Sha biyu

304 58 2
                                    

Dukkan wani bayani da ya kamata ace sun samu sun same shi. Abujan su ka tafi da kansu. Sai dai har yanzu ba su gano asalin abinda ya faru tsakanin Suhaima da Almansur ba. Suna dai fatan ji daga bakin Suhaima, daganan a san yanda za a bullo wa zancen. Duk iya kokarin su a ranar ganin Suhaima hakanan ya gagare su. Dole dai Barr Mustapha ya isa station in a matsayin lawyer mai kare ta, tunda ya samu lbrn sun kai case in court.

Abin da ya lura shine, kaman ba gsky a lamarin duba da irin kallon da su ke bin shi dashi. Sai kuma su fara kus kus tsakanin su. Wasa su ka dinga mishi da hankali da dai yaga abun da wata a kasa dole ya koma headquarter insu na nan Abuja yayi reporting abinda ke faruwa.

Ko a can inma, shugaban su ce mishi yayi "Barr Mustapha mai ya kai ka amsan irin case in nan? In zan baka shawara ka ajiye wannan case in mana"

"Amma miye dalilin ka na fadan hakan?" Ya tmby, girgiza kai yayi "yace haba Brr kowa ya kwana ya tashi a kasan nan fa yasan su waye Al-mansur, shin kana ganin za ka iya nasara a irin case in nan da ake amfani da kudi da karfin mulki a ci shi? Kai kasan shari'a, Hujjan da duk ka kafa shi shine abin dubawa. Kai ya kamata ka fadawa mutane cewa dayawan mutanen da ake kai prison ba su aikata abinda ake tuhuman su dashi ba,  Aa kawai karfin hujjan akan su ne ya ke kai su inda su ke. Wani irin kudi ma aka yi offering in ka kayi gangancin amsan case irin wannan mustapha?"

Runtse ido Barr yayi, tabbas dukkan abinda ake fada mishi gsky ne. Wannan shi ya ke kara tsorata shi da shari'an. "Ba kudi aka bani ba sir, i personally know the girl ne zan so in taimakeka"

Shiru  yayi alamun nazari, can yace "Shknn Barr tun da ka dage, Allah ya bada nasara. Kaje ka same su, zanyi sending note" godiya yayi ma shugaban nasu, cike da farin cikin nasara ya kara nufan station in.

...

Da constable ya bude mata lock in ta fito, ko kadan ba ta kawo komai a rai ba, binshi tayi kaman rakumi da akala har zuwa inda Mustapha ke zaune. Ko kusa ba tayi tsammani ganin daya daga cikin su ba, barin ma a yanayin da aka taho da ita. Kokarin tsagaita tunanin tayi ta fuskance shi da idanunta da su ke bushe kararau har izuwa yanzu.

Kallo daya ya mata ya ji wani irin mugun tausayin ta na ratsa dukkan jikin shi. Ta tsinci kanta ne a cikin wani irin mawuyacin halin. Ko shakka ba yayi gab ta ke da ta cire buri ga rayuwa gabdaya, shiyasa shi kuma ya lashi takobin taimaka ma ta ko ta halin yaya, ko da kuwa bashi ke da Nasara ba a karshen hankalin shi ba zai kwanta ba in har bai kokarta ba.

"Suhaima" ya kira sunan ta yana kara karantar yanayin ta, shi kam a kwana biyun nan har rama idon shi yaga ta mai. Hannun ta daya ta sa kan goshi ta runtse idanuwan ta, a can cikin ta ta keji wani irin radadi na wucin gadi. "Abban Haydar ka yarda dani Wlh ban aika ta ba"

"Kar ki damu, ba wannan bane matsalan a yanzu" ya fada yana kara gyara zaman shi.

Zaro idanu tayi cike da rashin fahimtar manufar maganar shi. Gane hakan da yayi ne yace ma ta "Kin fa san shi kotu hujja kawai ya ke nema Suhaima, kuma banda wurin ki ban gani akwai inda zan samu hujjojin da ya kamata, shiyasa na ke so ki kwantar da hankali muyi magana" saurin girgiza kai tayi tana fadin "ba wannan bane matsala ta Abban Haydar, so na ke kawai ku yarda dani, ku yarda ban aika ta ba. Amma nasan jayayye dasu ba zai wani haifar da da mai idanu ba, toh in ma na samu fita ina zan nufa? Ban ganin ina da wani abu da zanyi fada domin shi ba, banda komai kuma banda kowa"

Zantukan ta ba karamin illa su ka mai ba, sai dai ba ta cikin halin da za ta fuskanci hakan da ba ta karasa ba. Kaman dai yanda yayi hasashe ne, she is giving up akan rayuwa gabadayan ta. Da kyar ya iya hado kalaman da zai fada mata "Aa Suhaima ki daina maganar nan, ai kina da Allah kuma ba gamu ba? Mu dai ba mu ga wani halin assha a tare da ke iya zaman da muka yi da ke, shiyasa mu ka tsaya miki"

Labarin Rayuwata Donde viven las historias. Descúbrelo ahora