15

65 9 0
                                    

Sabirah ta samu farin ciki da kwanciyar hankalin da bata taɓa tsammanin samu ba sai dai damuwa ce danƙare a ƙasan zuciyarta na rashin neman ta da Umma tayi. Tana son kiranta taji lafiyarta don har ta ƙosa tayi wa Abban magana akan ya bari ta kirata su gaisa yace mata a'a ba yanzu ba tayi haƙuri idan sukayi hutu shi da kansa zai zo ya ɗauketa tayi hutu a gida. Ta tambaye shi zancen Suhaila yace ai tayi aure tuni. Abun ya daki zuciyarta sosai kuma ya ɓata ranta amma bata faɗa ko nuna masa hakan ba sai fatan alheri da ta yi mata. Ace ƴar uwarta uwa ɗaya uba ɗaya tayi aure a kasa faɗamata sai bayan satittika? Ita kuwa me tayiwa ahalinta da basa ganin girmanta ko darajar ta duk da cewa tasan Abba ba da manufa mara kyau ya ɓoye mata zancen auren ba. Hafsah ma cewa tayi bata sani ba, ta dai  daina ganin Suhaila kuma zatonta an hanata fita ne sannan ba zuwa gidan su Sabirahn take ba tunda ta taho Gombe. Da ta faɗawa Khairiyyah ce wa tayi ta sani tunda taji Ammah tana waya da Abba ranar da aka ɗaura auren. Bata tambaye ta dalilin ƙin faɗa mata ba don tasan yanzu sai ta hauta da masifa don kullum zuciyarta a kusa take da Sabirah kuma iya tunani tayi amma ta kasa gane dalilin hakan tunda dai lafiya ƙalau suke kuma basu cika zaman gidan ba idan ba weekends ba saboda shirye shiryen jarabawa. Hatta awarar da suke yi ta daina saka hannu sai dai tana kwance a ɗaki ayi wahalar kuma ta karɓe kuɗaɗen tunda a account ɗinta ake turawa sai daga baya suke cire uwar kuɗi ribar a tura account ɗin Sabirah. Amma yanzu mirsisi taƙi turawa tana jiran Sabirah tayi mata magana ta mata rashin mutunci amma hakan bai samu ba don ko kallon inda take batayi wannan kuma huɗubar mutuminta  Yaya Mubarak ne don ya tsareta ya tambaye ta ta faɗa masa gaskiya akan me ya haɗasu da Khairiyyah kuma tace masa batayi mata komai ba shine yace ta fita a sabgarta ta nuna bata san tanayi ba.

