Ashirin da takwas

266 57 13
                                    

Kaduna

Yana fadawa Anisa, jiki na rawa ta gaggauta kawo mishi manuscript in kaman yanda ya bukata. Bai yi wata wata ba kuwa ya amsa sannan ya wuce gidan shi da duba iyalin shi. A falo ya iske maryam zaune tana danna waya,  ga gidan duk yanayin shi sai a hankali. Abinda ya lura shine a kwana biyun nan ta fara maido halin ta na da. Tayi farin cikin ganin shi musamman da zuwan nashi ya kasance bazata, amma da ke shu'uma ce ta buga a jarida sai ta basar sannu da zuwan ma da kyar ya fito daga bakin ta. "Au baki ji dadin ganina ba in koma inda na fito?" Hararan ta yayi, dole ta ajiye wayan hannun ta, ta dan turo baki "Mu dai kawai an kwace mana kai wlh" daganan su ka dan sakewa juna, duk can kasan ranshi bai ji dadin irin tarban da ya tarar ba gun masoyiyar tashi kuma mallakin shi.

Sai da ya dan natsa tukunna ya fara bude manuscript in cike da son ganin abinda ya kunsa.

Rayuwata

Babi na daya


Damaturu, Yobe state

Ina tsalle tsalle na shiga layin gidanmu ina cilla jakan Islamiyya ta sama ina cafkewa cike da farin ciki a raina, buri na in isa gida in sanarwa Ummi tabbas yau na bada hadda ta dai dai malamin mu har kyauta ya min. Ina jin kawata Adama da muke dawowa islamiyya tare tana kwla min kira in zo in amshi pencil in da na bata aro nayi mata banza.

Tun a kofar gidanmu na cire hijabi na na ci dammara ina faman kwallawa mahaifiyata kira. "Ummi Ummi Ummi na dawo" da yayata Falmata na ci karo da sauri na matsa saboda saura kiris in buge ta, saurin matsawa nayi a tsorace Sanin halin ta, muddin kuskure ya Sani na buge ta kwana zanyi jiki na na ciwo. Kwafa tayi tana galla min harara "Allah ya rufa miki asiri kuma kar ki cika mu da ihu gantalalliyar uwar ta ki da kike kira tayi gaba tabi duniya" kallon ta kawai nayi domin shekaruna sunyi karanta in fahimci abinda ta ke nufi. ba don na damu da abinda tace ba na nufi wurin mu ina kokarin karasawa dakin Ummi ina cigaba da kwalla mata kira.

Sai dai wasa gaske ba Ummi ba alamun ta haka kuma ba kanwata maijidda. Gajiya nayi na fito na zauna kan baranda ina jiran ta inda za ta fito.  Shin ina Ummi taje? Ni dai nasan in zata unguwa tana fada min amma yau ba ta fada ba. Cikin falon na sake komawa na ga komai na nan yanda ya ke. Don haka nayi saurin nufan dakin ta ina kallon shi. A hankali na duba akwatinan da ke wurin sun ragu ko da na duba wardrobe naga ba kayan ta haka ba na maijidda, ban San lokacin da na saki kara ba na fara birgima a kasa, duk a tunanina tafiya su kayi su ka barni. Ni ko babban bakin cikina shine zan koma wurin Anty Yana. Duk lokacin da Ummi tayi tafiya ta barni a wurin ta ba karamin wahala na ke sha ba wurin Adda Falmata, Anty Yana dai ba za ta buge ni haka kuma ba zata hana a bugen ba, ko kallo ban ishe ta ba, kai ko gaisuwana ba cika amsawa tayi ba.

Wani irin tsawa naji a kai na daya Sani saurin yin shiru ba shiri, jikina har karkarwa yake a sanadiyyan wanda na gani a gaba na yana bina da harara alamun ba wasa akan fuskanshi. Yaya baba ne tsaye a kaina da abokin shi Umar sanda.

"Kukan uban me kike wa mutane? Har da birgima don tsabagen iskanci da samun wuri ko"

Cikin rawan murya da duk ya dishe tsabagen kuka nace "Ummina ban ganta"

Wani irin dariya na ji an kyakyata min, har cikin raina naji bakin cikin dariyan nan mai kama da na mugunta, sai dai ba daga bakin Yaya baba ya fito ba, abokin shi ne Umar sanda da su ke tare.

"Au ba ta fada miki za ta bar gidan nan bane? To tafi na har abada, ba za kuma ta kara dawo ba har abada. Kin San halina sarai ban son iskanci taso muje Abba na kiran ki" Yaya baba ya fada yana bina da harara.

Labarin Rayuwata Where stories live. Discover now