Talatin da bakwai

199 53 4
                                    

Rayuwata

Babi na goma

Ranar gabadaya wuni nayi a kitchen a sandiyyan da bakin da aka yi a gidan. Wandan da kwata kwata ma banda hadi dasu. Amma hakanann na jifgan musu aiki. Abinda na lura kuwa shine kaman duk yan'uwan Anty Yana irin halin ta ne dasu, sam sam ba wanda ke da kirki cikin su. Duk randa mu ka hada hanya banda zagi datsangwama su inma ba abinda ke shiga tsakanina dasu. Cikin wadanda su ka zo ranar kuwa har da wata yar uwar su Safina, mugun halin ta kuwa sak irin na Adda Falmata, shiyasa nake ga tasu yazo daya.

Bayan na gama kwasan aikin ne, a gajiye likis na nufi dakin da niyyan sannan in nemi gado dan banji zan iya wani abu a ranar. Abun mamaki, kaya na nagani na makaranta sun yi watsa watsa dashi a tsakiyan dakin. Still nayi ina kallon su, a raina kuwa na tsaya neman meya hada su da kayana. "Bakar munafuka karaso da uwar ki gantallaleyi yau dai Allah ya kama ki" Adda Falmata ce take maganan, daga irin kallon da take min nasan yau nai kwata na a wurin ta kuwa sai yabda Allah yayi kawai. Ban karasan ba duk da nasan irin abinda zai biyo baya, bugu ne na riga nasan bawanda bazan sha ba a ranar, don haka gwara inki matsawan ko bakomai a min wanda ke da dalili komin kankantan shi kuwa.

"Ba na fada miki na taba ganin su a Ajeyari da wannan abokin Al-lawan in da suke zuwa daga kaduna ba,  kika ce mai zai yi da ita?" Safinan ce wannan karon ta ke magana tana nuna ma Adda Falmata, pictures inda Amir ya bani ana washegari za su tafi. Wata kam sai a lokacin nasan in bala'i ya maka yawa ba wawanci da baka iya yi. Domin dai a lokacin daren da Amir zai tafi na tuno, yanda yazo ya same ni yana gaya min ba fa a daga tafyn su ba, gobe in sha Allahu za su tafi. Ban san sanda naji kwalla sun ciki min ido ba, akwai shakuwa na musamman kuma na daban da ke tsakanina da shi. Shi kanshi ya fuskanci halin da na shiga amma kuma sai ya dan fuske gudun ya sani kukan gabadaya.

Cikin siririn murya mai dauke da rauni nace "Sai yaushe kuma?"

"Wani Long vacation Suhaima, ai muna waya in sha Allahu ba wani matsala" juya kaina nayi a hankali wasu banzayen tunani su ka fara min yawa a kwakwalwa.

"Long vacation Amir, shekara daya fa kenan kuma kake kiran ba matsala? Abubuwa da dama za su iya faruwa a shekara daya, Haka kuma abubuwa da dama su kan iya canjawa ciki kuwa har da yanda muke ji akan junan mu. Za ka tafi bayan ka riga da ka saba wa zuciyata kusanci da kai, banjin xai iya rashin ka na wannan lokacin" shi din ma jikin shi ne yayi sanyi, juyiwa yayi ya fuskance ni da kyau

"Hakika Suhaima da ina da wani hanyan da zan iya ganin kafin cikan wannan lokacin wlh da nayi, za a iya ganina har yanzu karami amma Wlh ban dau lamarin ki da wasa. Ina sonki irin soyayyan da ban jin zan kara duban wata ya mace a duniya dashi ba fa wai zuciyata kadai ke sonki,  Aa da dukkan dyj wani abu da ke jiki na nake sonki My future wife, Dan Allah ke daina damuwan nan kinsan ban so ko?" A shagwabe na daga mishi kai, tun asali daman ni din shagwabibiya ce,  rashin Ummina ya sa ba wanda ya fuskanci hakan. Amma tun da na samu Ameer na ke sakin abu na kuma shi abun burge shi na yake, ya sha fadin yana kaunar mace mai shagwaba. Don ko Anty Nainerh, she is the weak one among us, shiyasa nan da nan za ta rafke.

"To mai zai hana ka zuwa amma?" Yanzun ma da shagwaban na mishi magana, sai da ya saki wani irin murmushi wanda kana gani kasan sautin muryana ba karamin ratsa shi yake ba. Kai ina son Amir, irin yanda ba zan iya fasaltawa ba. "Final year fa zan shiga, zan yi jamb, waec, Neco ga zaman extensions in da zamu yi kusan uku sannan kuma inyi facing graduation. Kar ki damu i want to focus ya da zan samu admission in University nan da nan inyi kudin da zan aure ki in fidda ki daga wannan kangin, i don't like your curre t situation Suhaima zan so ace ina da daman fidda ki, i want to fight for us no matter what" Wani irin dadin da na manta rabo na dashi naji yana ratsa ni "My heart can't never be free for anyone my future, i love you" Cike da kunya nayi maganan, wanda hakan ma yace yana burge shi. Kalaman kuwa duk a wurin ajiddah nake tsinta, ita ce malama ta a kowani fannin na rayuwa. Hannu na ya kamo duka biyu ya daura fuskan shi yana so in dago kaina sai dai na kasa hakan. A hankali shima yace "Na dade da gane we are made fir each other my love saboda tun ranar da na fara ganin ki, zuciya ta ke doka miki" ya fada yana taba saitin zuciyan nashi. Duk yanda na so daurewa ranar sai da nayi kwalla lokacin da zamu rabu. Life is crazy, so as love.

Labarin Rayuwata Where stories live. Discover now