Arba'in da Hudu

217 57 5
                                    

Rayuwata,

Babi na Sha bakwai.

Bayan bikin da kwana daya ya zo wurin Googo a cewan shi Mustapha suka you dashi zai maida ni maiduguri. Da ke Goggon ta San shi ba tayi wani musu ba illa ma godiya da ta hau mishi. Hakanan ba Shirin na dauki jaka na, na bishi duk da na so zuwa Ajeyari yiwa Anty Amarya bankwana don a watan zasu kaura Bauchi.

Ko a hanya ba wani magana mu kayi ba illa Nasihan da ya dinga min akan in natsu in maida dukkan hankalin a kan karatu shine kadai zai zame min gata a rayuwa. Godiya kawai na mishi, ya min fatan alkhairi. Ko da muka isa a tsaitsai ya gaida Goggo saboda ya sanar min daga maidugurin straight Abuja zai nufa. Washegari flight in su zuwa Egypt zai tashi. "Me zan fada ma Wanda ya bani sako a Baki?" Hakan da ya fada ne ya kara tabbatar min namiji ne mutumin.

"Allah ya saka da alkhairi" na fada kawai yayi murmushi yace "To zan isar, Sai munyi magana" daga haka ya ja motan shi ya wuce abun shi. Sai lokacin ma na tuna ban bude ledojin nan ba at all. Kayattatun Gift ne irin namu na mata, na Kuma ji dadin su sosai. Tun daman Abban ba mutum bane mai siya ma yaro duk abinda ya ke bukata balle kuma yanzu da nake wurin Goggo. Ni Kuma ban cika son ina tmbyn ta abu ba. Har ma da kudi, Wanda yawan su har Sai da suka girgiza ni Sai dai ko da muka yi magana na tmbyn shi ba'asi. Sai ce min yayi wai Wanda ya bani, na cancanci fiye da hakan ma a wurin shi.

Har na fara gajiya da zaman gida ba abinda nake yi tukunna Admission in Unimaid ya fito. Kuma na samu medicine in da nake nema dake duk wani abinda ake bukata na samu. Abbah shi ya min komai na makarantan, registration da sauran su. Ya ma so ya sama min hostel Goggo ta hana. Baffah kam mutum ne sam da bai da kara ko kadan. In ba rashin kara ba, har na gama secondary ba abinda ke hada ni dashi. Ko kudin break da kudin transport Sai dai in ya ba Goggo da ya zame mishi dole tukunna ta bani. Mutum ne Wanda bayan yayan shi ba wadanda ya damu da su. Su kam duk abinda su ka bukata Sai dai in basu furta ba. Dan ma ni ba irin mai sa abu a rai bane, komai nawa simple ne hakn ya kara sa suke ganin matsayina da nasu ba daya ba. To wadanda ma muke Uba daya basu soni ba balle kuma cousins.

Da muka yi magana da Yaya Sanda ta waya, ya nuna farin cikin shi sosai tare da kara min fatan alkhairi. Sai dai bayan nan Goggo ya Kira, ashe acc no ya bukata a wurin ta ban sani ba har tasa aka tura masa. Nan wasu kudaden ne aka turo har sun fi wancan. Goggo dai ya sanar mata kyautan shine gare ni. Ta ko ta godiya har da ce mishi wai ya dawo Egypt in nan hakanan kawai ayi auren in yaso na karasa karatu na wai a dakina. Ni dai ba mu taba zancen soyayya dashi ba, Amma duk lokacin da Goggo ta mishi irin maganan nan Sai ya bata wani positive reply. Amma ni da muka yi magana dashi cemin yayi wannan da ya aiko min sakon ne ya kara turo min kudaden. Na so takura shi ya fada min waye wannan hakanan, Sai dai fir yaki zancen  wannan karon ma.

Cikin ikon Allah na fara zuwa makaran ta. Sanadiyyan kara haduwa na da Faree'a kenan. Domin tun a ranar na farko na fito lectures karfe daya na nufin wurin alwala domin gabatar da sallan asuba. Na sunkuya ina cikin shafan Kai naji an riko baya na. "Suhaima" da sauri na juya muka hada ido da ita. Yanda naga ta sakan min fuska nasan ba muyi wannan sabon da ita ba. Na dai share mu ka gaisa faran faran. Daga wannan ranar kuwa har aka gama semester a masallaci muke hadu da ita. Tun muna dagawa juna hannu har muka zo muka fara hira sama sama. Har ina tmbyn ta Anty Nainah, tace min tana Abuja. Daganan dai ban bar zancen yayi nisa sosai ba.

Daga Masallaci next inda muka fara haduwa Kuma wurin cin abinci ne. Nan kam da kawaye kala kala na ke ganin ta. Da ke cafteria in hostel nake zuwa Kuma mata ne kadai a nan. Yawanci ni kadai nake zuwa saboda banyi kwashe kwashe wasu kawaye ba Sai dai course mate da muke magana daya biyu a Abuja. Watarana bayan na gama lectures naje wurin ni kadai. Sai ga ta nan ta shigo ita ma. Ban taba ganin ta ita kadai ba ma sai ranar. Tana ganina da fara'an ta ta karaso ta zauna inda nake bayan tayi ordern abincin ta.

Labarin Rayuwata Where stories live. Discover now