Kwakyawar doguwar farar yarinya da ba zata wuce shekara goma ba na hango, Zaune ta ke gaban famfon gidan su tana Yar wakar ta hade da yin wanke wanken da ke gaban ta Wanda ba wai a son ranta ta ke ba an dai Fi karfin tane ya sa ba yanda ta iya, kwanukan ma dirzan dole ta ke musu duk basu fita. A Haka Mustapha ya yi sallama a kofan gidan har ya shiga ba ta amsa ba. "Ke baki ji ana sallama bane?"
"To ni Ina ruwana da Kai da zan amsa ba gun Mama kazo" ta fada tana cigaba da wanke wanke kaman ta fashe.
"Kinga ko da ba ki min rashin kunya ba da na taya ki wanke wanken" da sauri ta taso har da durkusawa. "Lah ya Musty Dan Allah kayi hakuri kaga fa wasa nake maka Allah, Amin wa'alaika Salam Yayana na kaina" ta fada tana washe baki ita ala dole yaudara ta ke. Dariya ya dinga kwashe wa dashi har da rike ciki "an ki wayon yarinya baran yi ba"
"Ya Musty Allah daga yau Zan dinga maka biyayya kaga ma fa nace Zan maka zaman dakin in kayi aure" murmushi ya saki sosai "Ashe ko za ki garu yarinya, ba ma Zan dauko Yar aiki ba,
Yanzu dai dube ni na ci kwalliya ta kice in Miki wanke wanke?" Wannan karon turo bakin ta yi kaman za ta saki kuka "toh ba Kai kace za ka Taya ni ba"
"Zan Taya ki sai ran da baki min rashin kunya ba Kinga dai yanzu sauri na ke in Kai wa Mama sako in tafi tadi Kar Mata ta tayi ta jira na"
"Maryam Maryam yanzu har yanzu ba ki gama wanke wanken ba ko ki Zo ki tafi makaranta tsabagen rashin ji ko za ki Zo ki same ni"
"Mama fa na kusan gamawa"
"Ai Naga alama" ta fito tana fada, komawa tayi ta cigaba da wanke wanken shi ko Mustapha durkusawa yayi ya gaida mama sannan ya bata sakon da Babban Dan nata ya aiko dashi wato Abbah. "To Mustapha an gode ko ka ce mishi an gode sosai Allah ya Kara budi yasu yayar ta ka da faruku"
"Suna lfy lau Mama sun mace zasu Zo Anjima"
"Allah ya kawo su lfy shigo Mana Mustapha"
"Aa mama akwai inda Zan karasa ne"
"A toh shknn sai anjima"
"Toh mama sai anjima Mimi in Zo in Taya kin" harara ta watso Mai shi ko ya dinga Mata dariya yana jin mama na fadin "kyaleta kayi tafiyan ka ni da ita ne yau a gidan Nan" sai da ya Mata gwalo kafin ya bar gidan sai da taci kukan ta sannan ta gama islamiyyan ma latti ta je bayan ta Sha duka gun Mama.
Ai ko ana tashi gun shi ta yiyo Yana zaune a dan karamin shagon da ya ke Zama Yana Saida abubuwan shi. Tun daga nesa ta hango wata budurwa a kofan shagon a tsaye ai ko da sauri ta karasa tana zuwa ko ta rike kugu.
"Ya Musty dama wannan ce budurwar ta ko toh wlh ba ta da kyau" da mamaki ya bita da kallo sai dai kafin ma ya kwabe ta ta fadi kasa sai dariya ta ke ta yi, yarinyar da ta kumbura kaman ta fashe da ja dogon tsaki da karfi ya fara Mata magana "yi hakuri sadiya Zan aiki da roban tuwon Madaran da kudin anjima" dago ta yayi daga kasa ya matse Mata kunne Sannan ta saki Kara "Ya Musty daga fadan gsky"
"Me ya kawo ki wuri na"
"Tuwon Madara nazo Sha"
"Bayan ki zagi Mai yi ba Zan bada ba" turo baki tayi sai can Kuma ta ja tsaki "ba ma a so ai tunda nata ne" daga kafada yayi alaman ko a jikin shi sannan ta bar wurin tana Yar wakar ta.

ESTÁS LEYENDO
Labarin Rayuwata
Ficción General"Believe me ba wani abun birgewa a labarin Rayuwata shi yasa na gwammaci mutuwar akan Rayuwa irin wannan" idon ta a bushe karoro ta ke maganan ba alamun kuka ba wai don kukan ba Zama dole ba Aa, ta gaji da kukan ne saboda Bai da amfani a gareta do...