Khairiyyah kuwa maƙasudin jin haushin Sabirah ya samo salsala ne daga irin yadda kowa na gidan yake kaffa kaffa da ita, ake yabonta da janta a jiki sannan komai tayi daidai ne har ana cewa tayi koyi da ita. Kafin zuwan Sabirah ita ce ta gaban goshin kowa amma yanzu duk ta kwace mata fada ga shegen iyayi da ustazancin tsiya. Abu kaɗan ta fara Allah yace Annabi yace, Ammah da Baffa bazasuji dadiba. Gani take idan bata ci duniyar ta da tsinke ta sakata ta wala ba a jami'a sai yaushe zata samu damar watayawa? Tunda dai ita ba bin maza take ko shaye shaye ba ai bataga laifin ta ba idan tayi cruising. Kaita makaranta da ɗaukotan da Yaya Mubarak ya wajabtawa kansa yana mugun ɓata mata rai gashi Yaya Muhammad ma sai wani sakata yake a sabgar bikinsa dayake ta ƙaratowa.  Tana kwance a kan gado tana chatting da plate din da tagama cin abinci a saman bedside drawer wanda bazata ɗauke ba sai dai idan Sabirah ta gaji da ganinsa a wurin ta ɗauke Sabiran ta shigo da fara'a a fuskar ta. Kallo ɗaya tayi mata taja tsaki ta cigaba da danne dannen wayarta. Take fara'ar fuskanta ta gushe jikinta yayi sanyi. Ta shigo ne domin ta sanar da ita cewa Yaya Mubarak ɗin yace zai biya musu kuɗin online classes na kwalliya da koyon girke girken zamanin da suka daɗe suna son shiga idan anyi hutu. Bayan ta cire kayanta tayi wanka ta zauna kusa da ƙafar Khairiyyah tace 'Khairee kin san me ?"  Ɗago kanta kawai Khairiyyah tayi batare da ta bata amsa ba.
" Yaya Ba yace zai biya mana kuɗin online classes ɗin nan sannan idan muna buƙatar kayan kwalliya da abubuwan buƙata na girke girken zai siya mana"
"Mtsww shine kike ta wani rawar jiki kamar anyi miki albishir da gidan aljannah? Allah ya bada sa'a don ni na fasa bazanyi ba. Banda rainin hankali bazai fara faɗa min ba sai ke? To kije kiyi ke kaɗai bana so. Sannan Yaya Ba ɗin nan ya fita a bakin ki tunda ba ke kika saka masa sunan ba. Ni dana saka masa sunan ban isa na kira shi dashi ba sai wata banza?" maganar da tayi tayiwa Sabirah zafi sosai. A tunanin ta duk ɗaya suke a yanda Khairiyyah ta nuna mata farkon zuwanta ko dayake ba laifinta bane nata ne data manta matsayinta a gidan da rayuwa baki ɗaya har take neman zaƙewa amma in shaa Allah zata kama kanta kuma ta tsaya a matsayinta.
"Allah ya baki haƙuri" ta furta tana kokarin bar mata ɗakin.
"Ai hakuri ya zama dole. Zama da munafuki ai sai mai mugun haƙuri irina. Kina wani simi simi kamar ta kwarai bayan zuciyar ki ba mai kyau bace" ai kuwa zancen Khairiyyah na ƙarshe a kunnen Ammah da ta dawo taji su shiru kuma babu kowa a falon tazo taga me suke yi. Ta riƙe hannun ƙofar kenan zata buɗe kalaman Khairiyyah suka shiga kunnuwanta. A fusace ta banko ƙofar tayi kan Khairiyyah ta kwaɗa mata mari ba tare da ta tsaya jin ba'asin zancen ba.
"Ashe dama Khairiyyah baki da kirki ban sani ba? Sabirahn kike cewa munafuka? Munafurcin me tayi miki? A cikin gidana ake wulaƙanta ƴar ɗan uwana? Wanne irin sake kika samu a cikin gidan nan kike abinda ranki yake so? Yarinya tana sonki tana ƙaunar ki tana rufa miki asiri amma kike zaginta? Duk abubuwan da kike a cikin gidan nan ina sane shiru nayi na zuba miki ido ina taraki. Hatta kuɗin awarar da ba aikinta kikeyi ba kuma ki riƙe Baba Zuwaira ta sanar dani duk shiru nayi miki ashe ban sani ba harda zagi kike zama kina yi mata" Nan Ammah ta wanke ta tas. Ta rasa bakin magana sai kuka kuma ƙiyayyar Sabirah na ruruwa a cikin ranta. Sai da Ammah tagaji tayi shiru ta juyo kan Sabirah, ita ma kukan take.
"Me ya haɗa ku?"
"Babu komai Ammah, dama Yaya Ba ne yace zai biya mana kuɗin online classes na girki da kwalliya da muke so shine na faɗa mata  ta fara faɗa. Ammah dan Allah kiyi hakuri ki tayani tambayar ta ko nayi mata wani abu ne take jin haushina sai na bata haƙuri kuma na gyara" Ammah ji tayi kamar ta saki kuka. Tayi tunanin a yaranta babu wanda ta koyawa halin banza kuma ta yarda da cewa ba zasu ara su ɗaura wa kansu ba shi yasa da confidence dinta ta karɓi amanar Sabirah kuma tayi wa ɗan uwanta alkawarin cewa bazata taɓa wukaƙanta ba ashe ba haka bane ? Ka haifi ɗa ne kayi masa tarbiyyah sannan ya baka kunya ? Ficewa tayi daga ɗakin. Tana fita kuma Khairiyyah taja wani dogon tsaki tace "an dai yi asara. Kuma mai shiga tsakanin uwa da ƴarta ya cika ƙungurmin munafuki" Tashi Sabirah tayi ta bar mata ɗakin kafin ta faɗa mata maganganun da suka fi haka ɗaci. Kitchen ta wuce tana taya Baba Zuwaira aikin abincin dare kuma ko a fuska bata nuna mata ranta a ɓace yake ba sai ma hirar da suka fara.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now