Hamsin

296 60 6
                                    

Ba ta tashi hakan yasa tayi juyawan ta. Ta riga ta gama gane tsanar ta ne ke gudana a cikin zuciyan shi. Hakan yasa ya watsar da ita, ko maganar arziki bai bari ya shiga tsakanin su ba. Bata ga laifin shi ba, don ko ita ada ta kanji ta tsani kanta. Alhmdlh, tunda ta Mika lamarin ta ga Ubangiji take jin komai na dawo mata dai dai ga Kuma wani irin natsuwa da take samu.

"Ina ke kike yawan maganan Uzuri, shin meyesa itan ba zaki mata ba? Kinsan irin halin da ta shiga a sanadiyyan rashin ki? Rashin hankalin naki har ya Kai ki duba tsaban idon mahaifiyar ki, kina fada mata mugayen kalamai? Ba uwan da ta cancanci hakan, ko da kuwa ba ta hanya aure ta same ki ba, ba dai abinda ya Kai wannan ciwo don haka kisan mekike yi" ba ta amsa shin ba, Amma Kuma kalaman shi ya Kai inda ya Kai a kwakwalwar ta. Tabbas ba ta kyau taba, Amma Kuma ita kanta ba ta San me take fadi ba. Hakan Kuma Yana da alaka da alakanta dukkan wani gurbacewan ta da tayi da rashin mahaifiyar ta a tare da ita tun ba yau ba.

Kalan gaisuwan da Sandan kewa Ummi yasa ta gane ba karamin mutunci ke tsakanin su ba da girmama wa. Bayan nan, ko kallon ta bai yi ba ya fita daga dakin. Hakan yasa ta kara shan jinin jikinta.

