye. Ummi da su Faridah kuma sunyi tambayar duniya akan kayan da yasa a jibgo na suwaye ne yaƙi faɗa kuma shine karo na farko daya taɓa boyewa mahaifiyarsa abu. Bata ja zancen da tsawo ba tunda dai tasan ko ba dade ko ba jima idan abinda take hasashe ne to zata sani idan lokaci yayi. Tsiya dai ya shata wurin ƙannensa da Musaddik da ya riga yasan wurin wadda aka kai kayan.

"Ya kamata ka dinga bani girma fa. Surukinka ne ni ba aboki ba" ya faɗa yana shan mur.

"A inda babu suruki kenan. To banda abunka sai na rasa wanda zanji kunya sai kai? Ai wallahi babu ruwana da surukata ko Ummi ma kallon mahaifiya nake mata ballanta kai karan kaɗa miya" Musaddik ya faɗa yana masa kallon raini.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now