Bayan kwana biyu
Sukuku Dr Fahad ya shiga dakin Suhaiman domin ya duba ta. Kallo Daya ta mishi ta fahimci akwai abinda ke damun shi. Gaisuwa su kayi sai Kuma maganan da ba a rasa ba. Suhaima ba taji dadin hakan ba domin ko ance sabo turken Wawa, ka sa daure wa tayi da zai fita ta tmby shi.
"Dr me ke damun ka?"
Kaman jiran tmby ya ke ya samu wuri ya zaune bayan ya dafe Kan shi.
"Ansa min rana" yanda yayi maganan kadai zai tabbatar maka da yanda ya ke Jin zafin abinda ya furtan.
Ba ta San Lokacin da ta saki murmushi ba "Kai Dr wannan ai abin murna ne domin ne, she is a nice girl."
"Hmm ba daga nan ta ke ba Suhaima, In dan ita ne Rigimar mai sauki ce" girgiza kanshi yayi cike da takaici.
"Ummi na ba ta son auren" Da sauri ta juyo ta kalle shi cike da mamakin abinda ya fadan. Nodding kan shi ya kara yi domin tabbatar mata da abinda ya fada in.
"Any reason?"
"A long story"
Shiru ne ya mamaye dakin na yan sakanni, tunda taji ya fada haka sai tayi tunanin personal issue ne don haka na ta kara mishi maganan. "Kin sha magani kuwa?" Girgiza kai tayi, wani kallo ya mata alamun ba kya ji ko? Murmushin rashin gsky tayi shi ko ya nufi fridge in dakin.
Zaune ta ke ita kadai a dakin su na Nurses da ke cikin hospital in. Ita kadai ce a dakin sauran either suna gida ko Kuma sun fita wurin patient.
"Keh lafiya?" Nabeela ta fadi game da girgiza ta. Firgigit ta dawo cikin hayyacin ta tana Kallon ta.
"Kinsan dai ba kyau tagumi ko?" Nodding kanta tayi sannan ta cire tagumin.
"Rufaida lfy me ke damun ki?"
"Bakomai kaina ke ciwo" sannu Nabeela ta mata ba dan ta yadda ba sai dan ko ta so Jin ba lallai Rufaidan ta fada mata.
"Dr Najib fa ya iso kina nan"
"Subhanallah mu je ko?" Rufaida ta fada da mamakin lokacin da ta dauka tana faman tunane tunane.
A dai dai kofan da aka yi admitting Suhaima Rufaida ta tsaya "bara na dubo Suhaima"
Hararan ta Nabeela tayi "so kike muyi latti ko? Ki ja Mana magana"
Murmushi ta mata "haba dai ai Ina tare da Sister Nabeela ba fa so banda matsala" cike da tsokana Rufaidan ta fada haka, kusan duk ma'aikatan su ba wanda bai dago Dr Najib yana son Nabilan ba, itan ce dai ba ta bada fuska ba.
Tsaki Nabeela ta ja, a tare su ka shiga dakin. Turus su kayi ganin Dr Fahad a dakin, cike da tashin hankali kowaccen su ke bin hannun da Dr Fahad ke ba Suhaima yoghurt dashi da kallo. They were so much lost in their own world da ba su San da shigowan su ba ma, turo baki Suhaima tayi cike da shagwaba tana mitan ta koshi shi kuma sai insisting ya ke yi.
Nabeela ce tayi karfin halin gyaran murya. Sai ko a sannan su ka juyo "Dr da Kan ka ai da ka Kira nima sai na bata"
"No na hutashe ki" ya fadi yana Sosa Kai.
ESTÁS LEYENDO
Labarin Rayuwata
Ficción General"Believe me ba wani abun birgewa a labarin Rayuwata shi yasa na gwammaci mutuwar akan Rayuwa irin wannan" idon ta a bushe karoro ta ke maganan ba alamun kuka ba wai don kukan ba Zama dole ba Aa, ta gaji da kukan ne saboda Bai da amfani a gareta do...