Yau ma kotun a cike ta ke taf, dan har ya kusan ninka zaman da aka yi na farko. Bayan Alkalin ba ya buga a fara sauraron kara, Barr Mustapha ya tashi kaman yanda aka bukata. Da takardu guda biyu a hannun shi ya fito kai tsaye ya mika wa magatakarda.
"Ya mai mai girma mai shari'ah ina bukatan kotu ta bani daman gabatar ds wannan takarda a matsayin shaida na cewa wacce ake kara ba guduwa tayi kaman yanda lauyan gwamnati yayi ikirari" bayan alkali ya bashi dama ne ya cigaba da cewa "Ya mai girma mai shari'ah gobarar ta faru da ya ritsa da Zayd Almansur ya faru ne a ranar 31st watan july kaman yanda binciken mu ya nuna mana. Wannan takardan da ke hannu na kuma takarda shaidan rike Suhaima da aka yi a asibiti ne 1st August a sanadiyyan hadarin mota da ya gifta da ita a kaduna. A maganan da nayi da client ina, gigicewa ne ya sa ta barin asibitin da aka kai su bayan goboran nan har ta shigo motan Kaduna saboda rashin madafa bayan yan uwan Zayd sun tafi da nasu sun barta ita daya a wurin. Watan Kusan uku tana jinya a asibitin a sanadiyyan karaya da ta samu" nuna takarda yayi a matsayin shaidan record na asibiti "Ya mai girman mai shari'ah bayan ta warke ne ta zabi ta cigaba da zama a wurin wadanda su kayi jinyan ta a asibiti saboda rashin wani na ta a kusa, don haka malama Suhaima ba guduwa tayi ba illa ma nata jinyan tayi a asibiti." Amsan takardan Alkali yayi ya duba sannan ya jinjina kan shi alaman gamsuwa."
"Lauyan gwamnati kana da abince wa?" Girgiza kai yayi nan alkali ya sanar za a fara sauraron karan.
Lauyan gwamnati ne ya tashi sannan ya fara jawabi kaman haka "Ya mai girma mai shari'a in za a bani dama ina da gamsassun hujojin da zasu tabbatar da cewa wanda ake zarhi na da hannu dumu dumu a zargin da ake mata"
"Go ahead and present your witness" alkaline ya fadi hankalin shi na kan court in gabadaya.
"Da farko dai zan so in yi ma wacce ake zargi wasu yan tambayoyi" bayan kutun ta bashi dama ne ta koma sa Suhaiman fitowa gaban witness box, karasa wurin ta yayi yana kallon ta da murmushi dauke akan fuskan shi yace "Malama Suhaima right?" A hankali ta amsa shi. Yace "ko kinsan Zayd Al-mansur? Kuma waye a gare ki?"
"Saurayi nane" ta fada kai tsaye idon ta a kasan domin ba ta iya fuskantan mutanen da ke cikin court in ba.
Dariya prosecutor in yayi yace "Da kyau, Amal idriss Hayatudden fa?"
"Kawata ce" ta amsa a sanyaye, murmushin ya kara yi ganin yanda yarinyar ke bashi hadin kai cikin sauki.
"Da yawan mutanen da su ka san zayd su ka kuma san Amal sun san su a tare, ma'ana a matsayin saurayi da budurwan da su ka debi shekaru da dama suna tare, shin ko zaki iya fada ma kotu ya akayi kika dawo budurwan zayd in? Bayan kuma su in masoyan juna ne?"
Shiru kotun ya dauke, Suhaima kuwa idanun ta na kasa ta rasa ta inda za ta fara amsa wannan tmbyn. Kana ganin yanayin ta kuma kasan jikin ta yayi sanyi ta rasa bakin magana.
"Tou shknn tunda ba ki da amsan wannan amma za ki iya fada min mai ya faru ranar da gobara ta tashi a gidan zayd in" nan kaman tiryan tiryan ta bada labarin duk abinda ya faru.
"Nagode amma ko malama Suhaima za ta iya fada mana me ya zaunar da ita a gidan Al-mansur bayan kuma ba aure a tsakanin su kaman yanda addinin musulunci ya wajab ta"
Da sauri barrister mustapha ya tashi "objection my lord, lauyan gwamnati na kokarin sako addini a inda bai kamata"
"Sustain, Ka kiye lauyan gwamnati, this is not a shari'ah court" amsawa yayi cike da ladabi sannan ya juya gun Suhaima yace "ki cigaba da bamu labarin abinda ya faru a wannan rana har zuwa barin ki Abuja" labarin ta fada kaman yanda aka bukata.
VOCÊ ESTÁ LENDO
Labarin Rayuwata
Ficção Geral"Believe me ba wani abun birgewa a labarin Rayuwata shi yasa na gwammaci mutuwar akan Rayuwa irin wannan" idon ta a bushe karoro ta ke maganan ba alamun kuka ba wai don kukan ba Zama dole ba Aa, ta gaji da kukan ne saboda Bai da amfani a gareta do...