Rayuwata
Babi na sha hudu
A daddafe na daure na ke rubata jarrabawan da duk rubutawa kawai nake. A ranar papern mun na karshe ne muka hadu da mai Aliyu. Don har cikin school yazo ya same ni, yan makaranta na ta gulman su mu kayi kaman bamu ji su bama muka fita abin mu. Yanda muje yi duk ranar da yazo ya same ni a makaranta, direct wucewa muke ya taka min har zuwa kofan gidan Goggo. Yau in ma hakan ne ya kasance, mostly ma labarin School insu ya ke bani dake ya kwana biyu da fara karatu a garin bauchi.
"Bai in dan amso abu a wurin abokina pls" Ban kawo komai a raina ba na ce mishi "muje mana" Haka mu ka cigaba da tfy, yana ara jana da hira ina dan amsa mishi sama sama dake matsalolin da ke gabana sun fara fin karfin kaina.
A haka har mu ka karasa kofan wani gida mai dan girma. Wayan shi ya ciro ya kira abokin nashi ni dai ina tsaye a gefe ina jiran ya amshi abinda zai amsan mu wuce dake ma duk hanya ne sai dai kuma ba hanyan da muka saba bi ba. "Suhaima mu shiga please, yana so wai ku gaisa da matan shi" bude baki nayi idanuwa na kyar akan shi. "Matar shi? Kana da abokin da yayi aure ne daman?" Dariya ya min yace "lallai ma suhaima wlh kin raina ni. Kuma ma fa mu maza ba wai irin ku bane, saboda mu muna abokantaka har da wadanda suka girme mu, ba kaman ku da kuke ganin shi a matsayin ci baya ba." Ban ce mishi komai sabida nasan gsky ya ke fada. "To Amma ya akayi ya sanni da har zai hada ni da matar shi ku gaisa" murmushi yayi yace "Suhaima kenan an gaya miki akwai wanda yake tare dani da bai san ki bane?" Ina shirin magana sai ga abokin nashi ya leko. "Mai ku shigo mana ku tsaya nan, ko madam in taka ba ta son shigowa ne?" Saurin sadda kaina kasa nayi, ina mamakin sunan daya kira ni dashi. Nasan maganar soyayya bata taba shiga tsakanina da shi balle har ma a kirani da madam in shi. Fara'an abokin nashi yasa na basar kawai muka gaisa. "Please shigo ku gaisa da madam sai ku tafi mana" wani nauyin shi naji a lokacin, hakan yasa ban iya musu ba na bi bayan su muka shiga har cikin gida.
Sai bayan mun shiga naga girman gidan sosai. Ashe ta waje nema bai nuna wani girma ba.ga kuma space sosai kafin a kara sa cikin main house in. Haka dai na ta bin su har zuwa falon gidan. Iya haduwa wurin nan nayi don har na fara tunanin baban yarinyar wani attajirin mai kudi ne a cikin Damaturu, in ba haka ba irin wannan kaya kan sai dan wane da wane. Muna zaune kusan mintu uku ya shude, sai ga abokin da tray dauke da drinks da cups. "Sorry Suhaima, ta fito wanka ne tana sa kaya bara tazo" ban ce komai ba, banda murmushin da nayi. Motsin da nake ta faman ji ya sa na aminta akwai mutum a cikin. Duk yanda abokin ya matsa ku sha ruwa, kokallon teray in banyi ba. Ina dai zaune a haka dan har na far kosawa. Abokin ya kara fito, wannan karon kala bai ce min ba yayi hanyan kofan waje. "Ni kam mu tfy kawai" na cewa mai Aliyu sai dai banda murmushi ba abinda yayi min. Ina shirin kara magana naji bude kofa, ban juya ba don nasan abokin ne. Sai dai jin karan mutum a kusa dani, ya sani daga kai. Dum! Naji gaba na ya fada a sanadiyan wanda na gani tsaye gabana, Yaya Baba. Har ga Allah ba abinda ya fara zuwa min a kai sai shi inma kila gidan abokin shi ne. Nan take na murtuke fuska saboda na tsanin ganin shi. Dariya yayi ganin reaction ina "an gaya miki zaki taba guje min ne? Lallai baki sanni ba yarinya" ko kafin hankali na ya gama fahimtan abinda ya ke nufi sai jin wani irin nauyi nayi a kaina. Ban san lokacin da na saki wani irin razanannen kara ba saboda bugun wani abu ds ban iya tantance menene ba ya sauka a kaina. Idanu nane su ka fara kokarin lumshewa, yayin da nake iya jiyo sautin muryan maza dayawa a take a kaina sai babbakewa da dariya suke "Yarinya yau kin shigo hannu, irin wannan nama haka?" Ban san wa yayi maganan ba saboda yanda nayi nisa da fara fita daga cikin hayyacina. Da kyar na iya saita idanuna kan Mai Aliyu da naga wanda ya shigo damu gidan yana mika mishi wasu irin makudsn kudi. "Jeka kuma kar in sake inji wani zance kan wannan abun" da kai ya amsa ya mike, sai da yazo fita mu kayi ido huddu dashi. Wani irin kallo naga yana jifa na dashi, ba zan ce kallon menene ba amma dai nasan bana mugubta bane. He looks so helpless a haka ya fita ya barni a wannan wurin daban san me ke shirin faruwa dani ba. Ga wani irin azaban zugi da kaina har ma gabadaya jiki na ya dauka. Kwakwaran motsi na kasa, haka sautin murya na ba abinda ke iya fitowa. Ban kuma fahimtan duk wani abinda suke fada gabadayan su. Kasa fada nayi dasu lokacin da daya ke kokarin yaga kayan jikina, tun ina bige shi da kafana, yana zuba min wata azababbiyar mari na rafke a wurin gashi dama can kaina bai iya motsi. Amma haka na ciga da kokarin hana shi da hannuna, yana jan kaya ina ja. Hauri na yayi a karahe da kafa, a kuma kan cikina dole yasa na kasa komai har ya cin ma burin sa.
ESTÁS LEYENDO
Labarin Rayuwata
Ficción General"Believe me ba wani abun birgewa a labarin Rayuwata shi yasa na gwammaci mutuwar akan Rayuwa irin wannan" idon ta a bushe karoro ta ke maganan ba alamun kuka ba wai don kukan ba Zama dole ba Aa, ta gaji da kukan ne saboda Bai da amfani a gareta do...