Babi na takwas

364 90 2
                                    

Ana idar da Sallan Azahar Dr Fahad ya iso gidan, Sai da ta tabbatar da ta gama abincin da Barr ya sata ta hada musu da abin Sha sannan ta fita, ko da taje fadawa maryam, toh kawai ta amsa Mata ba tare da ko ta kalle ta ba. Jikin ta a sanyaye ta fita wurin Dr.


Gaisawa su kayi kawai ya ja motan su ka tafi. A wani katon super market taga sun tsaya "mu je ko ko ba Zaki tayani zabo kayan lefen bane?"

"Kai za ka hada?" She asked with a suprise expression plastered on her face.

"Mu je kedai kawai ya ce Mata ta ko bishi" siyayya su ka yi sosai na atamfofi, laces, bags, shoes, undies da cosmetics. Maimakon ta ga ya dau hanyar gida sai taga ya bi wani gun Kallon shi ta yi da mamaki yayi saurin ce Mata "shhhh" ai ko shirun ta yi.


Wani madaidai cin gida ta ga ya nufa Yana ta horn, Nan da Nan maigadi ya bude Mai Yana Mai sannu da zuwa. Shiru gidan kaman bakowa hakan yasa ta fara bin shi da Kallon tsoro. "Hey, i don't bite" ya fada Yana dariya. Ba Wai Dan tayi trusting in shi completely ba ta bishi Aa ta dai tsaya ta ga gudun ruwan shi. Sai dai taga yayi sallama taji muryar mace ta amsa sannan hankalin ta ya dan kwanta.


"Ah Fahad har ka iso?" Wata Mata da ba zata wuce 35 ba ta fito tana maganan hade da wata yarinya a bayan ta. Gaishe ta Suhaima ta yi ta amsa faran faran haka ma Dr in.


"Anty ga Suhaima Nan na kawo ta gaishe ki Kinga ita ma ta Taya ni muka karasa siyayyan" murmushi tayi cike da kunya don ko wani iri ta ke ji in Fahad in ya Kira ta da Anty don ta San da kadan ta fishi.


Suhaima dai Kallon da ake ta bin ta dashi ya sa ta tsargu, four eyes su kayi da Zahra Nan da Nan ko kirjin ta ya bada kulululu "Sannu fa kin Sha jiki" Wacce su ka Kira da Antyn ta fadi sai a sannan Zahra ta Mata sannu sai dai da alamun ita ba ta gane ta ba kaman yanda Zahraun ta gane. "Ga sis ita Zahra da nake baki lbr" Dr Fahad ya fada ita ko Suhaima murmushin karfin hali kawai ta sakan Mata cike da mamakin yanda zahran ba ta gane ta ba Amma sai ta barwa zuciyan ta. Sun Dan taba hira sama sama kafin a Kira Zahra a waya tayi saurin dauka tana fadin "F sai yanzu za ka kirani? Nayi fushi" Nan ta ke Suhaima ta gane da Faroukh ta ke waya don ko haka ta ke Kiran shi. Ihun da ta sa ne ya dawo da Suhaima daga tunanin da ta tafi "are you in your senses Zahra?"

"Sorry ya fad, F ne fa yace min In 5 days zai yi Landing a Lagos, nayi missing in shi"

Tsaki Fahad ya ja "I wonder if this guy is even going to marry you kin tsaya kina hauka akan shi" turo baki tayi kaman za tayi kuka "Anty Kinga brother ko"

"Kyaleta Fahad Ikon Allah ne"

"Aa Anty in Sha Allah ma ni shi Zan aura" murmushi su kayi gabadayan su.


Sai bayan la'asar bayan Fahad ya dawo daga masallaci su ka bar gidan, haddadun bokhoor Anty ta bada, zahra Kuma ta Bata bracelet taso ta ki amsa but she insisted, Dr Fahad ko da ya sauke ta a gida wasu haddadun Arabian gowns ya Bata guda biyu da jewelries a cewan shi tukuicin Siyayyan da ta Taya shi ne, ba ta Musa ba ta amsa don ko ta ki ma fada za suyi daga karshe ya sata dole.


Ko da ta shiga gidan as usual Matan gidan ba ta Nan sai Hadiza da haydar, Yaron har murmushi ya dinga yi ya ganta ita ma ko da sauri ta dauki shi sannan ta bashi tsaraban Bobo in da ta siyo Mai, Nan da Nan ya hau Sha, Yaron har tausayi ya ke bata har ya sa da wuni da yunwa tun Yana karamin shi Yana Shan abubuwan da Nanon Mahaifiyar shi ba da gabadaya ba ta da time in Shi, daga yau tana islamiyya sai gobe kasuwa gata gidan kawa kullum dai da inda ta hara, don da har weekend ta ke hadawa ta tafi gidan Anty sai da Antyn ta hada su da Mustaphan ta musu ta tas tukunna su ka shiga hankalin su. Shi dai ba wai Yana so bane Amma ya tsani abinda zai Bata Mata Rai Yana mugun gudun fushin ta.

Labarin Rayuwata Where stories live. Discover now