Yau tunda safe da Rufaida ta fito ta ke tunanin Suhaima, hakanan kawai ta ke jin Yarinyar ta mata. Ta na bata tausayi don ta san ba karamin abu zai sa mutum ya samu raunuka irin wannan amma yaki fadi yan uwanshi ba. Yanke shawara tayi tana zuwa asibitin ita za ta fara zuwa ta duba, kwana biyu ba ta leka ta ba ba don komai ba sai dan Dr Fahad, tana kokarin ganin ko yaushe haduwar su yayi karanci. Da wannan tunanin ta samu karasawa asibitin, tana rubuta suna a registern asibitin na ma'aikata gabadaya ta nufi wurin Suhaiman. Kaman ko yaushe kwance ta ke akan gado sai da wannan karon ko ina na jikin ta rawa ya ke, alamun sanyi na damun ta. Fankan da ke aiki a dakin Rufaida ta duba taga a kashe hakan yasa ta nufi wurin Suhaima domin sanin me ke faruwa. Bargon kadai da Sister Rufaida ta kai hannun ta ya dau zafi, ganin haka ya sa fa fara kokarin budewa. Sai faman karkarwa take hakoran ta har hadewa su ke. "Subhanallah! Lfy Suhaima?" Ta furta tana kokarin kai hannun ta wuyan ta, aiko nan in ma radau ta ji shi. Da alamun dai kwana tayi da zazzabin. Rufaida ba ta son lokacin da ta fiddo wayan ta ba ta fara neman numban Dr Fahad. Shigowan shi asibiti kenan yayi parking yaga kiran Rufaidan na shigowa wayan shi. Mamaki ne yaji mamaye sanin da yayi yanzun guje mishi mq ta ke. Daukan wayan yana tunanin ko dai patient in shi ne.
"Suhaima is..." Iya abinda ya ji ta fada kenan yayi saurin nufan dakin ba tare da ya damu da kashe wayan ba.
"What is the matter?" Kusan a tare ya fada da bude kofan dakin.
"Fever" Rufaidan ta bashi amsa tana kokarin dannawa Suhaima towel in da ta jika da ruwa akan goshin ta.
"Is it that high?" Da Kai ta mishi alamun eh kafin ta matsa ya fara duba ta da stethoscope.
Siririn tsaki ya ja ya juya wurin Rufaida "pls taimaka min da Sphygmomanometer daga ward wurin Vitals" bata ce komai ba ta fita. Mai da hankalin shi yayi kan Suhaimaj da har yanzu ta ke rawan sanyi, ta lullube da bargo fuskan ta ne kawai a waje sai ko kafa da hannun da ke da karayan. Idanuwan ta sunyi ja alamun hada ciwon kai. Hannun shi akan goshin ta, duk da towel in da yazo ya tarar Rufaida na sa mata amma radau yaji shi. Shi daman ya san yawan zaman asibiti ma na sa wa mutum ciwo. A yanda ya kamata, tunda ta fara warke wa ta tafi gida in yaso a dinga kawo ta check up har zuwa lokacin da za a kunce karayan. Sai dai bai jin za iya barin hakan duk da Brr Mustapha ya nuna son tfy da ita in, yana jin cewa ba yan uwan ta bane duk yanda su ka kai da tausayi ba lallai su kula da ita yanda ya kamata domin ko ba su san ciwon ta ba. Komai da ya faru da ita a gaban idon shi ne, yana tunanin ba mamaki hakan yana da alaka da tausayin ta da yake ji na ratsa ko ina na jikin shi. Da komai na rayuwan shi ya ke jin he needs to protect her. Kasa dauke hannun shi a saman goshin ta yayi, bai ko da yi tunanin zai iya kara mata nauyi ba. Addu'a ya fara kokarin mata, bai sanda idanun shi ya sauka akan na ta. Ba wani irin abu ya hango a cikin su da ya sa shi saurin dauke nashi idon, in bq gizo ba ne tabbas shi kam wani haske ya hango mai kashe wa mutum idanu cikin na ta idon. Bai san shigowan Rufaida ba, shi ko takun ta ma bai ji ba sai dai kawai ya ga ta ajiye mishi abinda ya bukata kan table in da ke kusa dashi. Sai a lokacin ya iya daga hannun shi daga kan goshin ta, a hannun da ba karaya ya sa mata abun domin gwada BP inta. Pulse rate inta is high sannan Kuma Bp ma is very high. Ba shakka duk yanda ya so kin yarda da abinda idanun shi ke gaya mishin, Suhaima na fama da hawan jini. Duk sanda ya gwada ba wani canji. Ya kan rasa dalilin da ke sa Yan mata hawan jini sosai a zamanin nan, gabadaya shi kam ji ya ke duk ya fara karaya. A rayuwan shi na likita ya ga abubuwa da dama masu matukar ban tsoro da girgiza, mutum da ranshi amma sai abubuwa da dama su hana shi jin dadin rayuwan. Hakika duk wanda bai ji tsoron Allah ba ya shiga Uku. "Ki kira lab su turo akwai da tests in da nake so a mata". Wayan da ke dakin Rufaida ta daga ta kira lab in, su ka tabbatar mata za su zo yanzu. Kara sa ta tayi ta hado alluran da yq ke ganinnza su saukar da zazzabin. Rufaida har ta zo tana tunanin yanda za ta fara yi mata. Fahimtan hakan da yayi ne yace " kawo kawai ki ban tourniquet a hannun zan mata. Sai ki rubuta min lab request foam in, za ayi Mp, FBC, widal test, Lipid profile, E/U/cr, Screening na hepatitis da Fasting na sugar. Ai ba ta ci komai ba ko?"
ESTÁS LEYENDO
Labarin Rayuwata
Ficción General"Believe me ba wani abun birgewa a labarin Rayuwata shi yasa na gwammaci mutuwar akan Rayuwa irin wannan" idon ta a bushe karoro ta ke maganan ba alamun kuka ba wai don kukan ba Zama dole ba Aa, ta gaji da kukan ne saboda Bai da amfani a gareta do...