Babi na daya

1.6K 127 10
                                    

4:00 pm

1st August, 2016

Kaduna, Nigeria.

Hadari ne ya mamaye garin gabadaya, daidai lokacin aka fara wani iska Mai karfi kafin kace kabo garin yayi bakikirin alamun ruwa Mai karfi na dab da saukowa. Dole ya sa motocin da ke kan titi su ka fara driving a hankali saboda da kyar su ke ganin gaban su.

Agogon hannun shi ya duba sannan yayi concentrating akan driving in da yake da kyar ma ya ke iya ganin gaban shi.

Roundabout in Oando ya bi ya shiga constitution Road, kaman ance daga kanka ya hango wata budurwa na kokarin tsallaka express in ko duba gaban ta ba tayi kaman ma hankalin ta ba ya jikin ta. Motan da ke gaban shi ma da budurwar ta shigawa gaba gudu yake sosai kaman zai tashi sama kafin ya ankara yaji wani irin kara daya sa shi yin parking ba shiri. Sai hango wanna budurwar yayi tayi sama sannan ta fado akan glass in moton ji kake tas tas glass in motan ya dagar gaje rolling budurwar ta Kara yi sannan ta kife akan kwalta daidai lokacin ruwa Mai karfi ya sauko kam da bakin kwarya, salati ya ke a fili ci ke da shock in abinda ya faru right a gaban shi.

Ko kafin ya je har mutane sun fara taruwa suna wa Wanda ke cikin motan masifa ganin ba a fito ba, Tinted glass ne hakan ya sa ba a gane Wanda ke ciki ba.Ganin karfin ruwan ya na karuwa ya sa dayawa daga cikin mutanen su ka ja baya sai sannan ya samu ganin budurwar da gabadaya jini ya gama bata Mata jiki. Tsaki ya ja da karfi hade da girgiza Kai "ko miye amfanin rufe ta da suka yi suna Kallon ta?" Ya tambayi kanshi. In ma ba karya idanuwan shi su ka mishi ba to tabbas ya hango masu kokarin daukan incident in a waya, girgiza Kai yayi Yana fadin "Allah ya shirya Mana wannan zamani namu" a kasan zuciyan shi.

Sai sannan Wanda ke cikin motan ta samu fitowa abin mamaki Mace itama da ba zata wuce 25 Years ba hade da danta a hannu, Yaron sai kuka ya ke ba ta bi ta kanshi ba Saboda ita ma kanta jikin ta rawa ya ke kaman za ta fadi kasa.

Cinciban yarinyar yayi ya bude bayan motan shi ya sa ta sannan yayi wa motan key, Wanda ke wurin su kayi yo kanshi suna tambayan Ina za shi da ita? Ko Kallon su Bai yi ba ya sa wa motan key ganin haka ya sa su kayi baya.

Komawa motan Matan ta yi ita ma ta bi bayan shi da sauri.

Unguwan rimi ya nufa direct ya dau hanyan nursing home, Barau  dikko yayi parking. Yana isowa nurses su ka fiddo yarinyar su ka daura ta kan gado Emergency aka tura ta zuwa cikin asibitin da sauri.

Da sauri ya bi su cikin asibitin ita ma Matan saurin binshi tayi rike da danta a hannu sai a sannan ya juya ya kalle ta gabadaya ta rude tafiya kawai ta ke ba wai hankalin ta na jikin ta bane.

Wayanta ne ya fara ruri tayi saurin dauka. "Lfy har yanzu ba ki Kara so ba?" A ka fada daga dayan bangaren

Ba ta San lokacin da ta saki kuka ba Jin muryar shi "Lfy me ke faruwa" ya fada a rude.

"Ka zo Barau Dikko " kawai ta fada sannan ta yi ending call in.

Accident and Emergency room aka nufa da ita da sauri ya je ya canja kayan surgery su ka shiga operation room tare da wasu Yan uwan shi doctors da nurses. Cike da kwarewa su ka fara aikin nasu.

Ta ka sa zaune ta kasa tsaye sai kai wa da kawo wa ta ke zuwa yanzu har yaron nata ya fara kuka. Bayan Yan mintuna Wanda su ka yi wayan ya karaso a rude "Mimi na lafiya me ya faru?" Ya tmby ganin yanda ta rude gabadaya.

Labarin Rayuwata Where stories live. Discover now