Rayuwata
Babi na Sha shidda.
Sauka na garin Damaturu, ji nayi kaman an sauke min garwashi a cikin zuciyana. Saboda wani irin azababbiyar tafasan da ya fara. Zafi na keji sosai yayin da fabadaya jiki na ya dau rawa. To avoid complication, na dau jiki sai Ajeyari duk can inma a yanzu ya zame min tamkar kabari ne duk da ko ban taba shiga a ciki ba. Har yau na kasa sanar ma Anty amarya dalilin da yasa ranar da muka gama jarrabawa a Nana Aisha na tafi maiduguri ba tare da na dawo gidan ba.
Tayi farin cikin ganina sosai. Baiwar Allah, duk girman gidan nan yanzu ita kadai ce a ciki. Sai yayi wani iri, duk ba dadi. Sai dai itan ma ta sanar min kwanan za su koma garin Bauchi. Anyu ma mijin ta transfer. Adama da ke ta faman jira na da taji cewa Ajeyari nayi, tayi ta bala'i tana hawa tana sauko karshe dai ta kule kaman yanda ta saba. Ban biye mata ba saboda nasan ina komawa gidan zamu shirya da ita.
Hakan ko ya faru, kwana na biyu a ajeyari na nufi sabon fegi. Duk da nasan ba gidan mu zanje amma kuma na kasa boye damuwan da ke mamaye a zuciya ta. Hakan nan dai na karasa, ko kallon hanyan gidan mu ban ba na wuce gidan su Adama. Na iske ma bata nan, mijin ya zo ya dauke ta sun tafi asibiti test wai. Goggo tayi farin ciki ganina sosai, ni ma kuma naji dadin ganin tan. Don duk mutumin da ya nuna min so, banji Ina da kaman shi kuma. Tarba na mutunci da karramawa aka min a gidan, ba laifi yan biki yan nesa har sun fara zuwa. Daman kuma nasan wasu daga cikin dangin nasu, musamman yan uwan Goggo da suke yan kollere. Duk da ba su da danganta ka, to amma zaman tare ya hada su da su Ummi na. Ballantana wasun ma da aure ya hada. Na dan yi mamakin farin cikin gani na dasu kayi. Ji kake ana "Ai yar gidan Aeeyn Aminaa ne" tuni na sake a cikin su, sai ma na hau taya su dan aike aiken da suke. A haka Adama ta dawo ta sameni. Ba ta ma san nazo gidan ba, sai gani na tayi kawai bakin famfo ina karasa wanke wurin da aka gama wanke wanke. Da farko harara ta bi ni dashi. Can kuma ko kasa basar da ni tayi, sai kuma tazo da gudu ta rungumeni tana dariya tana turo baki.
"To ai sai ki sake ta hakan nan ko, ko sai kin karya ta" Turo baki Adama ta sake yi jin yanda Goggo ta hau sababi. "Ke ko baki da kirki Allah" dariya na danyi, ganin sabon hararan da take min. "Yanzu dai ai nazo shknn" Hannu ta fara ja tana kokarin nufan kofan gidan. Da sauri na fincike hannun "Baiwar Allah lfy?"
"Dallah can zamu je ku gaisa da shi ne" Sarai na gane abinda ta ke nufi barin ma yanda ta sunkuyar da kai wai ita a dole kunya. "Waye shi?" Na fuske na fada, ai kuwa sai da na sha hara wannan karon ma har da Karin tsaki "Ke fa baki da mutunci ko?" Dariya nayi "Ai kya bari in dauko hijab ko? Ko haka kike so inje ba ko dankwalin arziki" itan ma sai lokacin ta fahimci hakan. Tilas ta sake ni na dauko Hijab sannan muka nufi wajen, Inda ya ke jiran ta a motan shi. Ai ko yana ganin ya fito, yana dan kara fara'an da already yake kwance a fuskan shi. Gaishe shi nayi, bai amsa ba yace "Maraba da babban kawar mu" Dan dukar da kai nayi, Ina mai cike da murmushi.
"Ya makaranta" ya bukata, a daddafe mu ka gaisa har yana tsokana na wai yayi fushi na bar mishi amaryar shi ita kadai. A gsky Adama tayi dacen miji, sai yanzu na fuskanci sanin da na mishi da muna yara ba wani na arziki bane. Ko da yake ma, tunda na gane Ya baba na cikin su, na tsani duk wata mu'amala dasu.
"Ya abokina kuma?" Da mamaki na dago kaina ina duban shi, don har ga Allah ban wani fuskanci inda zancen nashi ya nufa ba ma. Murmushi yayi fuskantan yanayin da na shiga "Ko baki San fada min? Ke fa yanzu kawar mu ce kuma muna fatan abin ma yafi haka soon, ko kuwa amaryata?" Dariya Adama tayi, hakan yasa na kalle ta cike da tuhuma. Sai dai na fuskanci itan ma kwata kwata ba wai tasan me yake nufi bane.
Karar wayar shi ce tasa na katse tunanin da nake "Mutanen Cairo, yanzu ko nake maganar ka ai" ban ji bai aka fada a wayan ba sai naji Mustaphan ya sake fadin "Dagaske gani ga mutuniyar ka ma ai" Tab! Sai lokacin kwakwalwata ta kawo min me yake nufi, Umar Sanda ne kenan? Tabbas shi dinne ma. Sai yanzu na tuna shi din ma abokin shi ne sosai ma kuwa. Kallon tuhuma Adama ta bini dashi, nayi saurin fahimtar da ita ban San komai a kai ba ma ta idanu. Ba dai ta gamsu ba amma.
YOU ARE READING
Labarin Rayuwata
General Fiction"Believe me ba wani abun birgewa a labarin Rayuwata shi yasa na gwammaci mutuwar akan Rayuwa irin wannan" idon ta a bushe karoro ta ke maganan ba alamun kuka ba wai don kukan ba Zama dole ba Aa, ta gaji da kukan ne saboda Bai da amfani a gareta do...
