Sha hudu

288 56 0
                                        

Zaune ta ke hakimce a kujeran office inta, a hankali ta ke faman juyawa. Ta kura wa news post in da ke gaban wayan ta ido. Wani daci taji ya ziyar ci zuciyan ta, ran ta na wani irin tafasa. "Oh Allah wannan wani irin masifa ne na jefa baiwar nan naka a ciki?" A fili tayi maganan, tana kara jin zuciyan ta na suya. "Allah ya kawo miki mafita, kwarai zan so in cece ki, sai dai hakan nima barazana ce ga rayuwa ta. Asiri na zai tonu, mutane za su daina ganin mutunci na. Duk wani kima da daraja da ake bani zai gushe" ita kadai ta ke magana a cikin rantsatsen office in ta da ya sha haduwa da interiors iya interiors. It looks so serene with simplistic beauty. Yanzu haka dai, tana bukatar wurin da za taje tayi cooling mind inta,  inda za ta samu natsuwa da kwanciyar hankali, tana matukar bukatan hakan. Ita haka zuciyan ta ya ke, in dai taji tana son yin abu to cikin gaggawa ta ke aikata shi. Don haka yanzu ma dole ta biya wa zuciyan na ta bukatar ta.

Saurin daukan waya tayi ta dannawa PA inta kira, ba jima wa ya dauka "i need a morning ticket to Seychelles tomorrow" dan jim PA in yayi cike da mamaki, kwata kwata bai jin tana da shirin yin tafiya kwana kusa. Amma kwatsam! Ta kira shi.

"Such a sudden trip" ya fada, yana tsimayin ta mishi bayanin tafiyan na ta. Instead, ce mishi tayi "please do as i said" tayi saurin katse wayan. Ba ta cika son binciken ba, barin ma a wannan tafiyan, da ta ke jin dole ma ne ta bar kasan har sai case in nan ya sarara koma an gama shi gabadaya. She can't do anything for Suhaima now, tunda ta san akwai kason sa hannun ta a abinda ke faruwa da ita. Tana dai fatan wani ya taimaka ma ta. She can't say exactly ga abinda ya faru, dan ba ta sani ba ma. Tuni ta dauki jakan ta, bayan shi ba ta kara daukan komai ba. Landline ta dauka ta danna wa secretary inta kira. "Yes madam" mercy ta fada bayan ta karaso cikin office in.

"Am going for a sudden short trip, make sure, you tied of this place" tana gama magana ta sabi jakan ta tayi waje, ba tare da ta amssa sallaman da mercy in ke mata ba. Mercyn ba ta wani damu ba, domin ta san yan mulkin inta tashi haka ta ke musu, sai dai ba ta jin za ta iya daina aiki da madam in na ta, domin akwai arzikin kyauta kam.

A gaggauce ta isa gida, dan abubuwan da za ta bukata ta hada. Ba wani yawa gare su ba, saboda ita al'adan tane in za tayi tafiya ba ta diban kaya da ya wuce 2 sets, duk abinda ta ke bukata in ta je wurin za ta yi shopping insu. Magungunan ta dai ta hada wuri daya.

Banda secretary in ta da PA, ba wanda ta sanar wa za tayi tafiya. Zama tayi duk wani abinda ta ke bukata ayi in bata nan tayi drafting sannan ta tura wa PA ta Email. A lokacin ta yi booking in hotel in da za ta sauka,  a Seychelles in. Bayan nan ne PA in ya sanar mata, an samu flight in amma 6:30 am kuma a airport in lagos. Sannan ba one-way sai round trip. "Its okay, get me a last minute ticket to lagos then"

Karfe hudu na safe driver in ta ya dauke ta zuwa Airport. Har isan ta airport in, fatan ta daya,  Allah ya sa ta bar kasan lfy ba tare da wani obstacle ba. Ba su wani dade ba, su ka daga zuwa Lagos.

A wurin kujerun da aka tanada ta zauna a airport in tana jiran a fara boarding. Don rage time ne ta fiddo magazine in interior decorations tana duba wa, coz akwai aikin da za tayi online very soon a seychelles. Time to time mutane na zuwa su gaisa da ita, wasu har requiring yin photo su ke da ita, perks of being a celebrity, she is an an influencer and blogger online. Cigaba da duba magazine in tayi coz she have to make sure everything is going smoothly.

“What a perfect decoration" ta ji an fada daga bayan ta. Kaman kar ta juya sai kuma kawai taji tana son juyawa taga wanene wannan?

Sanye ya ke da glasses karami da ya matukar amsan shi, frame in gabadaya transparent ne don haka ya hade da lens in ya bada kala daya. Kananan kaya ke jikin, shirt in navy ne ta saman aka yi manya layi ash and red in da aka sa tambarin kamfani. Fari ne sai dai bai yi irin mugun hasken nan ba, kana dai kallon shi kasan harda hutu ya kara mishi hasken da ke gabadaya jikin shi. "Handsome" ta fada a ranta, Kallon ta ya ke da kyakyawan murshi akan fuskan shi "it awesome" ya kara fadi yana mai fadada murmushin shi.

Labarin Rayuwata Où les histoires vivent. Découvrez maintenant