Talatin da hudu

230 52 4
                                    

Rayuwata

Babi na bakwai

Wannan karon Yaya baba da kanshi ya maida ni makaranta. Ba laifi tunda su ka fara shiri da Anty Nainah ya ke dan kyautata min. Wannan karon ma da alamun Anty Nainah ya ke son gani. Kayana na dauka nayi cikin school, ko da na dawo ba iske su tsaye da Anty Nainan Suna magana. Tana ganin ta saki fara'a, banyi mamaki haka kuma ban hade rai ba sai dai still ban mata dariya ba.

"Maraba da kanwata" dole nayi murmushin yake na gaishe ta, faran faran ta amsa. Nace "Halima Fa?"

"Ta shiga ciki" ta amsa. Sallama nayi wa Ya baba hade da godiya na dau sauran kayana. Bai wani mai da attention in shi kai na ba saboda daman ba wai danni yazo school in ba.

Banyi nisa ba, Anty Nainan ta biyo baya na. Amsan abun hannu na tayi tace "bara na taya ki ko, ya Hutu?"

"Alhmdlh" na amsa mata, muka cigaba da tfy tana ta min labarin hutun da akayin. "Kinji ni da yayanki" ta fada tana fadada murmushin ta.

"Hala yace yana sonki ne?" Siririn dariya tayi tace "kema kinsan ai dole ne, Adams akwai aljanun mata amma kinsan ce min yayi wai yaji hakan ne saboda kulan mishi da nake yi da kanwar shi, kiji wani zance fa" Ni nauyin zancen ma yasa ni dole sai da na dan dara. "Shi Yaya baba abin nashi khna har da karya ne?"

"Gashi nan ko kingani, kar ki wani damu ina jin duk abinda kike fuskanta zai iya zama tarihi kanwata." Murmushi nayi na nata godiya kawai. Dan ko na riga na cire ma raina akwai wani rana da wahalan da nake fuskanta a rayuwa zai samu aya

Da alamun huduban da Ajiddah ta ke min akan Amir ya shige ni sosai domin da numban shi a kaina na dawo makaranta. Ranar da yamma ana tashi prep ta jani wai in rakata staff room wurin Daddyn ta. Ba musu na bita saboda nima ina son yawan. Malam Aminu Geography shi ne sunan da ake kira shi. Irin malaman nan ne da duk da suna da budurwa. Ga dukkan alamun a set inmu Ajiddah ya hango, shine ya fakewa da School Daddy. Exam officer ne kuma shi kadai ne a office in shi.

"Ah maraba ku shigo mana" da murmushin shi ya amsa Sallaman Yana mana iso.

"Harda su Suhaima ne" kara fadada murmushin shi yayi. Ban ma san ya san sunana ba sai ranar. Gaishe nayi ya amsa sannan ya juya wurin Ajiddah "mutuniyar ya dai?"

"Waya nazo yi" ta amsa kai tsaye

"Wa za ki kira?"

"Yaya na" hade rai yayi yace "ni dai ban yarda da wannan yayan naki ba jiddah, ko dai abokin takara aka min?"

"Kai Daddy abokin takara kuma?" Dariya yayi ya Ciro wayan ya mika mata. Gabaya fita officer in yayi ya bar mu.

Kasa hakuri nayi na tmby ta "ke Anya Malam Aminu ba sonki yake ba?" Dariya tayi "share shi kinji, zai ma gaji ya kyaleni ne. Don wlh saurayi na ma zan kira yanzu" ina kallon ta tana wayan, na kan yi mamakin yanda Ajiddah ke iya hira da saurayi sosai, musamman da irin Malam Aminu. Ko da yake tana da yayyi mata da yawa, ba mamakin duk daga wurin su  ta ke samun courage in. Ire iren su Malam Aminu na nan da yawa a makarantu, musamman Wanda ya ke da yan mata zalla. Sai dai da principal ko vice inta zasu zan da abinda ke faru to fa tabbas da zasu dau babban matakai, amma da ke benefitting in daga malaman har daliban najin dadi ya sa Kowa ya rike bakin shi. Saukin ta da wuya kaji case in lalata, iya soyayyan kam za a sha ta.

Labarin Rayuwata Donde viven las historias. Descúbrelo ahora