A gajiye likis mu ka koma gida ranar, ko kallo na Zayd bai kara yi ba har nayi parking, daukan Amal yayi da ba ta san inda kanta ya ke ba yayi cikin dakin ta. Ni baccin ma ji nayi ba abinda zan iya yi, haka nan na zauna a falo na kunna film duk da hankali na bai wani kai, mutane kawai na ke gani suna ta displaying action. Sautin da ya ke fito daga dakin Amal yasa ni sanin abinda ke faruwa, daman ganin abinda a club in nasan dole hakan zai faru. Its been long sex yashiga tsakanin su as far as i know, they are all louders hakan yasa na ke ganewa.
Na dade a falon ni kadai ina kallon TV ko kuma ince film yana kallo na dan gabadaya ban sa abinda ake ba. Tunanin kunci rayuwa da tausayin rayuwa irin tawa ya sa naji gabadaya duniyan na neman fice min a kai. Kwallan da na dade ban zubda bane naji suna zuba a idanu na, na dauki lokaci a haka ina jin kaina na juyawa yayin da hawayen ke cigabda da tsiyaya. Ban ji fitowan Zayd ba ko takun shi sai tafun hannun shi da naji kan fuskana, hawayen ya laso da dan yatsan shi manuniya. Yatsan ya koma bi da kallo ya tsaya a kaina kaman mai son gano wani abu, can ya girgiza kanshi sannan ya saman ma kanshi matsugun ni a daf da inda nake. Hannuwan shi ya ratayo ta kan wuya na, sai lokacin na iya daga kai na kalle shi, idanuwan nan sun yi jajur kaman wanda ya sha kuka ya koshi.
Bai dai ce min komai ba har na fauke idanuwa na daga kan shi, kara jawo ni jikin shi yayi ya juya yana fuskan ta na da kyau. "Why are you here?" Na tmby, magana na farko kenan tun bayan fitowan shi.
"Suhaiima please" sauri dakatar dashi nayi da hannu na, a hankali nace "tmbyn ka kawai nayi nd you can only give me an answer" kan shi ya sadda kasa, focus in shi gabadaya na kan yatsun kafana. Ban san mai yake nema a wurin ba. "I want to check on you" more like a whisper maganan ta fito daga can kasan makoshin shi. Siririn tsaki na ja, na janye jikina daga nashi "You can pretend all you want, na riga da na gane komai" saurin girgiza kai yayi yace "pls babe kar muyi haka, ki saurare ni kafin ki yanke min hukunci"
"Wani saurara kuma Zayd? Bayan abinda idanuwa na da kuma idon duniya su ka gani. Ba ma wannan ba, me kuke son in fada wa Mum bayan yarda dani yasa ta amince ma zamana da yar ta, tun dazu na ke ganin miss calls inta" zaro idanu yayi, yace min"dont tell me abun nan yayi yawo?"
"You can check the media ai nd ka kwantar da hankalin ka am not talking about the kiss" ba wani reaction in da yayi sai can yace "am not happy seeing you with Hafeez, kinsan wanene Hafeez? Ta ya zaki biye mai har ki bari ya taba jikin ki bayan kinsan hakan bai dac..." Kaman ya karasa nayi saurin mikewa ina kallon shi cike da mamaki ina jan baya "kai har ka san abinda ya dace da wanda bai dace ba Zayd? Ko kuma kai da kake tabanin muharrami na ne? Fada min yaushe ka fara kokarin kiyaye dokokin Allah" jin yanda na ke magana a fusace ne ya sa yayi saurin mikewa.
"Yi hakuri jewel zo ki zauna Dan Allah muyi magana" tsaki na ja kaman ba zan zaunan ba sai kuma na koma inda nake kafin in mike. Ina jin wani irin tafasan da zuciya na ke fama da, i so much hate my life to the extend na ke jin gwara ayi komai kawai a kare ta cikin kankanin lokaci ko na samu in gina wa kaina sabon rayuwa dai dai da tsari na.
Girgiza kafa nake in hararan shi, hakan ya sa shi yin murmushi. Kwantar da murya yayi ya fara magana "nasan ban kyauta miki ba Jewel but kinsan Amal, kinsan yanda ta sani cikin rayuwar ta abu ne mai wahala kwatsam ace ba ma tare da ita, shi..."
"To mai zai hana ku kasancewan a tare? Kai ma fa na gane kana bukatar hakan. Dan haka please ka kyale min rayuwa tun wuri Zayd"
"Ba zan iya" yayi saurin fada "Zuciyan Amal ni ta ke so sai dai kuma ni nawa zuciyan ke ta hange, ke ce a cikin ta. Ban zan miki karyan ban son kasancewa da Amal ba saboda ita in wata jigone babba a rayuwata, i like her sai dai i have many reasons da yasa ni kasancewa a tare da ita. Nasan kin san me ya shiga tsakani mu a daki, she wanted to and i can just resist her. Amal mace ce Suhaima sai dai ban mata irin son da ta ke min. Ko da inma tausayin ta yafi son yawa, i befriended because of her eloquence amma sai mu ka tsinci kaman a cimin rayuwan da kika same mu."
![](https://img.wattpad.com/cover/150148529-288-k932188.jpg)
VOCÊ ESTÁ LENDO
Labarin Rayuwata
Ficção Geral"Believe me ba wani abun birgewa a labarin Rayuwata shi yasa na gwammaci mutuwar akan Rayuwa irin wannan" idon ta a bushe karoro ta ke maganan ba alamun kuka ba wai don kukan ba Zama dole ba Aa, ta gaji da kukan ne saboda Bai da amfani a gareta do...