Talatin da daya

207 54 6
                                    

Rayuwata

Babi na hudu


"Bafferh" na fada ina kallon shi cike da mamaki.


Da sauri ya karaso yana rike min hannu "Adda kuka me kike? Mu je ki kaini wurin Umminmu ni fa na dawo ba zan kara komawa ba kuma" wani irin faduwan gaba naji jin abinda ya ke fadi, kenan shima yana cikin damuwa?


"Adda mu je mana, ina so in ganta" cike da tausayi na girgiza mishi kai

"Bafferh Ummi ta tafi ance min ba zata kara dawowa ba"


Kallona yayi ya kasa magana, kuka ya fashe dashi. Na jawo mu ka zauna nan muna ta kuka. Anty Amarya ta fito ta same mu a haka. "Suhaima lfy? Kuka zauna kuna kuka haka?" Ko kafin inyi magana ta dau Bafferh tayi dakin ta dashi, ni ma nabi su a baya. Daga alamun ta na gane tana jin tausayin mu. Lallashin Bafferh tayi sannan tace min in daina kuka kar ya cigaba dayi. Matan na da kirki sosai, don duk lokacin da na ke gidan in naje wurin ta, ta dinga min kyauta kenan, sweet kala kala da kayan kwalliya. Sau daya ina jin yan gidan na fadin ta na da rowa ga sa aiki sai dai ni banga hakan ba. Aiki kam tun kafin ta sani ma zan mata, su Lance abinda ya sa ta ke sona kenan. Ni kam ban damu ba, nayi na dole ma balle Wanda za a yaba min? Sau dayawa godiyan da na kanyi wa a Anty Yana kenan, a tunanin ta cuta na tayi. Sai dai duk inda naje ana jin dadin zama dani saboda son aiki na sabanin yaran ta masu son jiki.


Ranar wuni mukayi ni da Bafferh, gani yake kaman na koma mishi Ummin, ko ina nayi yana nanike dani har tsokanan shi ake. Ko da Ajidda ta zo mu tafi wasa fir na ki binta saboda Bafferh nan fa Goggo tayi ta mana dariya, wai an jimu a rana duk son zuwa yawon mu.


Drama bai tashi ba sai da yan Maiduguri su ka tashi tafiya, kuka Bafferh ya sa ka yana cewa "shi fa Ummin shi ya ke so" yin duniya anyi yaki ji yace ba zai koma ba. Ni kam har ga Allah so na ke ya koma saboda ba San gwara mishi can akan nan. Saboda ya tabbatar min ba a dukan shi kuma ba aiki sai dai ba Wanda ya damu ya kula dashi. Karshe dai da karfi Abbah ya sa shi a mota yana kuka ina kuka haka muka rabu.


Ina primary five headmaster inmu ya dauke ni a cikin wadanda za su zana common entrance, a cewar shi INA da basiran da zan iya ci. Ko da naje na na Goggo lbr tayi ta jin dadi, kawata Ajiddah ko cewa tayi "Suhaima kicewa Abban Ku ya kaiki GGC Damaturu kinga nima can zani" zaro idanu nayi nace "sai dai in fadawa Goggo" ko da na Sanar mata kallona tayi tace "anya Suhaima zaki iya makarantar kwana?" Ganin ina shirin mata kuka tace "shknn zan fada mishi, gama ni ban yadda da zaman da kike wurin Yana ba" ban amsa mata saboda INA tsoro, sai ma murnar da mu ka hau ni da Ajiddah,  daman ta fini da aji daya, to yanzu zamu dawo dai dai da ita kenan, gsky na ji dadi.


Common entrance na fitowa naga na ci exams in dai dai yanda ake bukata. Kaman wasa Abbah ya amince, nan fa ya hau min shiri ni ko zumudi na ya ki boyuwa. Ina ji Adda Falmata na cewa "shegiya, daman daga can seniors in makarantan su kashe ki Kowa ya huta, ba dai boarding ba? Ga ki gashi. " komai ban ce mata saboda nasan za ta fadi abinda ya fi haka ma.


Ba laifi Abba ya min kokari sosai, haka ma Goggon nina biyu. Anty Yana kam ko ranar da zan tafi da na mata sallama, tsaki ta ja tace "kiyi ta tafiya ni kam ba matsala ta bace" salin alin nayi tafiya ta ban ma kowa magana ba sai Al-lawan da ya raka ni har makarantan. Shi ma ce min yayi "Suhaima kiyi karatu kinji?" Gyada mishi kai kawai nayi daga nan ban kara cewa komai ba har mu ka rabu.

Labarin Rayuwata Where stories live. Discover now