23

42 7 0
                                    

Ranar da  Bilkisu zata koma ɗakinta ƙin zuwa su Sabirah sukayi sai da Ammah tayi musu jan ido kafin suka tashi shima kuma sun ɗau alwashin cewa idan tayi ƙoƙarin yi musu rashin mutunci babu makawa sai sun rama. A hanya suna tafiya suna hirar su har Khairiyyah take cewa tunda kusa da gidan Adda Khadijah ne ya kamata su ɗan leƙa tunda sun kwana biyu basu je ba.

"Ai kuwa dai ya kamata mu je. Kawai idan mun isa sai mu kira Ammah mu tambaye ta kinsan yanzu tana iya cewa a'a tunda tasan bamu so zuwa gidan Yaya ba."

"Haka ne kam. Bari mu ƙarasa ɗin"

A falo suka tarar da Bilkisun tana mopping da alama babu wanda yayi mata rakiya shi kuma gogan yana ɗakinsa kamar mara gaskiya. Ba dan ba zai iya yiwa Ammah musu ba da babu abinda zai saka ya dawo da Bilkisu gidansa. Gaisawa sukayi a mutunce kamar ba ita ba sai kuma ta bawa Sabirah tausayi saboda haka sai ta kalle ta tace "Akwai abinda za'a taya ki  yine?"
Kai Bilkisu ta girgiza kafin tace "a'a ai daga wannan na gama. Me kuke son ci sai na dafa muku idan na ƙarasa?"

"To Bari mu taya ki girkin idan babu damuwa" Sabirah tace tana kokarin tashi ta wuce kitchen. Babu yadda Khairiyyah ta iya haka ta bita suka wuce takaicin Sabiran fal ranta.

"Ke wallahi kinada matsala. Duk alwashin da muka ci akan matarnan har ta baki tausayi kina kokarin taimaka mata"

"Tausayi ta bani sosai Khairee. Kuma da alama dai ta saduda tayi taubatan nasuha. Kiyi hakuri komai ya wuce dan Allah "

"Ya na iya tunda ustaza ta saka baki ai dole na manta komai" a ɗan ƙanƙanin lokaci suka dafa fried rice dayake Yaya Muhammad ɗin ma dasu yaje kasuwa suka siyo kayan miya. Dakyar ya yarda aka siyo dayawa saboda yace shi yana tsoron a sake yi masa asara kamar farkon aurensu da duk abinda ya siyo haka zata bari ya lalace batare da tayi amfani dashi ba.

Bilkisu tana ƙarasa mopping ɗin ta shige ɗakinta ta tsala wanka tayi kwalliya ta ɗaukar magana. Tasan tabbas ta cuci kanta kuma batayi wa Muhammad da tsaftacciyar soyayyarsa a gareta adalci ba. Gashi wanda take haukan domin sa ma yayi aurensa da kuma tayi ƙorafi akan hakan ya zage ta tas yace me zai yi da mace mara kamun kai irinta me waya da saurayi da auren wani a kanta. Ai shi ba mahaukaci bane yasan me yake yi. Anan ne ta gane cewa Allah ya so ta da rahama da saki bai shiga tsakaninta da Muhammad ba domin kuwa tasan da tayi asara kuma har abada bazata sake samun mutum mai nagarta irin tasa ba. Ƙawayenta ma tun ranar da abun ya faru babu wadda ta sake nemanta, ita ce ma take nemansu a waya daga baya ta watsar. Jira take taga karshen rashin kunyar su ko zasu zo mata gida idan suka samu labarin cewa ta koma. Fitowa tayi da addu'a a bakinta na fatan Allah yasa kar Muhammad ya gwasaleta ta wuce ɗakinsa.

A kwance ta same shi yana kallo a TV. Bayan amsa sallamarta da yayi bai sake kallonta ba ya cigaba da abinda yake yi. Zamewa ƙasa tayi ta tsugunna kusa da ƙafarsa tace " Nasan Ni me laifi ce a wajenka kuma  na cancanci duk wani hukunci daga gareka. Amma ina roƙon alfarma a wajenka dan Allah, dan darajar Annabi Muhammadu (SAW) ka bani dama domin na wanke laifukan da nayi maka. Nasan da wahala ka sake yarda dani amma dai ina rokon alfarmar ka bani dama ta karshe"

Sai da aka ɗauki lokaci me tsawo kafin Muhammad ya kalle ta yace "Tashi ki zauna" babu musu ta tashi ta zauna kusa dashi kanta a ƙasa domin har cikin ranta tana jin kunyarsa da abubuwan da ta aikata masa.

"Akwai abinda na taɓa yi miki da sanina ko a rashin sani da ya baki damar wulaƙanta ni?" Ya tambaye ta fuska a murtuƙe babu alamun wasa.

"A'a babu, idan kuma nace da akwai nayi maka sharri sai Allah ya saka maka. Sharrin shaidan ne da zugar ƙawayen banza amma in shaa Allah nayi alƙawarin hakan bazai sake faruwa in shaa Allah"

"Tashi kije naji. Allah yasa da gaske kike. Sannan ban yarda ki kawo min kwashi kwaraf ɗin ƙawayenki cikin gidana ba tare da izini ba. Ƴan uwanki kawai na yarda su zo amma bayan haka ban yarda da takarcen banza ba"

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now