Shiru tayi tana sauraron shi har ya kawo aya. Sai a sannan ta saki nannauyan ajiyan zuciya tace "zan baka gabadaya lbrn kaman yanda ka bukata. Sai dai ina bukatan wani alfarma in za ka iya min kafin in baka lbrn"
Bai ce komai ba sai dai kallon da ya ke mata ya nuna mata alaman ya yarda ta cigaba, shi dai barr har ranshi ya ke jin farin ciki samun nasaran da yayi a akan ta.
"Ina so Dan Allah in na fara baka lbrn nan kar ka katse ni, kar ka fuskance ni a bai bai haka kuma kar ka min wata tmby har sai kaji bayanin komai daga baki na." Kallon shi ta ke tana bayanin, ido gara rau, shi kam har yau yana mamakin rashin kukan da ba tayi ba duk da tsanin tashin hankalin da ya ke hango wa a idanuwan ta.
"Shknn ba matsala, sai dai kafin ki fara ina son sanin nawa zan amsa wurin zeenah" tabe baki tayi hade da girgiza kai.
"Ko nawa ake bukata za ta baka, kawai ka fada ma ta" kallon ta yayi yana mamakin yanda ta ke da tabbacin za a samu duk abinda ake bukata ko da kuwa yawan su. Kokarin furta hakan yayi.
"In ba za su isa ba fa? Akwai kudin da mu ka hada da Dr da baban su Faroukh ba sai mu hada ba? Sincerely speaking kudin nan na da yawa" ko da ya dago ya kasa karantar yanayin fuskan ta, banda yanda idanun ta su ka fada sosai, tayi wani fayau kaman ba ita ba, har rami kasan idanun ta su kayi, zai iya rantse wa bacci ya dade da kaura a idanun ta. Duk da ana ba ta abinci mai kyau, haka kuma wurin baccin ta ma ba laifi kuma ta tabbatar mishi har wa yau ba wanda yazo da niyyan ma ta tambayoyi.
"Abban haydar" ta fada tana kallon shi tace "kar ka damu, Dan Allah dai kar ku taba kudin ku, akwai more than enough a hannun zeenah, ko da an bar su ba za suyi wani amfani ba da yafi wannan in" iya gskyn ta ta ke maganan, shi kam gabadaya zuciyan shi ya tafi da mamakin shin wani irin kudi ne wannan? A ina kuma ta same su? Sai dai da alaman ta bar ma kanta sani. Katse mishi tunani tayi.
"Zan baka labarin sai dai zan fara daga abinda ya fara hada mu da zayd tunda a yanzu shine focus inmu" gyade ma ta kai yayi kawai ya gyara zaman shi yana mai kara fuskan tan ta. Kan ta a kasa ta fara bashi labarin kaman wacce ta ke karatun jarida ko wani littafi.
...
Uzuri, kalma mai mahimmanci da mutane kwata kwata ba sa wa Dan adam a zamanin nan. In ka ga mutum a cikin wani hali na kazanta a rayuwar nan in ba ka mishi fatan shiriya ba to ko tabbas kar ka zage shi. ba wanda ya san rubutaccen kaddarar shi da ta ke jiran shi a cikin littafin rayuwan shi. Kowa da irin yanda tashi za tazo mishi haka kuma da irin yanda zai kokarta wurin cin jarrabawar shi.
Da can a baya na kazanci masu hali irin nawa a yanzu, na yi Allah tur da wadai dasu. Duk a tunani na ba wani kaddarar rayuwar da za tazo in afka cikin rayuwa irin wannan sai dai ina nayi kuskure, jarabawar tawa dole tazo da hakan.
Lagos, Nigeria.
Yau ma kaman kullum zaune na ke a katafaren gidan rawan (club) in da ke birnin lagos a ikeja. Hankali kwance ba tare da nayi la'akari da daren da ya ja sosai ba. Kaman ba nice Watannin baya da su ka shude kafin yau in na ke dar dar da zaman wurin ba gabadaya na kasa sakewa. Kallo na kara bin gabadaya wadanda ke wurin da ke ta faman rawan su hankali kwance ba tare da an damu da cudanyan da ke tsakanin maza da mata ba kaman yanda ake yi a arewacin Nigeria. Amma nan al'adan su da dabi'un su ya sha banban domin daga musulman har arnan hade su ke hankali kwance suna shan rawan su mai hade da kida da ke matukar tashi, rawa ne na musamman da ya zama jiki anayi duk dare, mawakan su dayawa na halattar wurin. Kalolin giyan da ke wurin ko ba a magana balle kuma a kai da irin rawan shafa jikin da ke gudana tsakanin mace da namiji. In har budurwa ba ta zuwa irin wadannan wuraren to ganin mai duhun kai a ke mata shiyasa kowacce ke kokarin halarta wasu ma kawai don su faranta wa samarin su ne. A arewacin Nigeria ne za kaji wai don saurayi yaga budurwa a wurin rawa zai dauke ta yar iska ba zai iya auren ta ba ko da shi in ma yana zuwa. A can ko hankalin su kwance duk abinda zai gudana tsakanin su da mace ba zai hana su auren ta in dai suna son ta. Kawai dai sai dai ace auren ba Albarka sabida ba a gina shi akan turba mai kyau ba. Yau a irin yanda rayuwa ta juya min kenan. Na ruga na sawa raina ba abinda zanyi yanzu in canja hakan, kwalban da ke gaba na na dauka na cigaba da kwankwadan abinda ke ciki. Tunanin kowa a wurin giya ce na ke sha sai dai abinda ba su sani ba har wayau shine na kasa sabawa da shan shi duk barikanci na, ko dandanon sa tada min zuciya ya ke. Barni dai da duniyanci amma shan giya kwata kwata na kasa iya sa.
YOU ARE READING
Labarin Rayuwata
General Fiction"Believe me ba wani abun birgewa a labarin Rayuwata shi yasa na gwammaci mutuwar akan Rayuwa irin wannan" idon ta a bushe karoro ta ke maganan ba alamun kuka ba wai don kukan ba Zama dole ba Aa, ta gaji da kukan ne saboda Bai da amfani a gareta do...