30

59 11 0
                                    

Kiran da akayi wa Bashir ya gigita shi yadda bai taɓa zato ba domin yana falon mahaifiyarsa suna shirya irin cin mutuncin da zasu yi akan ɗa ko ƴar da Suhaila zata haifa domin ko da tsiya ko da tsiya tsiya sai sun rabata da babyn saboda a ganinsu jinin Bashir yafi ƙarfin a raine shi a gidan matsiyata kamar yadda suke kiran gidan Abba sai kuma kwatsam aka kira shi akan tana asibiti rai a hannun Allah.

"Ai sai ka tashi ka tafi kafin su ƙara laƙaba maka laifi akan bata da lafiya baka je ba" Mamansa ta faɗa tana taɓe baki.

"Wallahi kunya nake ji. Bana son haɗuwa da Abbanta" ya faɗa yana sosa ƙeya.

"Kaji min shashancin banza da wofi. Kunyar me? Su da ƴarsu ta gudu basu nemeka ba sai kai ne zaka ji kunyar su ?" Ta hayayyaƙo masa.

"Allah ya baki haƙuri. Bari naje naga me ke faruwa. Zan kira na sanar dake idan da buƙatar kizo"

"Kada ma ka kuskura ka kirani dan wallahi ba inda zanje, Kaji na gaya maka. Sai danace kada ka auri dangin matsiyata ka kafe ka nace. Ga yaran arziki daga gidan manyan mutane masu faɗa a ji ka tsallake ka kwaso mana wahala. Kaje chan ku ƙarata ni babu ruwana" taja tsaki ta wuce ɗakinta.

Dayake akwai go slow ko da Bashir ya isa asibiti har Suhaila ta sauka sai dai ƴar tana da matsala saboda haka an kaita inda ake bawa jarirai kulawa ta musamman (NICU). Suhaila da taji zafin da duk wata mace da Allah ya azurta da haihuwa takeji sai ta rusuna kuma ta jinjinawa mata musamman wadda ta kawota duniya. A take taji wani girma da ƙimar umma ya mamaye mata zuciya kuma tasan cewa lallai mata na jihadi. Tana son ta bata hakuri kuma ta jinjina mata sai dai ta galabaita sosai kuma bata da bakin magana gashi tana ji tana gani ko jin dumin ƴar data haifa batayi ba aka wuce da ita. Umma kuwa baki yayi tsami ya kumbura. Su Ammah ne ma da matar wan su Abba ke ta mata sannu saboda taje gidan kai musu abinci ta tarar da mummunan labarin abinda ya faru shine ta wuto asibitin.

"An auna arziƙi tunda ta sauka lafiya" Mama ta faɗa tana kallon Suhaila cike da tausayawa.

"Alhamdulillah kam abun yazo da sauki fiye da yadda ake tsammani" Ammah ta bata amsa. Umma dai binsu kawai take da kallo amma a zuciyarta ba abinda take sai tsinewa Ammah da ahalinta kuma da tanada hali sai ta shaƙeta har lahira. A duniya ta tabbata bata da maƙiyi sama da Ammah.

Sallamar Bashir ne ta katse musu zancen da suke.

"Sannunku ina wuninku?" Ya faɗa yana rarraba ido.

"Yawwa kaina sannu" Ammah ta amsa tana masa kallon sama da ƙasa.

"Ya me jiki? Dafatan ta sauka lafiya?"

"Gatanan ka ganewa idonka" shiru yayi ya tsaya a tsaye kyam kuma dukkan mazauna ɗakin babu wanda yayi alamar zai fita domin basu damar zantawa shi da matarsa. Suhaila ganinsa sai da gabanta ya faɗi kuma ya tayar mata da soyayyarsa dake danƙare a cikin zuciyarta. Da Bashir ya gaji da shirun ne ya kalli bangaren da Umma take yace " Ina abun da aka haifa?"

Umma na kokarin buɗe baki ta bashi amsa Ammah tayi caraf tace " Mun siyar, Kanada asara ne ?"

"Umaimah meye haka kike yi ne? Babu ruwanki da lamarin da ya shafi ƴata ki tashi ki bamu wuri " Ummah ta buɗe bakinta dakyar tana makawa Ammah harara.

"Idan kinada ƙarfi sai kizo ki fitar dani Habiba ɓarauniyar mutum" jin haka sai Umma tayi muƙus ta zauna tana muzurai. Suna zaune sai ga Baffa da Yaya Muhammad sun shigo. Bayan sun gaisa dasu ne Baffa ya nemi ganin Bashir a waje.

Faɗa yayi masa sosai  tas ya wanke shi soso da sabulu ya faɗa masa cewa dalilin abinda ya aikata yasaka Abba cikin matsananciyar damuwa yanzu haka shima yana kwance a bangaren majinyata maza an bashi gado saboda jininsa ya hau sosai.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now