Shaƙuwa mai karfi ce ta shiga tsakanin Sabirah da Nura har ya kasance duk abinda ya faru da ita tana faɗa masa shima yana faɗa mata. Har wannan lokacin kuma bata yarda suyi waya kuma da suka koma makaranta yace zai zo ya ganta ma ƙi tayi saboda a ganinta kamar bata kyauta wa su Ammah ba idan tayi haka ba tare da izinin su ba. Khairiyyah ta gama sadaƙarwa anci ɗan uwanta yaƙi ba tare da ya farga ba amma ko kaɗan bataji haushin Sabirah ba tunda tasan a wauta irin tata bata fahimci cewa Yaya Mubarak sonta yake ba. Fatanta kawai Allah yasa Nura na gari ne kuma zai riƙeta amana idan har Allah ya ƙaddara zamansu ma'aurata.
Bayan Sabirah ta fito daga Library tana jiran Khairiyyah su wuce gida ne ta shiga Whatsapp suke hirar yanda kunya tayi ƙaranci a zamanin nan sannan sai ka ga mace iya mace da iliminta da tarbiyyarta da komai amma ta dinga waƙe waƙe da raye raye a kafafen sada zumunci kuma ta saka da wanda yake muharraminta da wanda ba muharraminta ba ya kalla har ya adana a wayarsa ma ko ya yaɗa batare da sunji ko ɗar ba. Suna ganin hakan cinyewa ne sannan babu aibu idan sun aikata hakan domin abune da ya zama ruwan dare kowa yi yake. Hatta matan aure ma ba'a bar su a baya ba tsabar lalacewa da rashin sanin girma da darajar da Allah yayi musu a matsayinsu na mata ababen killacewa.
"It's like bama tunanin lahira duniya kawai muka saka a gaba. Sannan yawanci wa'yanda baka taɓa zaton zasu aikata haka ba sune suke yi da kayi magana ace baka waye ba ko kuma imani a zuciya yake sannan Allahu gafurur raheem ne. Amma ni babban tashin hankali na bai wuce yadda mutuwa bata bawa mutum notis ba sannan idan kayi abu kasan mafarinsa amma baka san ƙarshen sa ba sannan ita wayewa indai ba ta addini bace to wallahi wayewar banza ce da ta wofi wadda zata kai mutum ga halaka da dana sani mara amfani" ta rubuta ta tura masa.
"Zancen ki gaskiya ne Sabeeraah. Haƙiƙa yanzu duniya ta rufe mana ido sannan shaiɗan ya samu masauki a cikin rayukan mu har ta kai ga abubuwa da dama munsan cewa basu da kyau, basu kamace mu ba amma sai mu kau da kai akan rashin dacewar aikata su mu dinga aikatawa saboda kawai bama so ayi babu mu kuma kada wa'yanda suke yi suga gazawar mu ko rashin wayewarmu. Kamar yadda kika faɗa da zamu dinga tunanin lahira a ko wanne daƙika sannan mu a karan kanmu mu dinga yi wa kanmu hisabi sannan mutuwa ta zame mana ishara akan cewa ita fa rayuwar nan bata da tabbas sannan ko ba dade ko ba jima zamu koma wa mahaliccin mu to babu shakka za'a samu karancin aikata saɓo. Yes! Dan adam ajizi ne kuma tara yake bai cika goma ba amma ana so mutum kullum ya kasance yana nesanta kanshi daga saɓawa mahalicci kuma yana kusantar da kanshi wajen yi masa bauta da biyayyah. Allah dai yasa mu dace ya kuma tsarkake mana zukatanmu ya shirye mu da zuri'ar mu baki ɗaya" ya turo mata da amsa.
"Amin. Kuma ka lura da cewa yawancin abinda yake sa mutane basa hankalta shine zaka ga mutum ya ƙare rayuwarsa yana cin duniyarsa da tsinke, yana zalunci ko aikata alfasha amma har ya mutu bai girbi abinda ya shuka ba. Wannan shine zai sa mutane suga cewa to ai suna taka tsantsan akan gaibu ne tunda babu wanda ya taɓa mutuwa ya dawo domin bada labarin abinda ya tarar a lahira. Ina tsoron rayuwar nan sosai shi yasa kullum nake addu'a. I'm really scared of going astray ( ina tsoron kauce hanya)"
"Mu cigaba da addu'a da kuma ƙoƙarin bin dokokin Allah da Manzonsa. Da ikon Allah ba zamu taɓe ba"
"In shaa Allah"
Haka suka cigaba da hirar su cike da nishadi domin basa zama su ɓata lokaci suna zancen banza wanda bazai amfane su ba. Shiyasa take shagala ta manta a ina take ko da wa take zaune idan suna musayar saƙo da Nura. Tana mugun ganin ƙima da mutuncinsa sannan ya sake jaddada mata cewa kowa da ta gani a rayuwa yana da ƙalubalen da yake fuskanta banbancin kawai shine na wani yafi na wani kuma Allah yana jaraba bayinsa ta hanyoyi kala kala ba domin baya son su ba sai domin ya gwada imaninsu sannan Ubangiji baya ɗaura wa bawa ƙaddarar da bazai iya ɗauka ba sai dai idan shi ya gaza. Shiyasa ake so a ko wanne hali bawa ya tsinci kansa ya kasance me godiyar Ubangiji sannan ya duba wanda yake ƙasa dashi ba sama ba domin hangen nesa baya haifar da komai sai dana sani.
YOU ARE READING
ƳAR BAƘA
General FictionSabirah baƙa ce. Irin baƙin nan mai maiƙo, ga muryarta mai kauri da amsa kuwwa. Tana fuskantar tsangwama da izaya kala kala a wajen mahaifiyarta da ƴan uwanta da babu wata ƙauna da shaƙuwa a tsaƙaninsu. Shin zata iya haƙuri da ƙulubalen rayuwa ko ku...