Arba'in

259 52 7
                                        

Rayuwata

Babi na sha uku

Ina wurin har aka idar da sallah, na fara jiyo hayaniya an fito kenan. "Keh lafiya me kike yi a nan wurin a jike?" Rufe idon da nayi ya sa banga mai maganan ba, a hankali na bude su na sauke jajayen idanun nawa a kanshi. Nan take rai na ya baci na ji zuciya na suyi. Duk da na dade ban ganshi ba zan taba iya manta shi ba. Haka kuma ba zan iya taba cin fuskan da ya min ina karamar yarinya. A yanda na ke a lokacin duk mai imani in ya ganni ba zai zageni ba, inma bai ji tausayi na ba baya ci min fuska ba. Duk da halin da nake ciki bai hana na galla mishi harara ba, ina jin tsanan shi na ratsa ni har cikin gangar jiki na. "Me kika zo siyo?" Banza nayi dashi, ko bai ga kallon da na ke aika mishi bane? Ni kam har zuciya wlh na tsani ganin muguwar fuskan shi. saleh mai shago ne ya karaso wurin mu "Wai Suhaima ce a nan cikin ruwan nan kika fito? Me kike so?" Da sauri na fada mishi, kasancewar yawan zuwa shagon shi da nake yasa munyi mugun sabo dashi. In har zanzo shagon shi ko ya rufe sai ya bude ya bani abinda aka aiko ni. Bude shagon yayi ya dauko min abinda na zo siyo, shiko Umar Sanda ganin naki tanka shi yasa ya kama gaban shi ya shiga shagon domin ya siyo abinda ya kawo shi shima. Sai da Saleh ya kulle shagon shi sannan ya kawo min abinda na siyan, nan ya ke fada min shima kulle shagon zai yi saboda wani Sabon hadarin ne ke faman haduwa. Amsa nayi na mai godiya na kama hanya cikin sauri. Hadarin sosai ne, ina shiga layin gidan mu ruwa ya fara saukowa. Layukan garinmu manya layuka ne sosai, gidan farko layin da karshe ba karamin nisa ke tsakanin su, mu kuma tsakiya don haka akwai tafiya sosai. Garin akwai wadatattun filin da layuka su ke da matukar girma ga fadi sosai. Akwai land kam har ba a magana gashi kuma ba mutane dayawa a garin sosai. Ganin ruwan zai fara karfi ya sa na fara gudu in samu in isa, sai dai ina tuni ruwan ya sauko da karfin shi. Ina neman mafaka naga wani mota a gabana na faman min horn. Bazan nayi da motan saboda ban taba ganin ta balle in San mai ita. "Suhaima! Suhaima! Kizo in sauke ki gida" naji ana fada bayan an sauke glass in motan, sai a lokacin nagane Umar Sanda ne a ciki. Ban sa lokacin da na ja tsaki ba, ganin hakan ma na fasa fakewan na sa gudu sosai, har faduwa nayi tayi a hanya ina tashi, da kyar na samu na karasa gida. Ina ganin yazo ya wuce ni na kara yin tsakin. Ina Sallama zan shiga gidan Adda falmata ta zo fita barander mu ka ci karo. Harara ta bini dashi tana tunkude ni "kefa baki da hankali Allah, a haka za ki shiga gidan ki bata mana ko, duk kina diga" tsabagen takaici ban san Sanda na ce mata "to ai ni ke gyarawa ko na bata" kallo na tayi da mamaki kwance a fuskan ta. Ina ga ba ta taba kawo zan iya maids mata magana ba, amma daman ance yau da gobe sai Allah. Hakanan naji har raina banyi na daman abinda na fada ba. "Ke don uwarki ni kike maidawa magana? To ki shiga in gani, shegiya mai bakin hali irin ta uwar ta. Ki shiga mana Wlh sai dai Uwarki ta haifi wata" ban kula ta ba na nemi wuri na zauna abu na, ina ajiyan zuciya don ba karamin wahala na sha ba. Zagin da ta min bai isa ba sai shiga gidan da tayi tana mitan na maida mata magana. Anty Yana ne ta fito tana cewa "ke dallah ni bani aikin da na miki in kingama dama ki kwana a nan. Kuma wlh in battery in nan ya jike sai kin nemo wani wato ke wuyan ki ya isa yanka ko? Kin fara maida wa yayar ki magana ina ga watarana kaina zaki dawo" mika mata nayi ta tafi tana banbami. Ba ta sake dawo ba sai sadiya da ta zo ta kulle kofan da karfi a gabana tayi shigewar ta ciki. Na kai mintu talatin a wurin zaune har na fara gyangyadi sai ga Al-lawan da hijab da zani. Bai ce min komai ba yayi saurin mika min ya wuce side in Ummiy a da Wanda ya zamo nasu a yanzu kaman yanda Umar Sanda ya taba kawo shawara. Daurawa nayi na shanya kayan jiki na sannan na shiga gidan. Adda falmata na waya hakan ya sa ko kallo ban samu ba, da sauri na shiga wanka. Na samu nayi salloli na sannan na bi lafiyan gado. Na san dole zazzabi sai ya kama ni.

Washegari Sai wurin la'asar na samu aka bar ni tafiya ajeyari dubo su Anty Amarya da kuma Inna, itan ma dai gsky ba yanda take. Zazzabi na nan amma da ke nayi kazar kazar sai bai kwantar dani ba. Ina isa na gaida Inna,  gidan duk sai ya min wani iri dake Govgo bata nan. Dan ma Ajiida na na sai na shiga gidan su muka zanta,  a nan Mai Aliyu yazo ya same ni.

Labarin Rayuwata Where stories live. Discover now