Service ya kawo Amal garin Lagos, da farko gidan Friend in shi ya tura ta zama. Sai dai ba ta cika sati daya ba a gidan ta fuskanci akwai takura a al'amarin gidan sosai wanda ba haka ta saba ba a gidan su, she is free to do everything she likes. Hakan yasa ta tattara kayan ta ta koma daya daga cikin apartments in baban ta da ke lagos in. Ko da ya samu labari ya tmby ta ya akayi kawai ce mishi tayi she needs to be comfortable, shknn zancen ya mutu. A lagos mu ka hadu da Amal kasancewar ta mutum mai rauni tana gani na a hali na taimako ta ceto ni, a wannan lokacin nima in bautar kasan na ke a asibitin koyar na jam'iar lagaos a Ikeja. Ta sani a jikin ta sosai ba tare da wani shakku ko fargaba ba. Tare mu ke zama a Abuja a gidansu, ko kuma Lagos a apartment inta.
Tunda nasan ta nasan Zaid, na kuma san alaka mai karfi da take gudana a tsakanin su. Zan iya cewa suna rayuwa ne kaman na mata da miji duk da ko ba auren tsakanin su. Iyayen ta sun ki bashi auren ta duk da yana da burin hakan amma hakan bai hana ya shigo gidan su freely duk time in da ya ga dama ba a matsayin Friend in ta ko kuma yazo wurin Salim, wanda tare su kayi karatu a UK.
Kusan su in Kwarya tabi kwarya ne saboda shi inma dan masu hannu da shuni ne. Baban shi babban Custom officer ne da yaji kudi har ya gode Allah kafin yayi ritaya. Intrestingly, maman shi kuma na aiki da SSS ne. Business in Telecommunications ya ke yi a Abuja sai kuma Natural drinks da ya ke da shops in su branch branch a cikin Abuja. Shakes, Zobo, Ginger, Smoothies, mocktails, Yoghurt nd ice cream. Ba mu dade da haduwa yayi offering employing ina karkashin Drinks shop in shi duk time in da nake Abuja. Amal ba tayi wani tunani ba sai ma jin dadin da tayi, i get something to lives on. I really enjoy the work, the pay and everything.
Da shigar doguwar play gown na atamfa da Dan karamin veil na fito falon. Zaune su ke akan dinning suna breakfast ko kuma ince brunch, Shabiyu da rabi na rana har ya gota.
"Sis ina zuwa haka?" Amal ce tayi maganan da spoon in da zaid ya sa ma ta a baki, shi ke ba ta abincin.
"Shopping, ina son toiletries and some groceries. Akwai abinda kike bukata ne?"
"Just pomegranate, ina son yin cocktail in shi"
"Yaya na fah" na fada ina kallon Zaid, tun dazu ya ke faman Satan kallon fuskana.
Siririn murmushi yayi Wanda ya tsaya iya labba "Kanwata kenan, ai kin San mai na ke so" nan take na gane abinda ya ke nufi. Harara n shi nayi, amma idon Amal hararan wasa ne "Kaima kasan ba zaka taba samun wannan ba, I can't never go that far"
Clueless Amal cewa tayi "Jikin abinki Sis kinji, Traffic in Lagos in nan ina mutum zai yi nisa" bansan lokacin da na saki dariya. A wurin Amal Zaid na ke wa dariya, shi kuma a wurin shi ita na kewa dariya. Unknown to them dukkan su na kewa dariyan. Cikin farin ciki na isa store in, bayan na gama dukkan siyayyan da zanyi ne na ja motan sai Unguwar agege.
A bakin wani katon gida nayi parking, sai dai duk girman gidan bai da plasta ko fenti a jikin shi. Tun daga kofan gidan na fara cin karo da matasa, yan mata da Yan dudu. Daga masu shan sigari, tabar wiwi sai ko masu faman caca ga kuma kidan da ke ta faman tashi. Duk inda na wuce shewa za kaji na tashi suna kiran "Ah Yar baiwa manya yau an shigo kenan" daga musu hannu kawai na ke na wuce a haka har na karasa cikin gidan, inda dakuna ke nan birjik.
"Ah ah kawa yau kece a gidan namu" daga baya na naji an fada, saurin juyawa nayi muka hada ido da zeenah. Rungume juna mu kayi cike da farin ciki. "Yau lafiya da kanki a gidan namu?"
"Kawa fa ban son sharri sai kace da in ban zuwa?"
"Yaushe rabon ki? Ke da sai dai a ganki a mashaya" dariya mu ka kwashe dashi irin na yan duniya, hade da tafa hannu. "Yau dai nazo ai, Allah ya sa mutuniyar ta na nan"

KAMU SEDANG MEMBACA
Labarin Rayuwata
Fiksi Umum"Believe me ba wani abun birgewa a labarin Rayuwata shi yasa na gwammaci mutuwar akan Rayuwa irin wannan" idon ta a bushe karoro ta ke maganan ba alamun kuka ba wai don kukan ba Zama dole ba Aa, ta gaji da kukan ne saboda Bai da amfani a gareta do...