A hankali Suhaima ke samu sauki, da ke akwai orthopaedic doctor in da ke zuww asibitin yana duba ta. Abin yana zuwa da sauki sosai don har an fara koya mata taka kafan. Qur'ani kuwa tun ranar da su ka fara da Dr Fahad bai yarda an tsaya ba, har ma sunyi nisa. Ganin tana saurin dauka ya sa ya ke dan hada Mata da wasu littatafai gabadaya. Suhaima ko jinta ta ke wani fayau kaman ba ita ba saboda azkar in da ta sa gaba d istigfari. Hakanan kawai ta ke jin ta cikin annashuwa, kaman rayuwar ta ya canja gabadaya, sai yanzun ta gane ba abinda ya kai ka koma wa Allah dadi.
A gidan su Rufaida ko tuni su ka fara shiryen shiryen bikin da ya rage sauran wata uku sai dai ba tare da sa hannun ango ko Amaryan ba. Wani zuwan mahaifin Fahad da su ke Kira Abbah Kaduna ne ya ga irin ramar da Rufaida tayi gabadaya ta yi baki ta rame. Ganin hakan ya sa ya Kira ta gefe don Jin ko aiko abinda ke damun ta game da auren amma ta tabbatar mishi bbu, Fahad inma sai da ya tuhume shi ko akwai abinda ya ke mata shi ma dai babun ne. Mahaifin ta Baffah ya samu akan ko su hakura da auren tunda yaran kaman ba su so. Aiko ya ga bacin rai gun Baffah, kaca kaca ya mishi da ke daman shine Yaya, ya tabbatar mishi da ba abinda zai sa a fasa wannan auren. Don Haka Dr Fahad da Sister Rufaida sai hakuri.
"Oh yau dai ya kamata muje mu duba Suhaima gsky" Anty Ke maganan tana typing a system inta, Zaune su ke gabadaya a parlor suna kallo Amma as a workaholic ba ta iya Zama hakanan. Lecturer a Kaduna polytechnic da ke tudun wada, tana koyarwa da Course in SLT wato Science and laboratory technology. Mace mai ilimi sosai da ta San mahimmanci karatun boko Kuma ta daraja shi. Haka yaranta gabadaya ta daura su akai domin ko gabadayan su ba dakiki, da kanta ta ke sparing time ma ta musu lesson. sai dai Kuma Kash! Bata ba Ya'ya'n ta karatun addini kaman yanda ta basu na bokon ba. Ba Wai ba suyi bane gabadaya, Aa suna zuwa islamiyya kullum sai dai ko kadan ba ta damu da ta tmby su abinda aka koya musu koma ta koyar dasu kaman yanda ta ke wa na bokon.
Da murna Anisa ta tashi "Yauwa daman 2 days nayi missing inta so Zan biki"
"Nima zanje" Muhibba ta fada hankalin ta na Kan littafin da take dubawa. Kusan ita ce ta dauka gabadaya halin Antyn a gidan, kullum ka ganta da littafi gaban ta.
Nan fa Kulsoom da twins su ke ihun su ma zasu je har sai da Faroukh ya daka musu tsawa sannan su ka natsu.
Siririn tsaki ya ja "Za ku Wani cika ma mutane kunne"
"Ehm ehm Faroukh ban son zalunci fa"
"Allah Mummy sai ana musu haka ne. Ni wai Mummy wai wannan yarinyar ba zaku nemi iyayen ta bane ko Kuma Zaku huta haba!"
"Amma ai kana ganin kokarin da babanka da Uncle Musty ke yi ko"
"Mummy mutanen tunda fa kuka ji haka ba zasu fito ba, may be bata dasu ne"
"Ni dai yanzu tashi ka shirya da Kai zamu fita" tashin yayi ya nufi hanyan dakin shi yana gunguni "Duk Mimin nan ta jawa mutane"
"Haka kace a kunnen Uncle Musty" Da sauri ya juyo ya daga hannayen shi alaman surrender "Wai mommy ki rufa min asiri kisa aji mu da Uncle"
ESTÁS LEYENDO
Labarin Rayuwata
Ficción General"Believe me ba wani abun birgewa a labarin Rayuwata shi yasa na gwammaci mutuwar akan Rayuwa irin wannan" idon ta a bushe karoro ta ke maganan ba alamun kuka ba wai don kukan ba Zama dole ba Aa, ta gaji da kukan ne saboda Bai da amfani a gareta do...