Talatin da biyar

234 47 3
                                    


Kaduna, Nigeria.

Dr Fahad zauna a falon gidan sa yana karin kumallo, sai dai attention in shi yafi tafiya kan TV akan abincin da ke gaban shi. Labarai ne ake yi, abinda ya dau hankalin shi kuwa shine. Budurwar da hoton ta ke manne kan screen in ana sanar da rasuwan ta a ranar da Asuba. Fara sol da ita, kyakyawa ce sosai irin wacce kyan ta ya kai a fada har ma a kara. Sai dai ba wai kyan nata ya dau hankalin shi ba. Aa, sunan da ke makale a kasan hoton nata ne ya ja ra'ayin shi sosai. Amal Idriss Hayatuddeen, The Hayatudeens only daughter. Tabbas ita dai ce Friend in Suhaima da su ka zauna tare na tsawon lokutta. Matashiya yar shekara ashirin da uku, wacce tayi kokarin kashe kanta ta hanyan yin alluran kwayoyi, sai dai hakkan ta bai cimma ruwa ba a wannan lokacin, sai dai hakan yayin sanadiyyan doguwan jinyan da tayi a asibitin John hopkins da ke garin baltimore a kasan Amurka. Labarai dayawa sun kawo shaidar samun saukin ta don har ana shirin sallame ta daga asibiti. Kwatsam kuma yau sai aka wayi gari babu ita, to daman dai rai aron shi aka bamu don haka sai dai muce Allah yaji kanta.

Dr Fahad bai santa amma sai da yaji wani irin bugawan gaba daya tsorata shi, tunanin daya fara zuwa mishi a rai shine yanda Suhaima za ta karbi wannan zancen. Tabbas, mutuwa ba ta dadi balle ma irin mutuwan da ta taba wanda ka shakuwa dashi, ba sai an gaya mishi wannan labarin zai girgiza ta ba. Bai kara maida hannun shi cikin abincin da ke gaban shi sai ma idanun shi da ya kara maida wa kan Telebijin in yana kallon abinda BBC hausa ke cigaba da nunowa. Attajiri Idriss Hayatuddeen ne tsaye, kusa dashi yaran shi maza biyu. Ba an fada cewa suna cikin tashin hankali ba saboda yanayin su kadai ya nuna hakan. Balle ma mahaifin da ya dauki son duniya ya daurawa yar tashi, gabadaya jikin shi rawa kawai yake yana ta faman girgiza kai yayin da likitocin asibitin ke kokarin fiddo gawan Amal in. Mahaifiyar ta kuwa labari yazo cewa ta fadi, yanzu haka likitoci ke kanta domin ganin sunyi nasaran ceto rayuwan ta. Hakan ya kara sa family i  shiga matsinaiciyar tashin hankali wanda kana gani kasan basu taba tsintar kansu a wannan masifan da ta afko musu ba. Kaman daga sama wani ya fado wurin da gawan ke kwance yana ta faman jijiga ta, ba ka iya jin abinda yake furtawa sai dai hawaye da ke ta faman tsiyaya daga idanuwan shi. Da farko Dr Fahad bai gane waye ba, sai bayan ya dago fuskan shi yana ma likitocin magana wanda da alama tsawo ya ke musu su maida ta, dan gashi yana nuna hanyan dakin da aka fiddo ta. Ba ko shakka, Zayd Al-mansur ne. Iya rudewa ya rude a wannan lokacin. Rufaida da ta shigo falon ta fahimci yanayin shi ke faman tmbyb shi "Lafiya" bai ma san tana yi ba saboda wani iri nauyi da yake ji a kanshi. Iya sanin shi Zayd bai da ishasshen lafiyan da har ma zai iya takawa. What is reallay happening? Jar dai framing in yarinya su ke don singa ba ta da wani gata. Rufaida da ta fara rudewan itama ganin yanayin mijin nata yace ma ta kawo mishi wayan shi, ita yasa tayi dialling in Barr Mustapha.

"Kaima kaga news in ko?" Tmbyn da Barr in ya fara mishi kenan.

"Nagani, what are you thoughts?"

Labarin Rayuwata Kde žijí příběhy. Začni objevovat