Babu abinda lokaci baya gusar dashi musamman idan bawa ya yarda da ƙaddararsa kuma ya karɓeta hannu biyu yana da yaƙinin cewa Ubangiji ya fishi sanin abinda yake ji a zuciyarsa kuma da sannu zai musanya masa abinda ya rasa da wanda yafi alheri a gareshi. Khadijah ta cigaba da rayuwarta kamar Nura bai taɓa wanzuwa ba haka shima ya ɗauki dangana duk da cewa daidai da rana ɗaya bai taɓa mantawa da ita ba. Ummi dai tana kan bakanta amma abubuwa sun daidaita a gidan sai dai ta ciki na ciki.
Yaya Sa'ad yazo har Gombe neman izini a wurin Baffa abinda yayi matuƙar yi musu daɗi kenan kuma sun saka anyi musu bincike akan Sa'ad ɗin ba tare da sanin kowa ba duk da sun yarda da nagartar ahalinsu Abbu amma dai ba'a shaidar mutum a zamanin nan kuma duk abinda addini ya tanadar yace ga yadda za'ayi to ya kamata mutum yabi dokokin saboda akwai hikima akan hakan sannan ƙin yin yadda ya dace baya haifar da komai sai dana sani mara amfani.
Khairiyyah rasa inda zata sa kanta tayi don murna saboda abune da bata taɓa tunani ba. Ta zata sun rabu da Sa'ad rabuwa ta har abada don har tayi kukanta akansa ta haƙura, ashe dan halal yana nan yana mata shirin bazata. Sai da suke hira ne yake bata labarin yanda Khadijah ta wanke shi tas a kanta. Tayi mamaki sosai kuma girmanta ya ƙaru a idonta saboda ko da wasa bata taɓa nuna mata tasan abinda yake wakana ba ko sunyi zancenta dashi. Haƙuri ta bashi tare da yi masa alkawarin abu makamancin wannan bazai sake faruwa ba. A hankali yayi mata nasiha kuma yake nusar da ita illar abinda take aikatawa. Ta gamsu da zantukansa tunda ita ba jahila bace tana da sani daidai gwargwado saboda haka tasan tabbas gaskiya yake faɗa mata. Kwana biyu yayi ya koma amma kememe yaƙi yarda da kwana a gida a hotel ya sauka. Sunyi yawo sosai da Khadijah sun nuna masa wurare sai tsokanarta yake akan ta saje ta zama ƴar gari kawai zasu aurar da ita anan. Allah ya taimake ta ƴan kauɗin basa kusa da tasan sai Khairiyyah ta kwafsa mata. Yayi musu siyayyah sosai kafin ya tafi ana dokin juna.
"Ashe kinsan munyi faɗa da Yaya Sa'ad shine baki taɓa faɗa ko nuna kin sani ba?" Ta tambayi Khadijah dake goge hijabanta da ta dauko daga shanya. Bata yarda ayi mata wanki. Tafi ganewa da tayi da kanta.
"Me zance miki tunda bakya so na sani? Yanzu ba anyi walƙiya mun ganku ba?"
"Nagode Sabs. Allah ya bar min ke"
"Da akayi me? Ko har yanzu kina cikin shauƙin soyayyar ne shiyasa kika fara sambatu?"
"Wai ni me yasa ban iya abun kirki ba sam sai an gwasaleni?"
"Saboda baki saba ba shiyasa"
"Wai nikam ina Dr. ? Ina ta son tambayarki naga tunda ya bayyana manufarsa bai zo kun gana ba kuma kamar ma bakwa waya" Khairiyyah ta faɗa tana gyara zamanta a bakin gado.
"Yana gidansu" Khadijah ta faɗa tana tamke fuska. Khairiyyah ma daga nan bata sake cewa komai akan zancen ba don har Ammah sai da ta tambayeta tace bata sani ba. Tsakaninta da yaya Mubarak ma gaisuwa ce ta wayar Khairiyyah don ko ya kirata bata amsawa.
________
Allah yayi wa mahaifin Bashir rasuwa. Mutuwar da tazo musu a bazata domin ko ciwon kai baiba sa'i yayi aka zare ransa ya koma gidansa na gaskiya. Ba ƙaramar kaɗuwa ahalinsa suka shiga ba saboda duk da cewa ansan mutuwa tana kan kowa babu wanda ya kawo masa ita a lokacin da ta riske shi. Sunyi kuka sun godewa Allah kuma sunyi masa addu'a har akayi bakwai aka watse. Abun takaici kuma Suhaila bata taka ƙafarta taje gaisuwa ba kuma daga kan Yaya Idris, Abba, Abbas, Maama, Mama har Umma babu wanda bai je musu gaisuwa ba don Umma har zama sai da tayi kuma a lokacin ne taga Halima matar Abba. Shima Abban ta gansa sai taga ya ƙara kyau da ƙiba da kwarjini. Sun gaisa cikin mutunci har Abba yana binta da kallon tausayi don sosai take jin jiki kuma babu sana'ar yi sai abinda Abbas ya samo ya bata. Maama ma da fara'a akan fuskarta suka gaisa har take yi mata ya jiki saboda Abbas ya faɗa mata cewa bata jin daɗi lokacin da ya ɗauki Imam zasu je dubata. Kuka ne kawai Umma bata yi ba amma tasan cewa ta cuci kanta iya cuta kuma idan har mutanen da ta zalunta basu yafe mata ba to Allah bazai barta haka ba anan duniya kenan kafin aje lahira inda kowa zai girbi abinda ya shuka kuma babu halin dawowa a gyara kurakuran da aka aikata.
YOU ARE READING
ƳAR BAƘA
General FictionSabirah baƙa ce. Irin baƙin nan mai maiƙo, ga muryarta mai kauri da amsa kuwwa. Tana fuskantar tsangwama da izaya kala kala a wajen mahaifiyarta da ƴan uwanta da babu wata ƙauna da shaƙuwa a tsaƙaninsu. Shin zata iya haƙuri da ƙulubalen rayuwa ko ku...