Burj khalifa, Dubai.
United Arab Emirates.
Wani irin murmushi ne ya sauka kan fuskan shi dai dai lokacin da hannayen shi ke typing Mission accomplished a Email address in ogan shi. Wani iri annashuwa da farin ciki hade da kwanciyar hankali ya ke jin yana mamaye duk ilahirin shi. Ba yau ne na farko da ya fara samun saa akan case in da ya ke dauka ba. Wannan in dai ya kasance daban ne, saboda mahimmanci da ke tattare dashi. Bai ko shakkan komai ya zo karshe. Nan da nan yayi dialling wani numba, visa ya sa a mishi processing. He can't wait to be finally back in Nigeria. Har ya kwanta, tuno tan da yayi ta sa shi saurin mikewa yana mai lalubo wayan shi. Nan da nan yayi dialling numban ta, kaman Wacce ke jira yana shiga ta dau wayan. Saukan sautin sallaman shi a kunnen ta kadai taji ta gane shi ke magana.
"Faroukh" tayi sauri fada. Sai da yayi murmushin da ya tsaya iya bakin lebba. Sautin muryan ta kadai ya tabbatar mishi she have been longing for the call. Dama ya San dole hakan zai faru, Sai dai Kuma wannan na daya daga cikin punishment inta ne.
"Zan sa a miki processing Visa zuwa jibi you are good to go In Sha Allah, Sai ki zauna cikin shiri" Godiya ta fara yi, Sai dai duk yanda ta so ya tsaya su gaisa da kyau hakan bai faru ba. Duk da haka taji dadin call in nashi, a da tayi tunanin ba zai cika alkawarin ba ya manta da ita. But now it good to feel like Nigeria is safe for her. How she miss her job, Kai Allah ya kiyaye ta a abinda zai sa ta kara shiga dana sani. The good thing, kyautan da ta samu daga wurin su Rawan da ku sunan da bikin ya jawo mata. Ba taji akwai wani Event planner da ke tashe a kasan yanzu kaman ta. One good thing about her, ba ta Nigeria amma hakan bai sa ta samu gargada akan sana'an taba. Saboda hakan ya sa take making sure she work with professional. Mutanen da ke da principle, in kaga harka yayi kasa to tabbas kaddara ce kawai irin ta Ubangiji.
...
Kotu ta cika makil wannan karon fiye da tunani ma. Abun mamaki hadda fuakokin da ba ayi tsammani. Domin dai Hajiya Binta ce zaune a gefe daya, wato uwar gidan Al-mansur, Wacce ake kyautata zaton ita ce ta shigar da karar. Sai cika take tana batsewa, fuskan nan a tamke ko alamun fara'a ba za ka hango. Gefen ta kuwa, Amina ko ince Nainarh ce a zaune. Kana ganin yanayin fuskan ta zaka san ranta a bace yake. Da dukkan alamu ba da son ranta ta halarci wannan wurin ba. Can gefe guda kuma, Umaymah Ameen da mukaraben ta. Kowa dai jira yake yaga ta yanda shari'an zai kasance.
Bayan Alkali ya samu shigowa ne, a ka karanto karar da za a gabatar a wurin kafin Kuma a gurfanar da Wacce ake kara wato Suhaima Adam Bello a gaban kotu.
Suhaima dai kaman yanda kowa ya sani, she plead not guilty akan abinda ake zargin ta dashi. Saboda haka Alkalin ya bama lauyoyin daman su fara gabatar da shari'an.
Barr mustapha ne ya fara magana cikin natsuwa da addu'an neman nasara a bakin shi ya Mike kan kafafun shi. Bayan ya gaida Alkali, ya kara neman a bashi daman tabbatar wa kotu ba Wacce ake zargi bane ta aikata laifin da ake zargin ta dashi.
Kai tsaye Faroukh ya fara Kira, abun mamaki Sai da ya Kira Faroukh inne idanun shi ya fada kan Engr Usman, mijin Antyn shi Kuma yayar matar shi. Bai San yazo ko alama bai sanar mishi da zai shigo Abujan ba ma. Kusa dashi Faroukh in ya miko rashin a hade har ya karaso wurin da ake bukatan ya tsaya.
Cike da kwarewa, Barr mustapha ya kalle shi "Sannu Faroukh, wata yar guntuwan tmby ce nake da bukatan yi maka." Bai amsa kawun nashi ya cigaba dacewa "Zan so ka sanarwa kotu ina kuka je kai da ranar da staffs in company inku su kayi meeting a guest house in Al-mansur"
Kai tsaye ya bashi amsan inda suka je in da Kuma dalilin da ya Kai su.
"Wa ya fara barin wurin a tsakanin ku?"
"Shine, saboda Kiran shi da aka yi a waya. Sai dai yana fita nima na fita" Sosai Barr ke samun karfin guiwan amsoshin da yake samu gun Dan Yayar tashi. Ba shakka they are going somewhere.
YOU ARE READING
Labarin Rayuwata
General Fiction"Believe me ba wani abun birgewa a labarin Rayuwata shi yasa na gwammaci mutuwar akan Rayuwa irin wannan" idon ta a bushe karoro ta ke maganan ba alamun kuka ba wai don kukan ba Zama dole ba Aa, ta gaji da kukan ne saboda Bai da amfani a gareta do...
