20

62 6 0
                                    

Har suka koma makaranta second semester Nura bai sake zuwa gidan ba ko neman ta a waya. Hakan yayi mata domin ko ba komai sun samu daidaito tsakaninta da Yaya Mubarak ya daina wannan yawan hasala da faɗan nasa kamar yadda ya tsira a ƴan kwanakin. Sun koma yadda suke da hankali kwance babu hayaniya ko tashin hankali. Ji take kamar ta tsayar da lokaci domin ya kusa shiga camp domin bautar ƙasa kuma tasan abune mawuyaci a barshi a Gombe dole sai yayi mata nisa. Sosai suka ɗinke da Amatu gashi an kafa result kuma sune toppers ɗin class ɗinsu. Kowa na son sanin wacece Sabirah Muhammad ko don a amfana da iliminta amma tayi mirsisi taƙi buɗe fuskarta.

"Yanzu kam ina bayanki wallahi. Ki cigaba da saka niƙab kawai saboda da sun ganeki kin shiga uku academic donkey zasu mayar dake ayita ɓata miki lokaci ana amfana dake ke kuma ki rasa lokacin yin karatu" Amatu ta faɗa bayan wasu yan ajinsu maza sun zo seat ɗin da suke suna tambayar wacece Sabirah Muhammad a cikinsu.

"Ni abun ma har mamaki yake bani. Last semester fa har tsaki suke idan sun ganmu saboda suna jin haushi bama shiga harkarsu amma shine yanzu suke bibiyar mu" Sabirah ta faɗa tana ƙara gyara zaman niƙab ɗinta.

"Kema dai kya faɗa" haka suka cigaba da hira kafin malamin da zai musu lectures ya shigo.

Khairiyyah kuwa tuni ta dawo daga rakiyar su Ayush da Nadiya. Gashi ta kwaso kaya har courses uku Allah dai ya taimake ta ba prerequisites bane. Sosai Baffa yayi mata faɗa ya nuna ɓacin ransa yace ya kamata ta dage kamar yadda Sabirah tayi, bai ce sai dole tafi kowa points ba amma ko yaya ne tayi iyakar kokarinta wajen ganin bata faɗi ba. Ammah kuwa kashedi ta sake yi mata akan bin su Ayush, tace idan ta sake ganinta da su ko taji labarin suna mu'amala sai ta cire ta a makaranta kuma tasa yaya Muhammad ya lallasa mata ita. Tana zaune a gaban class tana danna waya taji an zauna kusa da ita. Bata ɗago kanta ba domin ta san ko ma wanene indai wurinta yazo zai yi magana.

"Khairiyyah kin bani mamaki wallahi. Akan dan abinda bai kai ya kawo ba shine kika daina harka damu hadda wani dawowa da zama a gaba. Kin bi kin takura kanki" Ayush ta faɗa a hasale. Ko kallo bata ishi Khairiyyah ba haka ta karashi ɓaɓatunta ta gama ta hakura ta wuce.

"Muna nan tare dake sai kinyi dana sanin wulaƙantani da kikayi. Ko baki neme ni dan Allah ba kwadayin abun duniyar ki zai kawo ki. Banza kawai" taja wani dogon tsaki ta ƙara gaba. Ba domin bata son tayi abinda zai sake ɓata ran Ammah ba, babu abinda zai hana Khairiyyah yiwa Ayush ɗan banzan duka. Maganganun data yaɓa mata sunyi mata zafi sosai amma haka ta danne zuciyarta tanata ambaton sunan Allah domin tayiwa kanta alkawarin bazata sake barin shaiɗan yaci galaba akanta ba. Har akayi musu lectures aka gama zuciyarta na mata suya amma haka ta danne ta bada dukkan hankalinta domin fahimtar abinda ake koya musu. 

Da aka tashi zama tayi a wurin da suka saba jiran juna ita da Sabirah domin yaya Mubarak bazai samu damar zuwa ɗaukansu ba yanada ayyuka dayawa a gidan gonarsa. Sabirah tun daga nesa ta san ba lafiya ba domin mutuniyar tata sai jijjiga ƙafa take yi.

"Nasan dai ba yunwa kikeji ba tunda na hango ki a mini mart ɗazu kina cin abinci. Waya taɓo mana autar Ammah?" Ta faɗa cikin raha tana kokarin zama kusa da ita.

"Tashi mu tafi gida kawai" Khairiyyah ta faɗa tana kokarin share hawayen da batasan ya akayi suka silalo kan fuskarta ba.

"Subhanallahi Khairee, me ya faru ? Me aka miki? Dan Allah ki bar kuka hakanan ko ma menene ki daure kiyi haƙuri idan munje gida sai ki faɗa min" riƙo kafaɗarta tayi kamar mara lafiya suka taka zuwa bakin gate. Sunyi sa'a babu cunkoso nan da nan suka samu abun hawa suke shige.  A nan ne Khairiyyah ke labarta mata abinda Ayush tayi mata.

"Ban taɓa dana sanin biye musu ba irin yau Sabs. Wai har ni Ayush zata kalla tace wa idan ban nemeta dan Allah ba zan nemeta dan kwadayin abin duniya "

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now