Hankalin Dr Fahad bai kwanta ba sai da ya amsa sakon Dr Usman, babban Neurologist a jahar Lagos. Haka ma a cikin asibitin ya tsaya kai da kafa domin ganin komai ya zama ready ta yanda likitan na iso wa za a hau aikin. Response patient in nashi kam har yanzu ba a magana.
Dashi a ka shiga Surgery in yayi assisting. Daki daki haka Dr Usman ke aikin shi a tsanake har ya cima burin abinda ke gaban shi. Wani ajiyan zuciya Dr Fahad ya saki lokacin da Dr Usman ya mishi alaman they are done. He hate losing his patient, a duk lokacin da abun ya zo da karar kwana ya kan tsinci kanshi cikin tashin hankali. Amma ya za ayi in lokaci yayi? Ba makawa tabbas sai an tafi. Kokarin kulle ta su ka fara. Engr da Mustapha ya ma bayanin yanda aikin ya kasance, Yanayin fuskokin su kadai ya isa tabbatar ma farin cikin da su ke ciki. Balle kuwa Maryam da ta ke ganin itace sillah, da Baban Haidar ya bata lbr har hawaye sai da tayi. Alhmdlh aiki yayi kyau sai kuma jiran farfadowan ta, nan fa duk su ka dukufa wurin addu'a.
Dr Fahad Jin Suhaima ya ke tamkar wata jinin shi shiyasa bai kyashi Mata komai although su Mustapha na Mata komai but shi in dai ya tsaya akan ta tare da taimakon Nabeela da Rufaida of course.
Some hours later
A hankali ta fara motsi da idanuwan ta tana kokarin bude su duk da matsanancin zafin da su ke mata haka ta daure tana ta kyaftawa har sai da ta yi nasarar bude idon kadan a haka tana bude tana kullewa har ta bude su gabadaya duk da hasken da ta ke jin ya ma idon yawa bai sa ta kulle ba. Wani irin ta ke Jin jikin ta kaman ba nata ba ga kanta ya mata wani irin nauyi da ba ma zata iya daga shi ba. Mata biyun da ta gani zaune a daki ta kafawa ido tana son tuno anya ta San su kuwa?
Dai dai lokacin Sister Rufaida da Nabeela zaune a dakin suna kallon wani Indian series mai suna Sehr Alasmar a tashar Bollywood da yake da yamma ne around 6:00 pm. Rufaida ce ta fara Jin alamun kaman ana kallon ta da sauri ta juya aiko four eyes su kayi da patient in ta zuba mata idanu ko kyaftawa ba tayi.
Tashi tayi ta nufi wurin ta tana Mata smiling "Sannu ko, are you alright?" Murmushin ta yi kokarin mai da mata ita ma a hankali can kason makoshin ta ta ke kokarin furta "ruwa ruwa" sai a sannan Nabeela ta juyo tana kallon su cike da mamaki. "Wow!! Yaushe ta farka? Let me call Doctor" da sauri ta fita dakin cike da zumudi. Rufaida ko matsawa tayi sosai domin ta ji abinda ta ke kokarin furtawa "Ruwa" ta ji tana furtawa a can kasan makoshi.
"Bara a samo miki" Rufaida ta amsa ba wai dan zata kawo ma ta in ba. Ta san cewa ba ruwa bane abinda ya kamata a fara ba ta bayan ta farka. Kokarin Mikewa patient in ta fara yi amma Kuma ta kasa sai ma wani azababben ciwon da taji bayan nayi.
Fahimtar hakan da Dr Fahad yayi ne ya sa yayi kokarin yi wa Rufaida magana "Faidah help her Mana" cije baki yayi cike da takaici, he can't believe he is the one messing things not her saurin basarwa yayi gudun ta fahimce takaicin da ya shiga "sa mata pillow ki daga ta she can't do it" ita Rufaida ba ta ma san ya shigo ba don haka obeying abinda ya ce tayi.
Hannun ta Kan shi nauyi ya ke Mata da kyar ta yi kokarin daga shi sai rawa ya ke ganin haka ya sa Rufaida kwantar mata da hannu duka biyu. Dayan ma kam ta kasa dagawa saboda karayan da ke hannun. Ita dai Nabeela tana baya tana Kallon su, a zuciyan ta tana ayyana yau za ta tmby Rufaida ina ta San Dr Fahad Banda Asibiti coz she can't take it anymore.
"Sannu Koh" Dr Fahad ke maganan Yana Kallon patient, daga kanta kawai tayi "me kike ji Yana Miki ciwo" ya bukata. Jikinta ta bi da kallo sai a Lokacin ta ankare da bandages in da ke kafan ta da Kuma hannun ta, hannun da ba bandage in ta daga da kyar ta shafa goshin ta nan ma ta Kara Jin wani bandage. Kan nata kaman ba nata ba haka ya mata, kara shafawa tayi ta tabbatar da da gasken dai ba komai akan. To ina gshin ta ya tafi? Life is full of wonders. Jikin ta nuna mishi gabadaya "sannu ko bara in baki pain reliever, Nabeela samo Mata Tea please, she needs to put something in her stomach" Fita Nabeela tayi ta hado tea in. Waya yayi aka kawo mishi maganin sannan ya Kira Mustapha ya sanar mishi farkawan patient in tasu.
YOU ARE READING
Labarin Rayuwata
General Fiction"Believe me ba wani abun birgewa a labarin Rayuwata shi yasa na gwammaci mutuwar akan Rayuwa irin wannan" idon ta a bushe karoro ta ke maganan ba alamun kuka ba wai don kukan ba Zama dole ba Aa, ta gaji da kukan ne saboda Bai da amfani a gareta do...