Babi na goma sha daya

388 60 1
                                        

Ranar yau ta kasance ranar juma'a. Saboda ruwan saman da ake ta shararawa ya sa ba lallai ka gane cewa juma'an bane. Ruwan ma an dade ba ayi shi ba. Da ke ana cikin karshen october hakan ya sa ake sa ran ruwan bankwana ne ake yi, lokacin kaka na gab da shigowa kenan. Yaran gidan gabadaya na makaranta sai su Anisa da Suhaima kawai. yanayin garin ya sa duk su libge akan gado,  har wurin Goma da rabi sannan su ka mike, shi inma Mommy ce ta musu waya su tashi su ma Baban su breakfast, zai shigo garin yanzu daga Abuja.

Bai dade da shigo gidan ba su ka gama. Anisa ce ta hada komai ta wuce dashi side in shi.

By 11:37 am, karan siren ya fara tashi. Da ke Unguwa ne da mutane ke hulda akan hanya sosai ba kaman GRA ba, jama'an wurin ne su ka fara mamakin mai ya kawo motocin yan sandan dayawa haka cikin layin? Shin lafiya? Wani mai laifin kuma su ke shirin kamawa. Haka su ka dinga tafiya har kofar gidan Engr Usman alkali, inda duk su ka ja birki. Wani karamin dan sanda ne yayi saurin sauka daga motan farko yayi wurin babban odyssey in da ke tsakiya. Sai da ya sarawa ogan nashi "Sir, how do we get in?"

"Get me the door" ya amsa, dan sanda yayi saurin isa ya bude mai kofan. "Get the boy, dashi za mu shiga" Faroukh ne ya fito daga cikin motan, Yan sandan na bin shi a baya. kai tsaye ya musu jagora zuwa cikin gidan.

Engr na zaune a falon shi yana tsakiyar breakfast ya fara jin siren in Polisawan na tashi. Ba abinda ya kawo a ranshi sai yanzu da ya daga kai, Faroukh ya hango suna faman shigowa cikin gida shi da polisawan kusan biyar. Ai bai san da ya ji kafafuwan shi ba, da kyar ya iya sa takalma yayi waje, domin jin me ya hada danshi da polisawan nan.

Idanuwa ya zuba musu domin gano dalilin shigowar su cikin gidan shi. Faroukh ya zubawa idanu yana kokarin gano wani tashin hankali akan fuskan nashi, sai dai sadda kan shi kasan da yayi bai ba wa mahaifin nashi daman hakan ba.

Hannu babban police in ya mikawa Engr, bayan sun gaisa police in ya gabatar mishi da wani takarda. Engr dai har yanzu a rude yake. Ga faroukh kam har yanzu kanshi na kasa yaki yarda ya kalli mahaifin nashi. Har sanda Engr ya bude takarta, ya ga shaidan kotu ya dauka Faroukh ne ya dauka mishi magana.

Tabbas arrest warrant ne, sai dai ba sunan Faroukh bane a jiki. Suhaima Adam Bello ya gani a rubuce. "An sanar mana cewa tana gidan ka, we need to take her for investigation" Shi dai Engr har yanzu shakku ke ranshi. Shin in ma yarinyar su ke nema me ye hadin ta kuma da Faroukh. Murya ya bude ya kwalla wa Anisa kira. Da sauri ta fito, sai dai tun kafin ta karaso wajen ya ce mata ta kira mai suhaima tazo waje.

Tun daga bakin kofa da ta hango su ta san abinda ya kawo su, ko shakka ba tayi ita su ke nema, balle kuma ma ga Faroukh a tsaye tare dasu. Gabaday jikin ta rawa ya ke, kusan uku ta ke tuntube jiki a sanyaye ta karasa wurin su "Ita ce wannan?" Engr ya tmby, Sergeant maccen da ke wurin ne ta fiddowa Engr hoton da su ka zo dashi domin tabbatar mishi wacce su ke neman ce.

"Suhaimaa" Engr ya kira cike da mamaki a idabuwan shi. Kanta a kasa yake, tana jin zuciyan ta kaman zai fito tsabagen yanda ya ke dukawa da sauri sauri "na'am Baba?"ta amsa.

"Me ke faruwa?" Ya tmby yana kallon ta da kuma yanayin da ta shiga, gabadaya a rikice ta ke sai dai duk da hakan ba ko alaman hawaye a idanuwan ta. Hakan kan shi abun tsoro ne.

Tana shirin ba da amsa taga Ogan nasu ya mika wa maccen handcuff. Kaman a mafarki ta fara jin yanda ake karanto mata marinda right "You are arrested for the suspicion of murder's attempt of Zayd Almansur. You have the right to remain silent. Anything you say maybe used against you in the court of law. You have the right to consult a lawyer, if you can't afford one will be appoint to you if you so desire"

Labarin Rayuwata Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin