Karfe 10:00 na safiyar washegarin a cikin garin Abuja ta mana. Driver in gidan su Amal ya zo ya dauka mu daga airport. Kai tsaye wurin mum na fara zuwa. Bacin rai kwance kan fuskan ta tace "Suhaima kun dawo?" Na amsa mata mu ka gaisa. Tace "Suhaima ya akayi haka ne wai? Na ga pictures in Amal na ta yawa a media tare da Zayd" ajiyar zuciya na saki, daman tun juya na shirya abinda zan ce mata. "Mum ba fa wani abu bane, kawai bikin wata friend inta da su ka yi School tare ne, tare ma muka je. To shi daman Zayd abokin mijin tane. Kawai pics bikin ne ke ta trending. Na fadi hakane dan nasan pic in Amal da Zayd kawai za a turo mata, wanda da gangan ake hakan. Sai dai duk wannan bayanin da na kwasa da Amal ta shigo, kala mum ba ta mata maganan ba sai ma hiran yaushe gamo da suke tayi.
A ranar na shiga Drink shop, sai dai ban dade ba na fito saboda kiran da Anty Umaymah ta min zuwa blue cabana. Lunch mu kayi da ita, ina bata labarin abinda ke faruwa. " aikin na kyau Suhaima, irin su Zayd su cancanci fiye da haka, Amal ba ta dace dashi saboda gurbata mata rayuwa kawai zai yi. Kema ki kula da kanki please ban son a zo a sami matsala fa" murmushi nayi nace mata "karki wani damu Anty na, duk abinda ya kama inyi to wlh zanyi. Ni kam ko kin San wani abu akan matan shi Amina? Na ji yana fadan ta" tabe baki tayi tace "I don't know much gsky, akwai dai inda na santa. sai dai ita ma yar Yobe ce"
Zaro idanu nayi da mamaki nace "kenan Zayd yana da alaka da Yobe?"
"Mamarshi yar Fika ce, abinda na sani kawai kenan" jinjina kai nayi ina ganin karfin al'amarin, anya shirin mu zai kai labari kuwa?
"Zan iya jawo ta jiki ina ganin daga wurin ta ma akwai burin da zan cin mawa" da kai kawai na amsa ta, a zuciya na kuwa ina tunanin duk abinda za a cewa dauka fansa to tabbas sai an samu gargada a cikin shi. Sai dai nasan she is so determine akan abinda ta sa a gaba, ni kuma alwashi na dauka i will help her out. Sometimes ina jin kaman Dana sani yana min katutu, sai dai a tsari na ba magana biyu. In nace zanyi to tabbas zanyi.
Kamo hannu na Anty Umaymah tayi tana fadin "baby kin dai guje ni Ku?" Daga giran ta tayi tana jiran amsa. Ganin yanayin fuskana ya sa ta murmushi "kar ki wani damu, kinsan tsari na ba takura mutum if you don't want it ba batun dole. Ra'ayi ne kowa na shi ya ke bi" I like this side of her sosai, duk yanda kake kasan ta in ba ka son abu ba ta tilas ta maka.
"Don't you think ya kamata ki bar gidan su Amal hakanan?" Kallon mamaki na mata nace "Anty in na zan je in ba nan ba? In har muna so muyi achieving abinda ke gaban mu then i can't live with you, ai kin san hakan ko?" Da kai na amsa mata tace "am just thinking kar su gaji dake" siririn dariya nayi nace "Su fa basu da damuwa, ko harkan shi yake yi a gidan nan bayan haka kuma na samu karbuwan wurin mum inta sosai"
"Da kyau baby, sai batun karatu when are you ready to continue?"
"Ba yanzu ba tukun"
A ranar, a wurin mu ka kara haduwa da Faroukh. Dashi da wani da ban sani ba suka zo wurin, ban ankara da kusa damu su ka zauna sai da nazo tafiya nace ma Anty Umaymah "bar naje, Kinsan Zayd yau zai dawo ina da wani plan kuma a yau in nan" dai dai nan muka hada ido da Faroukh, sake ido da baki kai har ma hanci nayi ina kallon shi. Na gama amincewa zuciya ta bibiyata ya keyi, in ba haka miye wannan? Kallon banza ya min ya juyar da kai, nima na saki tsaki nace ma Aunty Umaymah "anty akwai matsala zan kira ki" ina fadin haka na ga ya juyo yana kallo na. Murmushin mugunta ya saki yana girgiza kai.
"Har wayau Abban Haydar ban yarda Faroukh ba bibiyan lamarina yake ba" Suhaiman ta fada. tana kallon barrister da faman sauraron ta kawai ya ke yi. Zuwa yanzu shi inma ya fara yarda da Faroukh gsky ya ke yi. Ya kasa hango labarin da ta ke bashi a kanta, ya Riga da ya tabbatar da kokonta da yayi na zaman ta a gidan karuwai, duk da ko ba ta fada mishi kai tsaye a labarin ta ba. Abu daya zuwa biyu ya ke son jin yanzu, shin tana da hannu a kokarin kisan Zayd Al-mansur? Da kuma dalilin da ya sa ta yin abinda ta yi. Shi kanshi ya san karfin halin sauraron labarin ta yake izuwa yanzu, da wani ya bashi labarin ba ita ba to da tabbas ba abinda zai hana shi karyata wa.
YOU ARE READING
Labarin Rayuwata
General Fiction"Believe me ba wani abun birgewa a labarin Rayuwata shi yasa na gwammaci mutuwar akan Rayuwa irin wannan" idon ta a bushe karoro ta ke maganan ba alamun kuka ba wai don kukan ba Zama dole ba Aa, ta gaji da kukan ne saboda Bai da amfani a gareta do...
