Bayan wata huɗu Hisham da Rukayyah suka fahimci junansu yadda babu wanda yayi tsammani domin kuwa ita kanta Rukayyah tana mamakin yadda ya saki jiki da ita. Shi kuma yayi hakan ne saboda baya son ya bawa Khadijah kunya sannan aunty Nafisah ma ta karfafa masa gwuiwa akan in shaa Allahu alheri ce Rukayyan a gareshi. Dayake ita tuni tayi degree ɗinta harda masters bayan wata shida aka ɗaura musu aure akayi walima aka kaita gidan mijinta. Tun a lokacin ta so ɗauko Afnan amma Ammi taƙi tace ai an riga da an basu Afnan saboda haka babu inda zataje. Sannan ba za'a dinga yi wa yarinya wasa da hankali ba akan karatun ta. Ba haka Rukayyah taso ba amma ta haƙura akan duk hutun makaranta Afnan ɗin zata dinga yi a wajensu. Khadijah tayi bajinta sosai lokacin bikinsu domin ita ce ƙirjin biki ko a fuska bata nuna cewa abun ya dame ta ba kuma hakan da tayi ya ƙara mata ƙima da daraja a idon iyayenta.
Su Khadijah sun gama makaranta lafiya kuma ita ce best graduating student a set ɗinsu da first class mai ƙarfi sai Amatu da ke mara bata baya sai wani ɗan ajinsu namiji. Iyayensu, ƴan uwa da abokan arziki sunyi murna sosai da saka albarka. A lokacin kuma sun shiga wata ƙungiyar masu siye da siyarwa. Sun ƙara wayewa akan harkan business duk abinda suke so yi wa kansu suke yi batare da sun jira anyi musu ba. Daga graduation sai aka fara shirye shiryen biki domin har Ummi sai da Ammah ta gayyata taron. Duk yadda tayi akan Khadijah ta saki jikinta da ita akan an zama ɗaya ita ma ƴarta ce kasawa tayi saboda nauyin ta da take ji da kuma sanin cewa tun asali ita ce bata sonta da Nura. Bata tunanin kuma akwai abinda Ummin zatayi da zai wanke ta gaɓadaya a idanun ta.
A lokaci ɗaya aka kawo lefensu kuma duk Ammi tace a karɓa a Gombe basai anyi wahalar zuwa Kano ko Lagos ba. Baffa ya yaba sosai da dattakon su saboda duk wani shirye shiryen da akeyi sai an tambayi ra'ayinsu. Lefe yayi kyau na ƴan gayu ƴan boko masu class. Ba'a yi ƙarya ba sai dai an saka kaya masu kyau da daraja kuma unique. Khairiyyah sai kauɗi ake yi lefe yayi kyau mashaa Allah kuma sai da ta samu hanyar da su Ayush suka ga lefen don kawai ta cusa musu baƙin ciki. Naima ce kaɗai ƙawarta ta amana sai kuma ƙawayenta na secondary school. Khadijah tana kallon ta tana ta shirye shiryen yin bridal picnic harda dinner idan an Kaita Kano.
"Amarya in tambaye ki mana. Nace wai dan Allah Ammah tasan duk irin shirye shiryen nan da kike yi ko kuwa dai ke kaɗai kike kiɗanki kike rawar ki?" Khadijah ta tambayeta bayan ta nuna mata wani material tana tambayar ko zai mata kyau idan ta saka shi ranar dinner.
"Kema kinsan bata son bidi'a kawai so nake sai nagama shirya komai sannan na faɗa mata sai na roketa ta bari kinsan zata yarda tunda bazata so ayi asarar kuɗin da aka kashe ba"
"Lallai kanki babu mai a cikinsa sam Khairiyyah. Ko million dari kika kashe ina tunanin Ammah bazata amince ba. A gabanki tayi waya da Maman Yaya Sa'ad ta tabbatar mata da cewa ba'a bidi'a a gidan nan bayan walima da yinin biki amma shine kike shiri harda dinner. Kuma nasan shima Yaya Sa'ad ɗin ba so yake ba. Ki hakura kawai albarkan auren ake biɗa ba burge mutane ba"
"Amma yanzu fisabilillahi Sabs ace ina ƴar auta kuma ƴar gata ace a bikina babu wani Shagali mai ƙayatarwa?" Ta turo bakinta gaba saboda ita harga Allah ba haka taso ba.
"Ita walimar bata ƙayatarwa kenan? Sannan kin manta lokacin da yaya Bilkisu take ƙunci akan haka abinda kika faɗa? Dan Allah Khairiyyah kiyi hakuri ki bar zancen nan. Bana so daga baya rayuka su dinga ɓaci dan Allah."
"Idan dai ba faɗa mata zakiyi ba Allah zata yarda idan nagama shirin komai"
"Khairiyyah kenan. Ana ƙoƙarin a rabu lafiya kina son a rabu ana jin haushin juna. Ni bazan faɗa mata ba amma idan ta tambayeni bazanyi mata ƙarya ba sannan idan abubuwa suka kwaɓe ki kuka da kanki."
Ai kuwa Khairiyyah bata fasa shirye shiryenta ba sai da ta gama komai ta haɗawa Yaya Sa'ad bill yace sam bai san zancen ba saboda mamansa ta faɗa masa yadda sukayi da Ammah kuma an rigada an sanar da mutane sannan shi kansa abubuwan nan bawai suna burge shi bane.
YOU ARE READING
ƳAR BAƘA
General FictionSabirah baƙa ce. Irin baƙin nan mai maiƙo, ga muryarta mai kauri da amsa kuwwa. Tana fuskantar tsangwama da izaya kala kala a wajen mahaifiyarta da ƴan uwanta da babu wata ƙauna da shaƙuwa a tsaƙaninsu. Shin zata iya haƙuri da ƙulubalen rayuwa ko ku...