Talatin da takwas

224 49 10
                                    

Abuja, Nigeria.


Gabadaya Al'amura sun cabe mata tun daga lokacin da taga sanarwa rasuwan Amal, tayi kuka ta yanda har take ganin ba ta da ragowan hawayen da ya rage bai fito ba. Sai dai har yanzu ta jasa gasgata zancen duk ko da yanda yake ta yawo a kafaffan yada labarai. Sai yanzun ta ke kara tabbatar ma kanta da gasken rayuwan ta bai da wani amfani kuma, a duk wani dakika daya da zai wuce tana raye sai ta tuna cewa wai yau Amal bata duniya kuma daga report in da ake ta bayar wa yasa ta gaza gasganta cewa bata da sa hannu a mutuwan Amal in. Abin bakin ciki abin takaici kuma Allah wadai, shine duk abinda ta tara ta aikata sannan kuma gashi ita har yanzun ba ta da wani riba. Dole ma ai taga bala'i da masifa, wannan ma ba a fara ba, sannan kuma ba ta jin ta cancanci neman yanci da Dr Fahad da kuwa Brr mustapha ke fafutakan yi a kanta. Shakka bbu ta cancanci hukunci mai tsanani da horo. Kai ba ma ta jin za ta iya yafe ma kanta in har ba a dauki mataki babba a kanta ba. Ta shiga rayuwan su, farat daya ta rusa musu duku wani farin ciki da suke ciki gashi ita ba ta da wani riba. Ina ma yau zata hada idanu da Faree da kuma Umaymah, to da ba abinda zai hana ta dau wuka ta lafga musu, ya tabbata cewa ta aikata kisan da ake zargin ta dashi, suma sa dandanin mutuwan da suka sa baiwar Allah tayi ba taji ba ba kuma ta gani ba. Shin ma wai ita wani irin rayuwa ne take living? Kulkum daga wannan sai wancan, tun tana karaman ta take ganin ibtila'i kala kala irin na rayuwa. Tun lokacin da mahaifiyar ta ta tafi ta yarda ita a wurin kishiya. "Astagfrillah Allah na tuba, Allah na tuba. In jarabawa ce kuma Allah ka bani ikon cinye shi" a fili ta fada cikin wata irin raunanniyan murya da kana ni kasan ba karamin tashin hankali ta ke ciki ba.


Yanda tayi maganan ne yasa har zeenah taji ta. Tunda tazo ba wani zama su ke suyi hira ba, duk dai tana kokarin deba mata kewa. Zeenah akwai surutu sai dai kuma ba ta cikin sakewan da har za ta iya zama tayi hira kafiya kalau. "Lfy kawa?" Ba ta tanka ta ba sai kife kai da tayi a jikin kujera, ita ba kuka take ba amma kuma abinda take fuskanta a yanzu yafi karfin tunanin duk wani mai tunani. "Kawa mana" zeenah ta kara fada tana dafa kafadan Suhaiman da still dai ba ta dago ba.


"Kina so mu koma asibiti ko?" Ita kam zata so ma zaman asibitin, ba kuma ta cikin hayyacin ta akan irin wannan azaban da take fuskan ta. Zuciyan ta zugi yake mata, ga kuma wani irin bugawa da yake yi kaman zai fito fili. Ko ba a gwada ta bama ta san tana fama da ciwuka dayawa wadanda take ganin ta cancanci samu. Sai dai ba ta jin za ta iya kuma yadda amma mata wani treatment bayan wadanda aka sha yi a baya, gwara ta sha jinyan ta, ta wahala kaman yanda ta wahalar da yae mutane, in yaso ita ma in abu yazo da ajali sai ta tafi kawai. Sai yanzu ta ke jin ina ma ba ta amincewa Barr mustaoha ya sa anyi bailing ta ba. Tabbas da zaman gidan kurkukun ya fi mata nan da ya kasance fayau ba wani abu farin ciki ko marmari a cikin shi. Duniyan ma gabadaya ji take kaman yana juyi ne, gabadaya ta rasa ina ma zata fuskanta. Ganin har jikin ta ya fara rawa yasa Zeenah ta dan kamo ta. "Relax mana haba, wanda ya mutu yana dawowa ne? Ina ce kece mai min wa'azi why are you acting like this" da kyar ta iya juyawa ta fuskanci zeenah, cikin rawan murya tace "na gaji da duniyan ne, na gaji da rayuwan komai bai dai mahimmanci ko amfani a gare ni. Wlh na gaji, ban jin zuciya ta tana da karfin kara daukan wani abu kuma. I was so weak at first amma irin abubuwan da na fuskanta ya sa zuciyata zama mai nauyi, amma yanzu am crushed"


Kwalla ne ke faman ziyaya a idanun zeenah. On normal circumstancea ya kamata ace suhaima tayi mamakin hakan sai dai ko dar illa ma ganin da take hawayen dadin kawar ta take yi, duk da ma ta san a sanadiyyan tausayin tane.


"Kiyi hakuri kawa don Allah, ki kara juriya komai zai karshe" Hakuri, juriya, karshe. Kalmaomin nan guda uku gabadaya ta tsani jin su a yanzu, ta dade tana jin su sosai sai dai har yanzun abinda ake fada mata bai zo ba, wai to shin sai yaushe ne hakan zai faru?

Labarin Rayuwata Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz