Karfe Tara da rabi dai dai Suhaima ta gama duk wani abinda za tayi a dakin, ta share shi tayi mopping, ta wanke bayi, sai da ko Mai yayi tsaf sannan ta kunna burner ta fito falo.
A falo ta samu matar gidan da Kayan bacci a jikin ta tana zaune tana Kallo, Haidar ko na bacci akan kujeran da ta ke zaune "Ina kwana Maman Haidar"
"Lafiya kalau Suhaima an tashi lafiya? Ya kafan?"
"Alhamdulillah"
"Gashi kin tashi ko breakfast ba a dora ba, akwai ruwan zafi a flask ko Zaki Sha kafin Baban Haidar ya fita ya siyo mana breakfast"
"Ah bara na yi mana, ba akwai kayan abincin ba"
"Eh akwai kinsan Hadiza ba ta Nan so sai a slow"
"Ba matsala bara na yi in" Suhaima ta fada tana nufan hanyan kitchen, can kasan zuciyan ta ko tana mamakin hali irin na Maryam, gabadaya ta gama fahimtan ta a sati biyun da suka zauna tare. Kiwuya gare ta na bala'i ba ta iya komai na gidan in ba yi Mata za ayi ba to Bata damu ya zauna hakan ba.
Da tunanin hali irin na Maryam ta shiga kitchen in Wanda shima din kacha kacha ya ke kaman zai yi ihu. Saurin girgiza kanta tayi, a fili ko ta furta "No" ma'ajiyan tsintsiya ta nufa ta share kitchen ta tattare shi ta yi wanke wanke sannan ta goge ko Ina. In 20 minutes kitchen ya dawo hayyacin shi ita ma Kuma sai a Nan tayi feeling satisfied ta fara Shirin girkin.
Golden yam da sauce ta musu sannan ta daura ruwan shayi da ya Sha kayan kamshi kaman yanda ta ga anayi kullum a ajiye a dinning, may be maigidan ke sha. Nan ta gama ta je tayi setting dinning in, dai dai fitowan Mustapha daga bedroom yana daura cuplinks, cike da girmama wa Suhaima ta dan durkusa sannan ta gaishe shi. "Ah Malama Suhaima yau ke ki Mana girki kenan" murmushi kawai tayi ba tare da ta amsa ba. "Ai ko kin kyauta Kinga I don't have to waste my time and money" ita dai ba tace komai ba sai daukan nata share in da tayi ta nufi dakin ta. "Ah Suhaima ya za ki shiga ciki" Maryam tayi maganan tana Kallon ta.
"No bar ta Kila za tafi sakewa a can in ne" Mustapha ya fada Yana zuba ruwan shayin a cup inshi.
Tun da ya Kai abincin bakin shi ya ke ta yabon girkin. Tun Maryam na mishi dariyan Santi har ta hade Rai ko yayi magana ba ta tankawa, lura da hakan yayi ya sa yayi magana "mimi dear ya dai, wa ya taba min ke?" Banza tayi dashi ganin haka yasa yayi saurin ajiye cup in shayin da ke hannun shi ya tattara hankalin shi gabadaya ya maida kanta, Sa'a Daya da Maryam ta ci a rayuwar ta kenan, soyayyar da Mustapha ya ke Mata kaman zai lashe ta ko kadan bai son yaga baccin ranta.
"Kinga Dan Allah fada min Mana ko ni na bata Miki rai"
Ganin yanda ya marairaice ya sa ta dan saki fuskan ta "Ji fa yanda kake ta yabon girkin ta as if ba Ka taba cin abincin da ya Kai shi ba"
"No ba Haka bane Mimi na, na kwana biyu ban ci abincin da yayi dadi like wannan bane kinsan ba wai Ina son abincin restaurant bane and Mai aikin am not enjoying her food but you insist a bar ta"
"Whatever am very sure Zan iya Wanda ya fi wannan ma"
"Ba kiyi karya ba mimi, you are a very good cook but ba ki son you so i have to manage since i love my queen" murmushi farinciki ne yayi appearing a fuskan ta har ta manta wa abinda ta ke wa fushi.
Roudah watch da ke hannun shi ya dubo "I've to go mimi, shari'an mu will Soon starts"
"Okay dear Allah ya bada Sa'a"
VOCÊ ESTÁ LENDO
Labarin Rayuwata
Ficção Geral"Believe me ba wani abun birgewa a labarin Rayuwata shi yasa na gwammaci mutuwar akan Rayuwa irin wannan" idon ta a bushe karoro ta ke maganan ba alamun kuka ba wai don kukan ba Zama dole ba Aa, ta gaji da kukan ne saboda Bai da amfani a gareta do...
