Dr Fahad ne tsaya gaban Suhaima yana faman kare ma ta kallo domin ya tabbatar idanuwan shi ba gizo su ke mishi ba. Wannan ba Suhaiman da ya sani bace, wannan tayi duhu sosai, ta lalace sabili da wani irin mugun rama da tayi, kana ganin ta kaga wacce ke cikin garari da masifan rayuwa. Gabadaya ta canja mai a idanu, wani irin hawaye masu zafi yaji sun cika mai idanu ayayin da zuciyan shi ke faman wani irin suya na masifa. "Ya Allah" ya furta a hankali, shi kam ko lokacin da ta ke asibiti bai ga tayi irin wannan lalace wan ba.
"Suhaima, shin miye labarin Rayuwar ki?" Ya furta a hankali, idanuwan shi a kan nata. Sauke na ta idanun tayi kasa yayin da sautin bugawan zuciyan ta ke kara yawa. Da wani irin rikitaciciyar murya tace "Dr lbr ne mai matukar tsawo wanda ya canci a rubuta shi a cikin littatafai domin koyon darasi a cikin shi, zan baku labarin Rayuwata amma sai a hankali" kanta na a kasan har ta gama gabadaya maganan. Tun da ta shigo bakin wurin, wannan ne karo na farko da Dr Fahad ya sani faman ziyartar ta, ba Wai don bai so hakan ba sai dan daman ba ta samu mishi ba. Ko bai jin komai akan Suhaima, yana ma ta kallon kanwa a gare shi hakan ya sa duk wani matsala da damuwa shi ya ke jin shi kaman na shi. "In sha Allahu Za muyi kokarin fidda ki daga wannan wurin, ko baki fada ba ni kam jikina na bani you are innocent" ba tace komai ba saboda ba ta ma San abun da ya dace tace mishin ba, Dr Fahad na da wani mahimmanci na daban a kadadarorin da ke afkuwa a rayuwan ta.
"Nagode" ta fada a hankali, ita kanta ta san rashin abun cewa ne ya sa ta fadin haka saboda Dr Fahad yafi karfin godiyan fatan baki a wurin ta. Girgiza ma ta kai yayi yace "ki daina min irin haka Suhaima ban so" saurin gyade kai tayi, alaman gamsuwa da kalaman na shi.
"Ina Amarya?" Ta tmby cikin siririn muryar ta. Shi mamaki ma ta bashi, a halin nan da ta ke ciki har ta iya tmbyn wani? Share zance yayi da cewa "ki cigaba da addu'a kaman yanda kike yi sannan ki fawallah wa Allah sauran, mu ma muna yi kuma in sha Allahu za a dace" da kai ta amsa shi, dai dai lokacin dan sandan da ke tsaron wurin ya zo sanar mu su lokacin da aka diba musu ya kare. Murmushin yaki ta aika ma Dr Fahad, ba tare da cewa komai ba ta juya domin komawa inda ya zamar ma ta matsugunni a yanzu. Idanuwan shi na kan ta har ta bace, yana mai cikin dimbin tausayi da son ceton ta ya fito daga station in. Already, sun hadu da Barr Mustapha tun shigowan shi Abujan. Gidan Ummin shi ya nufa domin kai gaisuwa a gare ta zuciyan shi fal tsoron wani irin tarba zai samu, tunda su kayi aure da Rufaida ya ke fuskantan matsaloli daga wurin ta. Har yau kafan ta bai taba taka gidan shi ba, kulan shin da ta kan danyi ma saboda sa bakin Daddyn shi ne. Ranar da ya kawo Rufaida wurin ta kuwa sai da yayi kwallan bakin ciki, ko gaisuwan ta a fizge ta amsa daganan ba su kara ganin ta ba sai kanen shi su Zahra da su kayi ta hidima da Rufaidan. Da yayi tunanin yanda Dada ta ke mishi sai da yaji kaman ya nutse don kunya, amma da ke ita Rufaidan ta sa dawan garin sai Ba ta wani sa abun a ka ba.
...
Eden island,
Seychelles.
Zaune ta ke daga gefe guda a open restaurant in da ke kusa da pool in hotel in. Wannan karon ne ziyarar ta na biyu zuwa kasan da ta kira da kasar baiwa, sai dai ta kasa daina kallo da jinjina ni'iman ubangiji da yayi shi cikin tarin ni'imomi. Mafi yawan bakin da ke wurin wandan da su kazo honeymoon ko kuma dai masoyan da su kazo shakatawa. Yeah, the weather is totally good for them, kaman dai abinda ake cema weather for two. Haka kurum ta ke jin wani iri da ya kasance ita daya ne a irin wannan wuri ba tare da kowa nata ba. Wani irin kadaici ta ke jin ya mamaye yayin da ta ke kokarin danne shi da cocktail in da ke gaban ta, a yanda ta ke jin ta she seriously need someone to share those nice moment with her. Har ga Allah, ba za ta tuna when last taji abinda ta ke ji ba, ta dade da cire namiji daga cikin rayuwan ta, ta kulle su daga babin tarihin rayuwar ta gabadaya. Namiji y riga da ya mata illan da ba zata taba iya warke wa ba, shiyasa ta yakice su daga alamuran ta.
YOU ARE READING
Labarin Rayuwata
General Fiction"Believe me ba wani abun birgewa a labarin Rayuwata shi yasa na gwammaci mutuwar akan Rayuwa irin wannan" idon ta a bushe karoro ta ke maganan ba alamun kuka ba wai don kukan ba Zama dole ba Aa, ta gaji da kukan ne saboda Bai da amfani a gareta do...