37

66 6 0
                                    

Sai da Khadijah ta kwana biyar sannan Ammi tazo Kano. Dayake lokacin ta koma gidan Mama acan suka haɗu saboda bataje airport ɗauko ta ba tana tayi mata girke girken tarbarta. Da gudu taje ta rungume Amminta tana yi mata sannu da zuwa kamar wata ƙaramar yarinya.

"Yau ni nake ganin rashin kunya da tsakar rana"Mama ta faɗa tana yi musu dariya.

"Ai sai dai kiyi haƙuri kawai ki rufe idanuwanki Hajiya Mama" Ammi ta bata amsa kafin  zauna suka gaisa sosai. Sun sha hira har yamma kafin suka wuce gidan Baba domin Ammin ta gaishe shi. Sai da suka kusan tafiya sannan Baba yayi gyaran murya yace.

"Fatimah ina son ki dubi girman Allah ki saka Umar ya saki matarnan hakanan. Idan bazaki iya hakuri ba to ki shigar da ƙara kotu ayi muku Shari'a. Wannan abinda kike yi fa zai iya komawa zalunci kuma. Maganar nan ta wuce don Allah. Na tabbata ita ma ta gane kurenta yanzu"

Shiru Ammi tayi kamar bazatayi magana ba kuma sai ta ɗago da kanta ta share kwallar da ta gangaro saman fuskarta.

"Nima Baba ba daɗin tsare tan da akayi nake ji ba kuma da tunaninta nake kwana nake tashi. Kawai maganganun da ta dinga faɗa ne a ranar da asirinta ya tonu suke min yawo a kai. Bana son a saketa ta zama barazana ga rayuwar Khadijah tunda muguwa ce tana iya yin komai. Amma zan yi wa yayan magana sai a sake ta in shaa Allah amma sai anyi mata iyaka da Khadijah"

"Hakan ma yayi daidai. Allah yayi miki albarka ya albarkaci zuri'arki ya kuma jikan mahaifiyarki"

"Amin Baba. Allah ya ƙara lafiya da nisan kwana mai amfani"

"Yaushe zaki kai Khadijah Ethiopia taga dangin mahaifiyarki?" Ya tambaya bayan sunyi shiru na wani lokaci.

"Ina nan ina ta shiri Baba. So nake ta gama aji uku tunda hutun yafi yawa sai muje idan Allah ya kaimu da rai da lafiya"

"Madallah. Allah yasa muna da rabon ganin lokacin"

"Amin" suka amsa baki ɗaya. Da suka fito ne Ammi tace ta gaji Khadijah ta tuƙa su. Nan tayi wuri wuri da ido kamar mara gaskiya.

"Ya akayi?" Ammi ta daga mata gira alamar tambaya.

"Ai Ammi hannuna bai faɗa sosai ba. Ina tsoro kar na kifar damu a titi" ta bata amsa tana sosa ƙeya.

"Motar da aka siya miki kuma fa? Wake zuwa makarantar da ita?"

"Khairiyyah ce take kaimu "

"Course ɗinku ɗaya ne ko lokutan lectures ɗinku iri ɗaya ne da kullum ita zata dinga jan ku? Kuma ke baki san cewa da koyo ake kwarewa ba? Idan bakya hawa motar kina tuƙi ta yaya zaki kware? Kuma ita Amman tana kallo bazatayi miki magana ba? Meye amfanin siya miki motar kenan?" Ta faɗa tana mata kallon takaici.

"Ba laifin Ammah bane Ammi. Kullum sai tayi magana ita da Baffa. Niɗin ce kawai bana son tuƙin kuma naga Khairiyyan bata damu da tuƙa mu ba"

"Ba wani nan, kin dai sakar mata motar saboda tafiki rawan kai da kuma son a sani. Tun lokacin da aka baku motar ina ankare da ita. To bazai yiwu ba. Daga gobe kafin jibi mu wuce zaki cigaba da koyan mota kuma ina so ki kware kafin hutunki ya ƙare ki koma. Wannan ai shashanci ne da shirmen banza" haka ta cigaba da yi mata faɗa tana cewa bata ce ta nuna wa Khairiyyah iko ko kuma tayi mata gori ba tunda sunyi mata komai a lokacin da bata da gata amma kuma ba ta son ta zauna ana taka ta ana tauye mata hakki saboda tana gudun zancen mutane.

"Shi ɗan adam da kike gani ko me zakiyi a duniya bazaki taba biyansa ko ki burgeshi ba. Shi yasa ake so a ko yaushe ka kasance me yin abu dan Allah. Idan kin yi dominsa kinga baki da matsala ko fargabar za'a yaba miki ko a'a. Tunda dai dominsa kika yi kuma ladan ki na wurin sa"

"Haka ne Ammi. Zan kiyaye in shaa Allah. Kiyi hakuri hakan bazai sake faruwa ba"

"Ba kiyi min laifi ba my daughter. Kawai ina koya miki dabarun zaman duniya ne"  Abbu suka kira suna yi masa tsiya akan an baro shi a Lagos shi kaɗai. Ashe yaso tahowa shima tsayawa yayi yiwa Mubarak cuku cukun samun permanent aiki a kamfaninsu shiyasa baizo ba.

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now