43

50 9 0
                                    


Satinsu uku da hutu aka fara yajin aikin da ba'a san ranar komawa ba. Takaici kamar ya kashe Khadijah domin sun fi awa ɗaya suna waya da Amatu tana mita akan hakan. Ammi ma bataji daɗi ba amma dai hakan ya bata damar ƙara ƙaimi wajen yi mata international passport da visa domin daga Ethiopia tana son su wuce ƙasa mai tsarki suyi Umra kafin lokacin Hajji idan da rai da rabo sai su sake zuwa tare harda Abbu.

Hankali kwance take hutunta kuma take sake wayewa da harkar kasuwanci domin har ta fara yiwa kamfanin su Abbu kwangilar lunch. Kullum tana kitchen tana girki saboda haka bata cika bin Ammi shagunanta ba. Mubarak yayi nacin su koma yadda suke da har ya gaji kuma yanata mamakin dama tana da riƙo da zuciya sosai har haka? Ita kuwa bai san tana tsoron su samu kusancin da zai sake sawa zuciyarta tsatsa ba. Haka dai suka cigaba da ƴar hi, hi idan an haɗu basa wata doguwar hira. Kullum sai ta kira Ammah da Baffa ta gaishesu kuma sosai suke jin daɗin hakan. Yaya Muhammad ne ba kullum ba kuma shima sai ta kira shi sau uku, huɗu a lokuta mabanbanta bai ɗauka ba kuma bai biyo kiran ba. Tayi masa uzurin ko aiki ne yasha masa kai shi kuwa yana iya kokarinsa wajen ganin ya yakice ta daga zuciyarsa domin samun zaman lafiya da kuma tsira da mutuncinsa.



Wata ranar juma'a Khadijah tana zaune a falo bayan ta gama duk wasu ayyukanta ta miƙe ƙafafuwanta a kan three seater tana karanta Wani littafi tana zabga murmushi ita kadai domin littafin yana mata daɗi kuma characters ɗin suna bata nishaɗi sosai. Ƙarar ƙararrawar gidan ce ta katse mata hanzari ta turo baki tana mitar waye yazo musu gida da tsakar ranar nan?  Mayafin rigar dake jikinta ta ɗauka dake ninke a gefenta kafin ta saka slippers ɗin da take yawo dashi a cikin gida ta wuce buɗe kofar.

"Waye?" Ta tambaya bayan ta leƙa taga an juya mata ƙeya kuma namiji ne. Idan taji waye daman zata faɗa masa masu gidan basa nan ya dawo idan sun dawo.

"Hisham ne Khadijah. Munyi waya da Anti Fatimah tana hanya" Muryarsa mai taushi da bazata taɓa mantawa ba ta faɗa sai kuma taji muryar wata ƙaramar yarinya tana cewa "Abba ita ce aunty Khadijan da kake bani labari kace nayi koyi da halayenta na gari?" Bata tsaya jin amsarsa ba ta buɗe gidan tana binsa da kallon mamaki. Kwata kwata bai mata kama da mai aure ba kuma yarinyar tana kama sak dashi ba kuma zata wuce shekara huɗu ko biyar ba.

"Sannunku da zuwa. Bismillah" tace tana basu wuri domin su shigo cikin gidan. Yarinyar ce ta fara shigowa tayi caraf ta rike hannun Khadijah tana mata murmushi.

"Hey cutie! Ya sunanki?" Khadijah ta duƙa daidai tsawon yarinyar tana maida mata da martanin murmushi.

"Afnan sunana, ke kuma aunty Khadijah right?" Ta faɗa da gurɓatacciyar hausar da daga ji kasan bata iya sosai ba.

"Haka ne. Ku ƙaraso daga ciki" ta bata amsa tana jan hannunta Hisham da ya tsaya yana kallonsu ya ƙarasa shigowa bayan ya rufe gidan. Ruwa ta kawo musu da lemo sannan ta ɗebo musu abincin da ta gama dafawa mutanen gidan. Sannan ta zauna.

"Ina wuni? Anzo lafiya?" Ta gaida Hisham dake shan ruwa kamar ya shekara bai sha ba ita kuwa yarinyar lemo ta buɗe ta kafa kai.

"Afnan kinyi Bismillah kuwa? Kinsan wanda yake ci ko shan abu ba tare da yayi bismillah ba to yana ci da shaiɗan ne"

Kallonta yarinyar tayi galala kamar taga wata sabuwar halitta tace "Lah! Haka Abba ma yake cewa. Na manta amma bari nayi yadda kika ce. Bismillah" sai Khadijah tayi dariya kawai.

"Lafiya ƙalau Alhamdulillah Khadijah. Ya karatu ya hutu da rayuwa?" Ya bata amsa yana kokarin zuba abincin da ta kawo da plate. A zuciyarta mamakinsa take kamar wani tsohon mayunwaci ko ɗan Fulakon nan bayayi. kamar ya shiga zuciyarta yace "Sai kinyi haƙuri dani kwanana uku banci abinci ba sai ruwan shayi gashi munyi doguwar tafiya"

ƳAR BAƘAWhere stories live. Discover now