"Kiyi Hakuri bansan abinda nake fada ba" gyada Kai Ummin tayi "Na sani Suhaima nasan da ciwo Amma bar na Baki labarin abinda ya hada ni da mahaifin ki. Mahaifin ki mutum ne mai tsatsauran ra'ayi kema kinsan da hakan. Sai dai Kuma tun farko ya San ni ban dau hakan ba, shiyasa duk wani abu nashi Zaki ga ba kasafai yake min ba. Abinda Kuma baki sani ba shine, kafin na hadu dashi da Baffan ku na fara haduwa, shiya fara nema na amma Kuma sabo da irin halayen shi na neman mata shiyasa alakan tamu ba tayi wani nisa ba. Baban su Aseem kuwa shine saurayin da na so har sauran kiris muyi aure rabon ku ya hada ni da Abban ku. Bautan kasa ya kawo shi daga Kano, Kuma yayan Hajja ne, su biyu ne kadai wurin iyayen su. Sai Baban Abdallah daya taso a gidan su. Lokaci yayan babana da nake wurin shi a Borno shi yaki aura min shi, a cewan shi gwara Wanda aka sani domin dai kowa yasan baban mahaifinki a jahan borno da yobe. Nima Sai na hakura na aure shin duk da kuwa nasan kanin baffan ne, na dauka ba wata matsala tunda bashi in bane. Muna cikin kwanciyar hankali, ko a lokacin da na hadu da Hajja bansan cewa yayar baban su Aseem bace. Sai watarana da yazo ya iske ni, na shiga wurinta. Ba wani abunda ya hada ni dashi, har lokacin barin ta gidan da zama yaki dadi, ita kam kishiya tasa ta a gaba. Dole ta hakura da auren, har bayan ta tafi we keep in touch. Har lokacin da na haife ki, su kazo suna, yayan nata ya kawo ta. Lokacin already an hada ta aure da baban Abdallah, hukuncin mahaifin su ne. Bansan ina suka hadu da Baffah ba, Amma ya samu Abban ku ya sanar dashi wai saurayina yazo sunar yar shi, don haka ya bincike ni. A tare suka nemi ni lokacin, so sun San juna. A lokacin Abban ki bai dau abun wani serious ba, Amma a hankali ya dinga zuwa yana fada mishi abubuwa. Dalili kuwa har lokacin yana da ra'ayin ya mallake ni, cikin matan uwargidan tasan ya neme ni, hakan yasa kwata kwata bata kauna ta. Daga baya har waya ya fara min, Sai inki dauka. Tsabagen yawan wayan har Abban ki Sai daya San ana yawan Kira na, yace na bashi ya ma mutumin magana yaki saboda ban son ya gane Dan uwan shi ne. Abinda ya fara sa zargi tsakanin mu kenan. Cikin wannan sarkakiyan na haifi Baffah, tun lokacin ya fara tunanin baffan ba dan shi bane saboda irin text in da ake turo mai a kaina. An ganni a can, an ganni a nan, hakan yasa zargin ya kara yawo har yazo yana bibiyata. Kaman shi da Baffah, yasa shin yardan dan shine. Zuwa lokacin na riga da nasan aure na ya fara samun gargada. Wani Ikon Allah, ban dade da fara koyarwa ba, aka kawo Baban su Aseem University in da nake, ai Kuma lokacin abun ya tsanan ta. Domin dai rahota ake Kai mishi akan ana ganin mu tare dashi, Wlh Suhaima ko gaishe shi banyi saboda gudun matsala. Ya nemi in daina zuwa ko ina, ni Kuma naki. Baban su Aseem kuwa Oga nane, hakan yasa duk yanda naso guje mishi Sai wani abu ya hada mu. Bayan Baffah, na kara Samun wani cikin Amma haka mahaifin ki ya rantse ba nashi bane, muka hau muka fado Amma Ina yaki zancen, daga karshe dai tilasta ni yayi Sai da aka cire cikin nan. Nayi kukan bakin ciki, nayi takaici amma na zabi kare martabar aure na. To Sai dai shi aure ba ayin shi da zargi. Akwai wani zuwana maiduguri, Baffah na kai asibiti Abban ki ya sani zama gidan Baffa duk da ban son haka. Wlh cikin dare ba kunya mutumin nan yaso ya far min, ikon Allah ne ya cece ni a wannan daren. Amma ya min alkawarin ganin bakin ciki mara misaltuwa. Yanda ya fara kuwa shine da amsan Baffah, duk da nasan daga shi har matan shi ba Wanda zai kula min da da, nayi kuka na, nayi bakin ciki Amma hakanan aka Kai shi. Sai Kuma na samu cikin Mai Jiddah, lokacin Kuma bala'i ya taso gadan gadan, domin dai Abban ki cewa yayi Sai dai na kara cire cikin, ni Kuma nace ba Wanda ya isa ya sani kaf duniya. Muka dinga hawa muna sauka, har na haifo ta. Yaki yarda yar tashi ce, musamman ganin ba kamannin. Lokacin ya fara hada ni da yan uwana, har nasiha suke zuwa yi min in rasa abun ce musu. Daga karshe ce min sukayi in na kashe aure na kar na sake na waiwaye su, domin dai labari ya zaga cikin shege nayi da aure na, na haihu. Ban iya zama ana shegan ta min ya, don haka na nemi mahaifin ki da ya gyara abinda ya hada ko Kuma in Kama gabana. Yaki, Sai ma ya kafa min bala'i, wai zai iya hakura ya zauna dani Amma ba tare da Maijiddah ba, in San inda zan kaita, in ko nace zan zauna da ita a bakin aure na. Na gaji da auren zargi, don haka na sama ma kaina mafita domin auren dai ba inda zai Kai ki na zauna tunda ba yarda a tsakanin mu. Labari ya Kai gun yan uwana mun rabu dashi, kowa yace in Kama gabana. Ko na gaya ma Goggo da Goggon Adama illa iyaka za suce nayi Hakuri na zauna ne, ni Kuma ba Zan iya ba. Don haka na hau shirin tafiya, a lokacin Kuma mahaifinki ya sanar min in har na tafi kar na sake na kara tako mai gida, sannan Kar na sake na daukan mishi ya'ya' bai amince ba. Ko ya fadi hakan ne ya na tunanin zan hakura na zauna, bai San na riga da nayi nisa ba. Wannan shine sanadiyyan rabuwan mu, Kuma direct Kano na tafi na kai ma Hajja kuka na. A wurin ta na gama idda na, har na cigaba da zuwa makaranta baban su Aseem bai ma sani. Sai da nayi shekara biyu ma a wurin ta sannan ya San Ina nan. Auren mu Kuma Sai bayan an mishi transfer Egypt, shi ma ikon Allah ne kawai saboda na hakikance na gama aure a rayuwa ta. Ban Kara waiwayan Damaturu ba, Amma kullum kina raina, dake bake kwana nake tashi. Kullum addu'a ta Allah ya raya min ke. Na barwa Allah ikon shi, nasan Kuma duk abinda ya same ki kaddarar kice Suhaima. Ko Ina tare dake kuwa zai faru, a sannan bakin cikin ma zai fi yawa. Sanda ke kawo min feedback akan ki, har zuwa lokacin da yayi loosing contact dake. Lokacin daga ni har shi mun ahiga tashin hankali, saboda yana da niyyan tun kan ki shiga University ya aure ki ya taho dake nan. Amma yasan baban ki ba zai amince ba, ba mu so ya fahimci wani abu bayan nan Kuma ga Goggo. Ya dade yana neman labarin ki, tukunna ya samu a lagos bayan ansan case akan company in da kike aiki. Tanan ya samo ki, don haka ina fatan Zaki yafe min duk wani abinda kike ganin na Miki" da kuka idanun ta, ta rungume mahaifiyar tata "Ina son ki a kullum Ummi na" rungume ta tayi ita ma, cike da farin cikin dake zagaye su ta ko ina.

Labarin Rayuwata Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